• About
  • Contact
Tuesday, October 6, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa Waƙa

Waƙar “Taimaka Rabbana” ta Sani Sabulu Kanoma

by IBRAHIM SHEME
August 26, 2018
0
Waƙar “Taimaka Rabbana” ta Sani Sabulu Kanoma
0
SHARES
8
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

 

Baitikan da na fi so a waƙoƙin Alhaji Sani Sabulu Kanoma su na cikin waƙar sa ta “Taimaka Rabbana”. Ga su na zauna na rubuta su kamar haka:

In ka na yawo cikin duniya,
Kag ga abin mamaki bai kamar ƙarewa,
Sai kullum ƙaruwa za ya yi.

Sai ka samu mutum cikakken mutum,
Ka iske mutum kamak kamili,
Hannu na mutum, idanun mutum,
In ka koma cikin zuciya tasa sai ka ga ƙwamma kura da shi!

Ka san sha’anin duniya wuya ce garai,
In an ka iya shi daɗi garai.

In kay yi kure, akwai ‘yaw wuya.

Ya ikon Allah, ka tserad da mu ka hana mu faɗa ka ganar da mu gaskiya.

Taimaka Rabbana, ya Jallah ka ceci ‘yan zamani.

Ka san sha’anin duniyag ga sai Rabbana.

Ka san sha’anin duniya wuya ag garai,
In ka ga mutum ka na ra’ayi nai malam,
Kafin ku zam jiki kai da shi, na so ka yi bincike nai kaɗan,
Ka bar dubin fuska da kaurin jiki,
Na so ka yi binciken zuciya da irin halin da duk ag garai.

Ka san cinikin ɗan’adam wuya ag garai,
Ko an bar ma sule goma nan a cikin naira rage sule biyar,
Watakila ka na zaton faɗuwa.

Ka san hikima – eh?
Sha’anin duniya wuya ag garai.
Amma inji mai waƙa uban Zainaba, Sani,
Amma inji mai waƙa uban A’isha, Sani.

Sha’anin duniya wuya ag garai,
Sannan cinikin ɗan’adam wuya ag garai,
In an ka biyo ana bincike, ka je ka hwaɗi garan an ka ji.

Taimaka Rabbana, ya Jallah ka ceci ‘yan zamani.
Ya ikon Allah, ka tserad da mu ka hana mu faɗa ka ganar da mu gaskiya.
Ka san sha’anin duniyag ga sai Rabbana.

Ka samu mutum cikakken mutum,
Hannu na mutum, idanun mutum, a’ah!
Daidai ya yi godiyar Rabbana, sai ka iske ana ta’asa da shi.

Allah ya yi ma jiki na mutum,
Kuma yai maka lafiya ta mutum,
Daidai ka yi godiyar Rabbana, sai ka iske ana ta’adi da kai.

Ka san sha’anin duniyag ga sai Rabbana.

Ka samu mutum kamar kamili,
Ka iske mutum cikakken mutum, (2x)
Ga riga, cikin rawani,
Da ka koma cikin zuciya tasa sai ka ga ƙwamma kura da shi!

Ka san sha’anin duniyag ga sai Rabbana. (2x)

Loading

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading…
Tags: Sani Sabulu Kanomawaƙar Hausa
Previous Post

Garba Dangida at 62: A Short Appreciation

Next Post

Littafin “Shata Ikon Allah!”

Next Post
Littafin “Shata Ikon Allah!”

Littafin "Shata Ikon Allah!"

Waƙar “Ranar Kilishi Jikar Dikko” ta Mamman Shata Katsina

Waƙar "Ranar Kilishi Jikar Dikko" ta Mamman Shata Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Odia: What next after the 50th?
  • Chinua Achebe in Hausa: An Interview with Ibrahim Sheme
  • Uzziah J. Alabra: The Man Behind A Free Newsmagazine
  • People Would Dance If Something Negative Happened to Obasanjo
  • Taƙaitaccen tarihin Habibu Sakarci Mai Kukuma (1926-1977) 

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d