• About
  • Contact
Monday, October 5, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Columns Online Musings

Littafin “Shata Ikon Allah!”

by IBRAHIM SHEME
August 29, 2018
0
Littafin “Shata Ikon Allah!”
Littafin "Shata Ikon Allah!"

Littafin "Shata Ikon Allah!"

0
SHARES
64
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter
Littafin “Shata Ikon Allah!”

Alhamdu lillah! Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!

Bayan na shafe shekara 12 ina aiki kan sake rubuta shahararren littafin nan na tarihin Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina, da zurfafa bincike a kan rayuwar sa, a yau dai Allah (SWT), mai kowa mai komai, ya yi ikon sa, littafi ya shigo hannu na. An kammala dab’in sa da shirya shi a bisa sabon fasalin da ya dauka. Allah na gode maka!

Wannan littafi, wanda Shata da kan shi ne ya ba ni izinin rubuta shi, ya bambanta da wanda na jagoranci rubutawa a baya, wato wanda ya fito a shekarar 2006. Ko makaho ya shafa, zai ji bambancin. Ya inganta ta fuskar kyautata bincike da nazari, ya inganta ta fuskar yawan shafuka, ya inganta ta fuskar kyan dab’i, ya inganta ta wajen yawan shafuka.

Shafi 921 ne. Akwai shafi 32 masu dauke da hotuna masu kala, wadanda aka buga kan takarda mai santsi.

A cikin littafin, akwai hotuna guda 580. A cikin su, akwai hotuna masu kala har 98.

Babu littafin da na taba shan wuyar rubutawa kamar wannan. Na yi yawo a garuruwa da kauyuka. Na kashe kudi ban san adadin su ba. Na rika zama a tebur, a gaban komfuta, daga safe zuwa karfe 2 na dare, na tsawon watanni, na hana kai na more rayuwa yadda ya kamata, kafin wannan aiki ya kammala. Sannan na sha fama da masu cewa don Allah yaushe wannan littafi zai fito? Masoyan kenan. Na sha fama da masu zunden cewa na rike littafi, na hana shi fitowa. To, Allah ya yi – wai aure da mara kwabo – a yau ga kwafen littafin ya shigo hannu na.

To yaushe zai shiga kasuwa? Ai har ma ya shiga, domin kuwa ko a gobe za mu iya sayar da shi ga duk mai so.

Addu’a ta ita ce Allah ya sa a ce gara da aka yi. Allah ya sa albarka.

Allah ya jikan Alhaji Muhammadu Shata, amin.

Ibrahim Sheme

Loading

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading…
Previous Post

Waƙar “Taimaka Rabbana” ta Sani Sabulu Kanoma

Next Post

Waƙar “Ranar Kilishi Jikar Dikko” ta Mamman Shata Katsina

Next Post
Waƙar “Ranar Kilishi Jikar Dikko” ta Mamman Shata Katsina

Waƙar "Ranar Kilishi Jikar Dikko" ta Mamman Shata Katsina

Farashi da inda za a samu “Shata Ikon Allah!”

Farashi da inda za a samu "Shata Ikon Allah!"

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Odia: What next after the 50th?
  • Chinua Achebe in Hausa: An Interview with Ibrahim Sheme
  • Uzziah J. Alabra: The Man Behind A Free Newsmagazine
  • People Would Dance If Something Negative Happened to Obasanjo
  • Taƙaitaccen tarihin Habibu Sakarci Mai Kukuma (1926-1977) 

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Loading Comments...

    %d