• About
  • Contact
Tuesday, October 6, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Columns Online Musings

Waƙar “Ranar Kilishi Jikar Dikko” ta Mamman Shata Katsina

by IBRAHIM SHEME
August 30, 2018
0
Waƙar “Ranar Kilishi Jikar Dikko” ta Mamman Shata Katsina
Hajiya Halima Usman Nagogo (Kilishi)

Hajiya Halima Usman Nagogo (Kilishi)

0
SHARES
348
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Wannan waƙa, mai amshin “Ranar Kilishi Jikar Dikko”, Mamman Shata ya rera ta ne ga Hajiya Halima Usman (Kilishi), uwargidan Sarkin Daura Muhammadu Bashar (Allah ya jiƙan shi). Jigon waƙar shi ne kambamawa da yabo. A waƙar, Shata ya tuno da yadda aka yi bikin auren Kilishi (ɗiyar Sarkin Katsina Usman Nagogo) da Bashar lokacin yana Wamban Daura.

Wannan waƙa gajera ce, to amma ta ƙunshi abubuwa da yawa.

  1. Ta nuna cewa sarakuna a ƙasar Hausa suna auratayya tsakanin su; 
  2. ta nuna ƙasaitar wannan bikin aure, wato irin babban taron da aka yi na jama’a da motoci da babura da kekuna, da kuma yadda sarakai suke yin babbar kyauta ga maroƙa ko mawaƙan su;
  3. ta taskace mana tarihin al’adar “durbar” da Turawa suka kawo mana, wato hawan dawakai domin nuna al’adun mu;
  4. waƙar ta bada tarihin ita Kilishi a taƙaice, wato Shata ya nuna mana cewa ita ‘yar Sarki ce jikar Sarki;
  5. a waƙar akwai nason addinin Musulunci, musamman ɓangaren karatu da kuma tarihi. Misali, mun fahimci cewa Shata ya san wani abu game da wasu waƙoƙin Larabci, wato irin “Alburda”, da mawaƙan Larabci irin su Alfazazi.

Na rubuta waƙar ne daga wani faifan Shata da na saurara. Na alamta inda aka yi amshi da alamar tauraro, wato *. Bismillah.

Hajiya Halima Usman Nagogo (Kilishi)

SHATA: Ranar Kilishi jikar Dikko.

AMSHI (*)

Ranar Kilishi jikar Dikko.
*

Bukin Kilishi jikar Dikko,
Taron ta sai ka ce an Durbar:
Mota dubu ta je tarbar ta,
Doki dubu ya je tarbar ta,
D.K. dubu ya je tarbar ta,
Ba sa’ikul ba, ba ‘yan ƙas ba,
Tarbar Kilishi jikar Dikko.
*

Rad da Wamban Daura jikan Abdu,
Mamman jikan Sarki Musa,
Jikan Murka da Sarkin Fada,
Jikan Murka da Sarkin Fada,
Ran nan Wambai yab ban mota,
Yac ce don darajar ɗan Hamza,
Sardo Ahmadu jikan Shehu,
Sai ko Kilishi ta ce ita ta ba ni domin Ahmadu jikan Shehu.
*

Daidai, Kilishi jikar Dikko!
*

Kilishi Allah ya ba ki ladan aure,
Da ma ki san gidan Aljanna.
*

Da sauya waƙar Kilishi jikar Dikko,
Yara su na ta dukan fata,
Kiɗan sai ka ce fitah harsashi!
*

Zuba waƙa nikai,
Ni sai zuba waƙa nikai kama da ta Alfazazi,
Kamar ana tamsiri.
*

Zuba waƙa nikai kama da ta Alfazazi,
Kamar ana Alburda.
*

Ta Tatsumburum garin Ɗanyaro,
Waccan Kilishi jikar Mamman,
Waccan Kilishi jikar Mamman,
Wannan Kilishi birnin Dikko,
Wannan Kilishi birnin Dikko,
Kakan ta Shehu ne Usmanu,
Baban ta Shehu ne Usmanu,
Kakan ta kau Muhamman Dikko.
*

Kilishi kakan ta kau Muhamman Dikko.

*

Kilishi kakan ta kau Muhamman Dikko.
*

Allah ya ba ki ladar aure,
Da ma ki san gidan Aljanna.
*

Daidai, Kilishi jikar Dikko.
*

Taron Daura ya kai taro.
Taron Daura ya kai taro.

Loading

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading…
Previous Post

Littafin “Shata Ikon Allah!”

Next Post

Farashi da inda za a samu “Shata Ikon Allah!”

Next Post
Farashi da inda za a samu “Shata Ikon Allah!”

Farashi da inda za a samu "Shata Ikon Allah!"

Adam A. Zango a bangon mujallar Fim

Adam A. Zango a bangon mujallar Fim

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Odia: What next after the 50th?
  • Chinua Achebe in Hausa: An Interview with Ibrahim Sheme
  • Uzziah J. Alabra: The Man Behind A Free Newsmagazine
  • People Would Dance If Something Negative Happened to Obasanjo
  • Taƙaitaccen tarihin Habibu Sakarci Mai Kukuma (1926-1977) 

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Loading Comments...

    %d