Fitaccen ]an jarida kuma marubuci, Malam Ibrahim Sheme ya bayyana cewa ba za a iya samun magajin Abubakar Imam a wannan zamani ba. Ya yi bayanin nan ne a yayin wata tattaunawa da Aminiya ta yi da shi kwanakin baya, a lokacin Arewa House Kaduna, yayin da aka karrama su da kambin tunawa da Abubakar Imam:
AMINIYA: An za~e ka a matsayin ]aya daga cikin wa]anda }ungiyar Al}alam ta karrama domin tunawa da gwarzon marubucin }asar Hausa, marigayi Dokta Abubakar Imam. Me za ka ce game da wannan zave kuma game da wannan rana ta tunawa da Imam?
IBRAHIM SHEME: Ina farin ciki matu}a saboda wannan taro wani abu ne wanda zan ce kusan ni ne na ba da shawarar a yi shi. Abin da ya sa na ce haka shi ne, akwai wani rubutu da na tava yi a jaridar mako-mako ta Weekly Trust, a lokacin ni ne Editan Adabi na jaridar, inda na yi kira da a fito da wasu hanyoyi na karrama Alhaji Abubakar Imam. [aya daga cikinsu shi ne, yin taron shekara-shekara a kan wannan gwarzon marubucin, domin kada tarihi ya kasa yi masa adalci. Mun san tarihi ba zai mance da shi ba, amma dai ya kamata a ri}a tunowa da shi.
Haka kuma, na ce ya kamata a gina gidan yana a intanet, domin a saka ayyukan Abubakar Imam. Na uku, na ce a kafa gidauniya, domin shirya wasu abubuwa kamar gasa da kuma shirya wata cibiya ta Arewa House, inda za a aje wasu ayyuka na Imam, wa]anda mutum zai zo ya gani. Na ce idan yau muna ganin wa]anda suka san shi ido-da-ido, to wata rana ba za mu gan su ba, mu ma da muke ganin su, ba za a gan mu ba. Wa]annan suna daga cikin shawarwarin da na bayar a wannan rubutun, sai iyalin Abubakar Imam suka kira ni, suka ce wa]annan shawarwari sun karve su, yaya za a yi?
Muka kira taro na farko, aka zauna a Zariya, a gidan shi Alhaji Abubakar Imam ]in. Da ni da Farfesa Abdalla, sai su kuma iyalin. A nan ne aka kafa gidauniya da aka sa wa suna Gidauniyar Tunawa Da Abubakar Imam. Bisa ga wannan shawara, Farfesa Abdalla ne ya jagoranci aikin cewa a yi wannan gidan yana na AbubakarImam.com kuma aka yi ta. Wani mutum mai suna Salisu ]anyaro, wanda ke zaune a Amurka, shi ya gina ta kuma aka amshi ayyukan Imam aka zuba.
Sannan kuma iyalin suka bu]e wannan cibiyar a nan Zariya, inda har aka aje wasu daga cikin ayyukansa da suka ha]a da rubuce-rubucensa, rubutunsa na hannu ma, da kamar riguna ko takalma. Wannan abu ya yi armashi, sannan aka ci gaba da cewa za a ci gaba da yin bikin ranar tunawa da Abubakar Imam. Wannan ne ba a samu an yi ba, sai yau ne Allah Ya sa aka fara. To, ka ga ai dole in ce na yi farin ciki, shawarar da na bayar ta yi albarka. Saboda haka muna murna, ba don kawi ni na ba da shawarar ba, sai domin saboda abin da za a yi zai amfani marubuta, musamman masu tasowa.

AMINIYA: Kana ]aya daga cikin ’yan jarida kuma marubuta da suke }o}ari wajen harkar adabi, shin wane ne Abubakar Imam?
SHEME: To, Alhaji Abubakar Imam an fi saninsa a matsayin marubucin Hausa saboda littattafansa da ya rubuta suka shiga duniya amma shi wani mutum ne kuma na daban, wanda yawancin mutane ba su san wannan ba sai idan ana shirya irin wa]annan tarukan. Shi ya sanya na ce ya kamata a yi masa adalci, kada a kalle shi ta fuska ]aya. Baya ga zamansa na marubuci, Abubakar Imam ]an jarida ne, domin za ka iya zama ]an jarida amma ba marubuci ba, wato ba ka rubuta littafi ba.
Za}a}urin ]an jarida ne, kusan yana ]aya daga cikin manyan ’yan jarida a Najeriya ko in ce Afrika ta Yamma, domin ko lokacin da aka fara ]ibar ’yan jaridar Afrika ta Yamma zubin farko domin su ziyarci Ingila, da shi aka tafi. Ba ya je ba ne a matsayinsa na marubuci mai rubuta littattafai, ya je ne a matsayinsa na ]an jarida. Saboda haka a san wannan, ]an jarida ne wanda ya yi Editan jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo.
Na biyu, Alhaji Abubakar Imam malami ne, mutane ba su san wannan ba, domin kuwa masani ne sosai na addini, domin har littattafai ya yi. Shi ne ma ya rubuta littafi mai suna Tambaya Goma Amsa Goma. Domin idan kai ba malami ba ne, ba za ka iya rubuta wannan littafin ba, saboda me, amsoshin tambayoyi ne kan abubuwan da suka shige wa mutane duhu kan addinin Musulunci. Haka kuma, shi ne ya assasa }ungiyar nan ta Jama’atu Nasril Islam. Shi ya ba da shawarar a }ir}ire ta kuma lokacin da Sarkin Musulmi ya kira taro na manyan malaman Arewa, yana ciki. Shi aka na]a a matsayin Babban-Sakatare na wannan }ungiya na farko, don yana malami fa, ba don yana marubuci ko ]an jarida ba, yana cikin malamai, yana da Islamiyya kuma yana koyar da addini.
Sannan Abubakar Imam ]an siyasa ne, shi ne ya ba da shawarar a kafa Jam’iyyar Mutanen Arewa, wadda daga baya ake kiranta NPC. Kuma duk wani zama da aka yi na yaya za a yi a samu mulkin kai, da shi a wajen. Ya halarci taron tsarin mulki a Ingila, ya yi mu’amala da su Gwamna Lugard, ba a matsayinsa na marubucin littafi ko ]an jarida ko malami ba, a’a, a matsayinsa na ]an syasa, wanda ana jin muryarsa ke nan a Arewa, wanda ya isa a ji da shi. Domin idan kai ba ]an siyasa ba ne, ba za a je irin wannan taron da kai ba.
Sannan akwai wasu abubuwa, shi manomi ne. Haka kuma shi ]an gwagwarmayar ’yancin ]an Adam ne, domin shi ne ma Shugaban Hukumar jin Koken Jama’a. Idan ka zo ka same shi zai saurari kokenka, zai je kowane ofis ne abin ya shafa a gwamnati, su kai }ara, su kai kuka domin amso maka ha}}inka.
Saboda haka, Abubakar Imam wani irin mutum ne da ya ha]a abubuwa da yawa, wanda ba kowa ke da irinsu ba. Za ka ga mutum ya yi fice a matsayinsa na ]an siyasa amma iyakarsa ke nan. Wani ya yi fice a matsayin ]an jarida, iyakarsa ke nan. Wani ya yi fice a matsayin malami, nan ka]ai aka san shi. To, Abubakar Imam, za a iya kiran sa da Turanci: “All Rounder.” Sai ku fassara wannan.
AMINIYA: Shin ko akwai yiwuwar a samu magajin Abubakar Imam a wannan zamanin?
SHEME: To, in ka ce magaji, yana da ’ya’ya, yana da iyali wa]anda suka gaje shi ta vangaren abin da ya mallaka, wato kamar gidansa da sauran harkoki nasa na dukiya da kuma cewa su jininsa ne, sun amsa sunansa da sauransu. Amma idan ka kalli wa]ancan abubuwa da na lissafa, ni a ganina, zai yi wuya a samu wani mutum ]aya da ya ha]a wa]annan abubuwa, domin ni ba na kallon Abubakar Imam a matsayin marubuci ka]ai, sai a matsayin wa]annan abubuwan.
Amma idan tambayarka tana nufin Abubakar Imam a matsayinsa na marubuci, kamar yadda koya ya fi ]auka, to ba zai yiwu ba a ce ga wani mutum shi ne magajin Abubakar Imam. Ina da dalili, kuma dalilin shi ne, yanayin zamantakewa da al’ummar da ya zauna a cikinta ko irin karatunsa da tarbiyyarsa, zai yi wuya a samu wani ya samu wa]annan kuma ya zo ya ha]a da irin basirar da Allah Ya ba shi.
Misali, Abubakar Imam ya ji Larabci kamar ra}umin Madina, ya kuma ji Hausa kamar jakin Kano. Idan ka ]auki wa]annan abubuwa biyu, aka ce ga wani mutum ya ji Larabci kuma ya ji Hausa sosai, e, akwai. To amma shi marubuci ne na littattafai na }ir}ira, na hikaya? Kuma a ce wa]annan littattafai da ya rubuta suna haska rayuwar Hausawa ko al’ummar da yake ciki, tare da amfani da wa]annan abubuwan guda biyu? Ni sai in ga yana da wuya, sai dai akwai masu kamantawa.
To shi wannan yun}uri na farko na fara bikin tunawa da Imam a wannan shekara, kana ganin ya wadatar ko kuwa akwai bu}atar gwamnati ta shigo cikin al’amarin nan?
SHEME: Ni sai in ga harkar }ungiya ba harkar gwamnati ba ce, shi ya sa ma ake kiran abin wanda bai shafi gwamnati ba NGO, wato }ungiya mai zaman kanta. Sai dai kam gwamnati ta ba da tallafi, inda za ta iya, idan misali aka samu ko Gwamna ko Shugaban {aramar Hukuma da za su iya ba da tallafi ko ma Shugaban }asa da zai iya ba da tallafi. To, amma akwai ayyukan da gwamnati ta sa gaba, saboda haka ni a ganina, aikin }ungiya aiki ne na mutane, na sa kai, na mutanen da suke da sha’awa.
Misali, a gwamnati ana iya samun wani mutum mai ra’ayin Abubakar Imam, kamar ni, in a gwamnati nake, ka ga ina da ra’ayinsa, idan aka nemi tallafina zan iya ba da wa iya inda }arfina ya }are. Saboda haka, ya kamata a yi havvasa, wa]ancan abubuwan nan da na lissafa, a faro su. Ka ga misali, gidan da aka ware domin yin Cibiyar Abubakar Imam, tun da muka je zuwan farko, ban da wancan taro fa da muka je, mun je an nuna mana cibiyar, amma daga baya gaskiya sai abin ya shiririce, domin ina jin kila ma an kwashe kayan, ko gidan haya ne ma ban sani ba, kila an sake shi. Amma dai ina jin wajen nan yanzu babu shi.
To, ka ga ya kamata a dawo da wannan. Yanzu idan ka je Ingila, marubuci William Shakespeare, a garinsu idan ka je, za ka samu akwai wuri da aka ware, kana shiga wurin, wanda ya kai girman Arewa House Kaduna, za ka ga yanayin zamanin Sarauniya Victoria. Gidajen da aka yi da komai da aka yi, an shirya su ne daidai yanayin mutanen zamanin da ya yi wa rubutu. Da ka shiga wurin, hatta mutanen da suke gilmawa, suna yawo da tufafin da suka sanya, suna nuna irin tufafin da Shakespeare ya rubuta ne a littattafansa.
Sannan akwai taurari na labarunsa, su Macbeth, su Romeo and Juliet da su Julius Caeser da sauran su, mutanen duk sun yi shiga irin tasu. Za ka je ka gaisa da mutum, kamar ka gaisa da Julius Caeser, domin irin shigarsa ya yi da yanayinsa. Wannan ne aikinsa a wurin, don haka aka ]auke shi aiki. Haka kuma duk wasannin kwaikwayon da Shakespeare ya rubuta, ana yin wasanninsu a wurin a kan dave. Mutane kan yanki tikiti, su shiga su kalla. To, irin wa]annan abubuwa ya kamata a yi domin tunawa da Abubakar Imam.
A da can baya an fara, misali a gidan talabijin na NTA an fara yin fina-finan Magana Jari Ce, amma aka zo aka watsar. Yanzu idan kana neman duka wasannin da aka yi, ko a NTA ba za ka samu ba. To, ya kamata a dawo da havvaka ayyukan nan na Abubakar Imam ta wa]annan hanyoyi. Aiki ne na ni da kai da ya kamata mu zo mu yi, domin abin ya fi }afin iyalinsa, sai dai su yi jagora amma dai mu da su, mun zama iyalin Abubakar Imam ta fuskar kasancewarsa marubuci.
![]()


