• About
  • Contact
Wednesday, October 7, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid

by IBRAHIM SHEME
February 17, 2008
0
Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid
0
SHARES
14
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Hajiya Rahama A. Majid tana daga cikin fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ta rubuta littattafan hikaya masu damar gaske, kuma ta ci moriyar su, ciki kuwa har da littafin ta da ta fi so, wato ‘Za Ta Iya.’ A yanzu haka ɗaliba ce a Jami’ar Al-Azhar ta ƙasar Masar. To, kwanan nan ta yi wani hoɓɓasa, inda ta fito da wani jibgegen littafin hikaya mai suna ‘Mace Mutum’, wanda girman sa ya fi na kowane littafin Hausa da aka taɓa bugawa, domin kuwa ya haura shafi 520 ne. Kamfanin Gidan Dabino Publishers ne suka wallafa littafin.

Shin wacece Rahama A. Majid? Menene tunanin ta game da rubuce-rubucen Hausa, da rayuwar mata a ƙasar Hausa, da kuma makarantan littattafan Hausa? Rahma dai za a iya cewa mace ce mai kamar maza, kwari ne babu! Tana da kazar-kazar da nuna ƙwazo da bajinta a duk harkar da ta sa kan ta. Idan aka ce maka za ta iya yin abu kaza na bajinta, to kai da ganin ta ka san za ta iya.

Wannan hirar da za ku karanta, mun yi ta da Rahma ne tun a cikin shekarar 2005, a lokacin da ake ta yin kici-kicin buga littafin ‘Mace Mutum.’ An buga hirar a mujallar Fim ta Nuwamba da Disamba 2005. Kafin mu kawo muku sabuwar hira da marubuciyar, mun ga ya dace ku fara karyawa da wannan, domin kuwa ko me za ta faɗa a yanzu, bai dai wuce wanda ta faɗa a wannan hirar ba.

A sha karatu lafiya.

SHEME: Hajiya Rahama Abdulmajid, mu fara da jin taƙaitaccen tarihin ki.

RAHAMA: Assalamu alaikum. Suna na Rahma Abdulmajid. An haife ni a shekarar 1980 a Agege, Legas, kuma a can na yi makarantar firamare, na fara sakandare, amma daga bisani na ƙarasa karatun sakandare ɗina a Zariya, bayan da aka yi mana canjin wurin aiki a shekara ta 1998. A Zariya ne na yi difloma a Shari’a, ƙarƙashin Jama’atu Nasril Islam.

 

SHEME: A wace makaranta kenan?

RAHAMA: A Jama’atu Institute ne na yi karatun difloma daga shekarar 1999 zuwa 2000. Bayan nan ne na koma gida Legas, na yi kwasakwasai irin na komfuta har zuwa shekarar 2002, lokacin da muka fara cuku-cukun neman tallafin karatu zuwa ƙasar Misra. A halin yanzu ina karatu a Jami’ar Al-Azhar, shekara ta 3 zuwa ta 4, ina ɓangaren Tarihi da Al’adu. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihi na.

 

SHEME: Bari mu koma baya kaɗan; ki gaya mana sunayen makarantun da kika yi na boko.

RAHAMA: Da farko dai na yi makarantar firamare ɗina a KK Primary School da ke Agege ɗin, kuma bayan kammalawa ta a dai nan Agege ɗin na ci gaba a Dairy Farm Secondary School. Wannan kenan ta ɓangaren boko. A ɓangaren Arabiyya kuma na soma a makarantar gidan mu ne da ake ce wa Nubrasul Huda, wacce bayan mun yi sauka na sake shiga wata wadda ake ce mata Rahmatu Islamiyya wadda take Ikeja. Bayan na kammala aji shida sai na wuce Danmarkazul Illumi Islami ta Sheikh Adam El-Uluriy na yi aji 3, lokacin ne kuma ya yi daidai da tafiyar mu Zariya.

SHEME: A bayanin ki, kin ce an haife ki a Legas, to ko za ki iya bayyana asalin jihar ki?

RAHAMA: Gaskiya idan aka cire Legas to sai dai a yi waje da ni, domin mahaifin mu mutumin Sudan ne, mahaifiyar mu kuma ’yar asalin Jihar Adamawa ce. Amma na tashi ne a matsayin cikakkiyar Bahaushiya ko in ce cikakkun Hausawa a gidan mu, domin ita ce al’adar da mahaifin mu ya karɓa tun zuwan sa a matsayin sa na Musulmi.

SHEME: Ku nawa ne a gidan ku, kuma ke ta nawa ce?

RAHAMA: Mu 22 ne, kuma ni ce ta cikon 22 ɗin.

SHEME: Idan muka koma ɓangaren rubutun adabi, da yaushe kika fara yin rubutu?

RAHAMA: Sanannen abu ne ga duk wanda ya yi makaranta a Kudu cewa yaren Nijeriya da zai iya ɗauka zai zama Yarbanci ne. Ni dai Yarbanci na koya kuma shi na iya rubutawa, to amma a wannan lokutan da wasu littattafai ke tashe, akwai wasu gidajen rediyo a Legas ɗin, Sashen Hausa, suna karanta littattafan Hausa, mu kuma mukan ɗan bi. To amma da yake yana ɗaukar sati kafin mutum ya ji ina aka kwana a wannan labarin, to bayan zuwan mu Kano wata ziyara, sai na sayi wasu littattafan na riƙa bi ina karantawa, wanda ta cikin su ne zan iya cewa na koyi Hausa. Kuma abin da ya ja hankali na wajen yin rubutun littafi shi ne wani littafi da na taɓa karantawa, wato ‘In Da So Da Ƙauna’ na Ado Ahmed. A wannan littafi da akwai wani babi na musamman wanda aka ce “Kishi Kumallon Mata.” A gani na, wannan karin magana ta saɓa al’ada, ganin ba mata kaɗai ne suke yin kishi ba. A wannan lokacin ne na fara rubuta duk wani labari da na ji, ko ya zo kai na, a kan kishin maza da na mata. To wannan sai ya zama kamar wani raddi ne a kan wancan karin magana, wanda a kan sa na fitar da littafi na na farko, ‘Wa Ya Fi Kishi?’

Na samu masu ƙalubalanta, suna ta yin kira a kan cewa ya kamata marubuta su juya suna yin rubutu mai yawa saboda a kawo canji a adabin Hausa, ya zamanto ya samu ƙima daidai da adabi na duniya. Sannan kuma abu na biyu, ya zamanto ya kawar da kasala ta karatu, to amma sai aka kasa samun wanda zai bugi ƙirji har yau ya yi, kowa ya koma daga gefe yana jiran wani ya yi tukunna. Sai na ga cewa a wannan lokaci ana buƙatar wani ya bugi ƙirji ya ce bari in je in yi wannan.

SHEME: Wasu na ganin idan suka yi littafi mai yawa, wai ’yan kasuwa ba za su amince ba domin zai yi tsada. Ke ba ki yi tunanin haka ba kika rubuta wannan wagegen littafi?

RAHAMA: Kasuwar littafi tana da alaƙa da kowace ƙa’idar kasuwanci. Ƙa’idar kasuwanci tana buƙatar ka kyautata abu, sannan ka tallata wa jama’a cewa lallai wannan abin mai kyau ne, sannan kuma ka sa ido kan ganin yaya za a yi su saya. To amma kasuwar littattafan mu na Hausa da ake ganin shin za ta tafi ko ba za ta tafi ba? Shin ina ta tsaya tukunna? Littafi zai fito a sati, amma babu wanda ya san zai fito sai marubucin. Wataƙila ma shi mai shagon da za a kai wa littafin domin ya sayar bai san da littafin ba sai a ranar, a wannan lokacin ake tunanin cewa za a iya tantance shin ko wannan littafin yana da kasuwa ko kuma ba shi da shi? Bisa ga tsarin kasuwanci, littafin da ya zamo cewa na ɗaya ko ka kyautata aikin sa, misali tafiyar ka ta baya ta nuna wa mutane cewa e, lallai wannan aikin da gaske kake. Ina ƙoƙarin ganin na tallata littafi na tare da sanar da isowar wannan littafi da inganta aikin sa. Kuma wannan shi ne zai nuna wa mutum cewa e, na gama duk abin da zan iya. Abin da ya yi saura kuma shi ne ƙaddara da za ta biyo baya a kan me littafin ya ƙunsa?

ƙalubalantar sa, kamar yadda “adabin kasuwar Kano” yake da masu ƙalubalantar sa. Haka ma ya ke da waɗanda suke son sa. To wannan ya nuna cewa ba ƙoƙarin fita daga “adabin kasuwar Kano” ba ne, illa cewa ra’ayi na da tunani na shi ne ya yi mani wahayin wannan littafin.

SHEME: Wacce irin alaƙa ce tsakanin ki da masu karatu?

RAHAMA: Alaƙar da ke tsakani na da masu karatu ta fi komai daɗi a wuri na. Na ɗauki masu karatun littafi kamar wani ƙashin baya ne, kuma su ne za su iya gaya maka cewa abin da ka rubuta ya yi daɗi ko kuma an samu kuskure domin ka gyara a rubutun gaba. Hakan ya sa akwai alaƙa mai kyau tsakani na da su.

Alaƙar ki da sauran marubuta fa, domin masu kula da harkokin marubuta na ganin babu alaƙa mai kyau a tsakanin ku marubuta.

Alaƙa tsakani na da mafi yawan marubuta alaƙa ce mai kyau. Ko da yake ni ba a ƙasar nan nake zaune ba, to amma na samu an kafa ƙungiyoyi wanda kuma manufar kafa su shi ne wata ta yi gaba da wata, wanda hakan ko kaɗan bai kamata ba. Amma ni ba na cikin kowace ƙungiya; kusan in ce ni marubuciya ce mai zaman kan ta.

SHEME: Ga shi ke monita ce a wani zauren tattaunawa a intanet a kan rubuce-rubucen Hausa (Majalisar Marubuta). Ko za ki yi mana bayani a taƙaice kan yadda wannan zaure yake, da manufofin sa?

RAHAMA: Wannan yana da labari ne na shiga ta ita ƙungiyar. Kafin in shiga ban san cewa Hausa adabi ba ne wanda yana da masu ƙalubalantar wata kasuwa wadda saboda nisa na da ita, iyakaci na in yi littafi in ajiye, amma da shiga ta wannan ƙungiyar kafin ma in zama monita a ciki na ga waɗannan amfanonin da dama. A cikin wannan majalisar na samu sanin wasu littattafan Hausa da aka yi masu ƙima, da kuma abubuwan da ake ƙalubalantar marubuta da su, sai in je in ɗauka wanda zan gyara ya zamanto cewa na gyara. Sannan kusan zan iya cewa a da ina da ɗan shakku wajen cewa yaya za a yi in yi littafin Hausa mai yawa ya tafi? To amma shiga ta wannan majalisa ya nuna min cewa lallai ashe ana iya yin, kuma zai iya tafiya. Misali, na tarar ana tattaunawa a kan ‘Ruwan Raina,’ wanda a lokacin ban san shi ba, da kuma ‘’Yartsana,’ wanda shi ma ban san shi ba sai a cikin wannan majalisar na samu cewa littattafai ne masu yawan shafuka, kuma aka yi masu kyakkyawan bugu. Sai ga shi ba su samu wata matsala ta kasuwa ba, sannan marubutan da suka yi su sun cancanci yabo.

Saboda haka ina shawartar marubuta da su shiga cikin wannan ƙungiya ko majalisa domin akwai abubuwan ƙaruwa masu tarin yawa; haka ma masu karatu, domin su samu damar ƙalubalantar abin da marubuta suke ciki. Wannan ita ce hanya ta haɗuwa da ’yan’uwan su masu rubutu a tattauna da manazarta waɗanda suka yi fice da fuskantar ina adabin ya dosa. Hakan a gani na zai taimaka wajen kawo cigaba ga ita wannan harka tamu.

SHEME: Yaya kike ganin adabin Hausa zai iya kasancewa nan da wasu shekaru?

RAHAMA: E, ai Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa. Daga cikin kashi biyu, wato marubuta da masu karatu yanzu ya zamanto su ne suke canza adabin Hausa, wanda wannan kuma alamomi ne na nasara. Da farko idan na soma da masu karanta littafi a zamanin baya, kamar ƙarshen ƙarnin da ya wuce, littattafan Hausa suna samun suka domin babbar matsalar da na sha faɗi ita ce masu bayar da saƙon suna da wani saƙo da suka ga cewa lallai ya damu Hausawa, ya kamata kuma a tashi a yi fama da matsalolin, kamar na auren dole da makamantan su, domin haka na da illolin sa na ɓacin ’ya’ya, to amma sai suka manta da wani abu guda ɗaya, wato ba iyayen ba ne suke karanta littafin za su iya kwafar ɓacin da aka nuna a cikin littafin, maimakon iyayen wanda da aka yi wasu wannan salon. Hakan ya janyo ’yan matsaloli waɗanda littattafan baya suka samu kan su a ciki. To amma masu karatun da ake samu a yanzu su ne ’ya’ya na wancan zamanin waɗanda suka karanta kuma su ka ƙaru da wani abu, su ne suka zama iyaye, suke karatu a yanzu. Adabin Hausa ya samu iyaye da ’ya’yan su suna iya karantawa, saɓanin zamanin baya.

Na biyu, masu karatu na da hanyoyin sabuwa ko hulɗa da marubuta kamar ta wayar tafi-da-gdan-ka ko kuma ta intanet, domin yi masu gyare-gyare ko sharhi da makamantan su. Ta ɓangaren marubuta kuma, ban da masu yin canjin sheƙa ma da akwai waɗanda suka ce adabi ko na menene yana da amfani, don haka sun bayar da lokacin su wajen yi wa adabin Hausa hidima wacce ta cancanta za su rubuta da kan su, za kuma su yi kira ga marubuta su ce kuma ku rubuta abu kaza. Saboda haka adabin yanzu idan za mu lura da littattafan da ake rubutawa masu yawan shafuka da kyawu, zai nuna mana cewa duk wani littafi da yake kamar wata annoba ce a cikin adabin Hausa a baya kamar shekara goma, zai zamanto cewa ya kwanta dama.

SHEME: Akwai wani kira da za ki yi ga su marubutan Hausa?

RAHAMA: Kiran dai a kowane lokaci shi ne waɗansu abubuwa ne waɗanda da zarar an same su komai zai daidaita. Marubuci ya kamata ya san cewa ga inda saƙon sa za shi. Na biyu, ana buƙatar marubuci ya san menene adabi. Na uku shi ne menene na saƙo, wato adabin da nake yi wa hidima? Sannan kuma bai kamata marubuci ya yi tsoro ba, ba wai ina nufin sai ranar da marubuci ya fito ya zagi wani babba ba, a’a, tsoron kasuwa ma bai kamata a ce marubuci ya ji shi ba, domin ba a taɓa yin masu yi wa adabi hidima iyakacin sa ya damu da kasuwar sa ba ko inda adabin za shi ba. Don haka ya kamata ya zamanto cewa wannan yana kan gaba.

SHEME: To menene zai biyo bayan ‘Mace Mutum’ daga alƙalamin ki?

RAHAMA: Abin da zai biyo bayan ‘Mace Mutum’ shi ne ina so in ci gaba da yin rubutu a manyan shafuka mai ingantaccen bugu, kuma wanda zai zamanto yana da saƙon da zamanin yake so. Wannan ya sanya ba zan iya sanin menene zai biyo bayan ‘Mace Mutum’ ba, domin ina so ne in kasance kowace shekara a ce da littafin da zai fito, ya zamanto cewa ainahin saƙon da ake buƙata shi littafin ya taho da shi.

SHEME: Yaushe ne za ki kammala karatun ki ki dawo Nijeriya da zama?

RAHAMA: Shekara mai zuwa ne zan kammala karatu na, to amma da yake ina da buƙatar ƙare digiri na na biyu shi ne ya sa ba ni da masaniyar lokacin da zan dawo.

SHEME: A can Alƙahiran ko kuwa?

RAHAMA: E, ko a Alƙahira ko kuma a gaba da ita.

SHEME: A’a, to shi kenan kin dinga karatu? Aure fa?

RAHAMA (ta yi dariya): Ai aure ba ya hana karatu.

SHEME:To yaushe za a yi auren? Wasu za su so sanin haka daga gare ki.

RAHAMA: To ai kada wanda ake so a yi da shi ya ji, kuma ya matsu ya ce an sa maraɗa magana! (ta ƙyalƙyace da dariya)

SHEME: Hajiya Rahama, mun gode.

RAHAMA: To, ni ma na gode.

—–

ƘARIN BAYANI: An sake buga wannan hirar a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a da ta gabata, 15 ga Fabrairu 2008

Loading

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading…
Previous Post

KANO’S CENSORSHIP LAWS

Next Post

BUK Alumni: Karramawar har da ni!

Next Post

BUK Alumni: Karramawar har da ni!

BUK Alumni Honours Leadership Editor

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Odia: What next after the 50th?
  • Chinua Achebe in Hausa: An Interview with Ibrahim Sheme
  • Uzziah J. Alabra: The Man Behind A Free Newsmagazine
  • People Would Dance If Something Negative Happened to Obasanjo
  • Taƙaitaccen tarihin Habibu Sakarci Mai Kukuma (1926-1977) 

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d