• About
  • Contact
Thursday, October 8, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

KOTU TA SOKE BELIN IYAN-TAMA

by IBRAHIM SHEME
August 11, 2008
0
0
SHARES
1
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

A yau ne kotun majistare da ke hanyar zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, karkashin mai shari’a Muktari Ahmed, ta bayar da dokar a kama shahararren mai kamfanin shirya finafinai, wato Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, bisa laifin rashin zuwa kotu a yau, laifin da kotun ta kira tsallake beli.

Alkalin ya ba da oda an kamo Iyan-Tama, aka mayar da shi gidan kaso, har zuwa ranar da kotun za ta kara sauraron karar, wato ran 20 ga Agusta, 2008, kamar yadda lauya mai gabatar da kara, Barista Sanusi Ma’aji, ya bukata a gaban kotun.

Har ila yau, kotun ta ba da dokar cewa a rubuta wa mutanen da su ka sa hannu wajen belin Iyan-Tama a karon farko, takardar sammaci, domin su zo kotun su bayyana dalilin day a hana shi zuwa kotu, kuma ba tare da wani bayani ba. Wadannan mutane su ne Auwalu Yusuf na unguwar Gadanga da kuma Muhammed da ke zaune a unguwar Sarari a birnin Kano.

An gurfanar da Iyan-Tama a gaban kotun ne cikin Mayu bisa tuhumar da Hukumar Tace Finafinai ta ke yi masa na sakin wani fim mai suna ‘Tsintsiya’ wanda kamfanin sa na Iyan-Tama Multimedia ya shirya, wanda kuma ake tuhumar cewa ya sake shi ne ba tare da hukumar ta tace shi ba.

Haka kuma kotun ta tuhumi Iyan-Tama da laifin mallaka tare da tafiyar da kamfanin shirya finafinai wanda ba shi da rajista da hukumar.

A halin yanzu, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama na tsare a gidan kaso har zuwa lokacin da kotun za ta kara zama a ranar 20 ga Agusta 2008.

Loading

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading…
Previous Post

Hiyana: An Yi Suna, An Samu ‘Daddy’!

Next Post

AN SAKO IYAN-TAMA

Next Post

AN SAKO IYAN-TAMA

DEATH THREAT FROM KANO CENSORS

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Odia: What next after the 50th?
  • Chinua Achebe in Hausa: An Interview with Ibrahim Sheme
  • Uzziah J. Alabra: The Man Behind A Free Newsmagazine
  • People Would Dance If Something Negative Happened to Obasanjo
  • Taƙaitaccen tarihin Habibu Sakarci Mai Kukuma (1926-1977) 

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d