{"id":5569,"date":"2017-02-22T23:20:41","date_gmt":"2017-02-22T23:20:41","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5569"},"modified":"2025-06-22T23:33:55","modified_gmt":"2025-06-22T23:33:55","slug":"ba-za-a-iya-samun-magajin-abubakar-imam-ba-ibrahim-sheme","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569","title":{"rendered":"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme"},"content":{"rendered":"<p><em><strong>Fitaccen ]an jarida kuma marubuci, Malam Ibrahim Sheme ya bayyana cewa ba za a iya samun magajin Abubakar Imam a wannan zamani ba. Ya yi bayanin nan ne a yayin wata tattaunawa da Aminiya ta yi da shi kwanakin baya, a lokacin Arewa House Kaduna, yayin da aka karrama su da kambin tunawa da Abubakar Imam:<\/strong><\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong>AMINIYA: An za~e ka a matsayin ]aya daga cikin wa]anda }ungiyar Al}alam ta karrama domin tunawa da gwarzon marubucin }asar Hausa, marigayi Dokta Abubakar Imam. Me za ka ce game da wannan zave kuma game da wannan rana ta tunawa da Imam?<\/strong><\/p>\n<p>IBRAHIM SHEME: Ina farin ciki matu}a saboda wannan taro wani abu ne wanda zan ce kusan ni ne na ba da shawarar a yi shi. Abin da ya sa na ce haka shi ne, akwai wani rubutu da na tava yi a jaridar mako-mako ta <em>Weekly Trust,<\/em> a lokacin ni ne Editan Adabi na jaridar, inda na yi kira da a fito da wasu hanyoyi na karrama Alhaji Abubakar Imam. [aya daga cikinsu shi ne, yin taron shekara-shekara a kan wannan gwarzon marubucin, domin kada tarihi ya kasa yi masa adalci. Mun san tarihi ba zai mance da shi ba, amma dai ya kamata a ri}a tunowa da shi.<\/p>\n<p>Haka kuma, na ce ya kamata a gina gidan yana a intanet, domin a saka ayyukan Abubakar Imam. Na uku, na ce a kafa gidauniya, domin shirya wasu abubuwa kamar gasa da kuma shirya wata cibiya ta Arewa House, inda za a aje wasu ayyuka na Imam, wa]anda mutum zai zo ya gani. Na ce idan yau muna ganin wa]anda suka san shi ido-da-ido, to wata rana ba za mu gan su ba, mu ma da muke ganin su, ba za a gan mu ba. Wa]annan suna daga cikin shawarwarin da na bayar a wannan rubutun, sai iyalin Abubakar Imam suka kira ni, suka ce wa]annan shawarwari sun karve su, yaya za a yi?<\/p>\n<p>Muka kira taro na farko, aka zauna a Zariya, a gidan shi Alhaji Abubakar Imam ]in. Da ni da Farfesa Abdalla, sai su kuma iyalin. A nan ne aka kafa gidauniya da aka sa wa suna Gidauniyar Tunawa Da Abubakar Imam. Bisa ga wannan shawara, Farfesa Abdalla ne ya jagoranci aikin cewa a yi wannan gidan yana na AbubakarImam.com kuma aka yi ta. Wani mutum mai suna Salisu ]anyaro, wanda ke zaune a Amurka, shi ya gina ta kuma aka amshi ayyukan Imam aka zuba.<\/p>\n<p>Sannan kuma iyalin suka bu]e wannan cibiyar a nan Zariya, inda har aka aje wasu daga cikin ayyukansa da suka ha]a da rubuce-rubucensa, rubutunsa na hannu ma, da kamar riguna ko takalma. Wannan abu ya yi armashi, sannan aka ci gaba da cewa za a ci gaba da yin bikin ranar tunawa da Abubakar Imam. Wannan ne ba a samu an yi ba, sai yau ne Allah Ya sa aka fara. To, ka ga ai dole in ce na yi farin ciki, shawarar da na bayar ta yi albarka. Saboda haka muna murna, ba don kawi ni na ba da shawarar ba, sai domin saboda abin da za a yi zai amfani marubuta, musamman masu tasowa.<\/p>\n<figure id=\"attachment_5577\" aria-describedby=\"caption-attachment-5577\" style=\"width: 300px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" data-attachment-id=\"5577\" data-permalink=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?attachment_id=5577\" data-orig-file=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Alhaji_Abubakar_Imam_Kagara.jpg\" data-orig-size=\"720,545\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"Alhaji_Abubakar_Imam_Kagara\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Alhaji Abubakar Imam yana aiki a ofis&lt;\/p&gt;\n\" data-large-file=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Alhaji_Abubakar_Imam_Kagara.jpg\" class=\"size-medium wp-image-5577\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Alhaji_Abubakar_Imam_Kagara-300x227.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"227\" srcset=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Alhaji_Abubakar_Imam_Kagara-300x227.jpg 300w, https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Alhaji_Abubakar_Imam_Kagara.jpg 720w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption id=\"caption-attachment-5577\" class=\"wp-caption-text\">Alhaji Abubakar Imam yana aiki a ofis<\/figcaption><\/figure>\n<p><strong>AMINIYA: Kana ]aya daga cikin \u2019yan jarida kuma marubuta da suke }o}ari wajen harkar adabi, shin wane ne Abubakar Imam?<\/strong><\/p>\n<p>SHEME: To, Alhaji Abubakar Imam an fi saninsa a matsayin marubucin Hausa saboda littattafansa da ya rubuta suka shiga duniya amma shi wani mutum ne kuma na daban, wanda yawancin mutane ba su san wannan ba sai idan ana shirya irin wa]annan tarukan. Shi ya sanya na ce ya kamata a yi masa adalci, kada a kalle shi ta fuska ]aya. Baya ga zamansa na marubuci, Abubakar Imam ]an jarida ne, domin za ka iya zama ]an jarida amma ba marubuci ba, wato ba ka rubuta littafi ba.<\/p>\n<p>Za}a}urin ]an jarida ne, kusan yana ]aya daga cikin manyan \u2019yan jarida a Najeriya ko in ce Afrika ta Yamma, domin ko lokacin da aka fara ]ibar \u2019yan jaridar Afrika ta Yamma zubin farko domin su ziyarci Ingila, da shi aka tafi. Ba ya je ba ne a matsayinsa na marubuci mai rubuta littattafai, ya je ne a matsayinsa na ]an jarida. Saboda haka a san wannan, ]an jarida ne wanda ya yi Editan jaridar <em>Gaskiya Ta Fi Kwabo<\/em>.<\/p>\n<p>Na biyu, Alhaji Abubakar Imam malami ne, mutane ba su san wannan ba, domin kuwa masani ne sosai na addini, domin har littattafai ya yi. Shi ne ma ya rubuta littafi mai suna <em>Tambaya Goma Amsa Goma<\/em>. Domin idan kai ba malami ba ne, ba za ka iya rubuta wannan littafin ba, saboda me, amsoshin tambayoyi ne kan abubuwan da suka shige wa mutane duhu kan addinin Musulunci. Haka kuma, shi ne ya assasa }ungiyar nan ta Jama\u2019atu Nasril Islam. Shi ya ba da shawarar a }ir}ire ta kuma lokacin da Sarkin Musulmi ya kira taro na manyan malaman Arewa, yana ciki. Shi aka na]a a matsayin Babban-Sakatare na wannan }ungiya na farko, don yana malami fa, ba don yana marubuci ko ]an jarida ba, yana cikin malamai, yana da Islamiyya kuma yana koyar da addini.<\/p>\n<p>Sannan Abubakar Imam ]an siyasa ne, shi ne ya ba da shawarar a kafa Jam\u2019iyyar Mutanen Arewa, wadda daga baya ake kiranta NPC. Kuma duk wani zama da aka yi na yaya za a yi a samu mulkin kai, da shi a wajen. Ya halarci taron tsarin mulki a Ingila, ya yi mu\u2019amala da su Gwamna Lugard, ba a matsayinsa na marubucin littafi ko ]an jarida ko malami ba, a\u2019a, a matsayinsa na ]an syasa, wanda ana jin muryarsa ke nan a Arewa, wanda ya isa a ji da shi. Domin idan kai ba ]an siyasa ba ne, ba za a je irin wannan taron da kai ba.<\/p>\n<p>Sannan akwai wasu abubuwa, shi manomi ne. Haka kuma shi ]an gwagwarmayar \u2019yancin ]an Adam ne, domin shi ne ma Shugaban Hukumar jin Koken Jama\u2019a. Idan ka zo ka same shi zai saurari kokenka, zai je kowane ofis ne abin ya shafa a gwamnati, su kai }ara, su kai kuka domin amso maka ha}}inka.<\/p>\n<p>Saboda haka, Abubakar Imam wani irin mutum ne da ya ha]a abubuwa da yawa, wanda ba kowa ke da irinsu ba. Za ka ga mutum ya yi fice a matsayinsa na ]an siyasa amma iyakarsa ke nan. Wani ya yi fice a matsayin ]an jarida, iyakarsa ke nan. Wani ya yi fice a matsayin malami, nan ka]ai aka san shi. To, Abubakar Imam, za a iya kiran sa da Turanci: \u201cAll Rounder.\u201d Sai ku fassara wannan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong>AMINIYA: Shin ko akwai yiwuwar a samu magajin Abubakar Imam a wannan zamanin?<\/strong><\/p>\n<p>SHEME: To, in ka ce magaji, yana da \u2019ya\u2019ya, yana da iyali wa]anda suka gaje shi ta vangaren abin da ya mallaka, wato kamar gidansa da sauran harkoki nasa na dukiya da kuma cewa su jininsa ne, sun amsa sunansa da sauransu. Amma idan ka kalli wa]ancan abubuwa da na lissafa, ni a ganina, zai yi wuya a samu wani mutum ]aya da ya ha]a wa]annan abubuwa, domin ni ba na kallon Abubakar Imam a matsayin marubuci ka]ai, sai a matsayin wa]annan abubuwan.<\/p>\n<p>Amma idan tambayarka tana nufin Abubakar Imam a matsayinsa na marubuci, kamar yadda koya ya fi ]auka, to ba zai yiwu ba a ce ga wani mutum shi ne magajin Abubakar Imam. Ina da dalili, kuma dalilin shi ne, yanayin zamantakewa da al\u2019ummar da ya zauna a cikinta ko irin karatunsa da tarbiyyarsa, zai yi wuya a samu wani ya samu wa]annan kuma ya zo ya ha]a da irin basirar da Allah Ya ba shi.<\/p>\n<p>Misali, Abubakar Imam ya ji Larabci kamar ra}umin Madina, ya kuma ji Hausa kamar jakin Kano. Idan ka ]auki wa]annan abubuwa biyu, aka ce ga wani mutum ya ji Larabci kuma ya ji Hausa sosai, e, akwai. To amma shi marubuci ne na littattafai na }ir}ira, na hikaya? Kuma a ce wa]annan littattafai da ya rubuta suna haska rayuwar Hausawa ko al\u2019ummar da yake ciki, tare da amfani da wa]annan abubuwan guda biyu? Ni sai in ga yana da wuya, sai dai akwai masu kamantawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong>To shi wannan yun}uri na farko na fara bikin tunawa da Imam a wannan shekara, kana ganin ya wadatar ko kuwa akwai bu}atar gwamnati ta shigo cikin al\u2019amarin nan?<\/strong><\/p>\n<p>SHEME: Ni sai in ga harkar }ungiya ba harkar gwamnati ba ce, shi ya sa ma ake kiran abin wanda bai shafi gwamnati ba NGO, wato }ungiya mai zaman kanta. Sai dai kam gwamnati ta ba da tallafi, inda za ta iya, idan misali aka samu ko Gwamna ko Shugaban {aramar Hukuma da za su iya ba da tallafi ko ma Shugaban }asa da zai iya ba da tallafi. To, amma akwai ayyukan da gwamnati ta sa gaba, saboda haka ni a ganina, aikin }ungiya aiki ne na mutane, na sa kai, na mutanen da suke da sha\u2019awa.<\/p>\n<p>Misali, a gwamnati ana iya samun wani mutum mai ra\u2019ayin Abubakar Imam, kamar ni, in a gwamnati nake, ka ga ina da ra\u2019ayinsa, idan aka nemi tallafina zan iya ba da wa iya inda }arfina ya }are. Saboda haka, ya kamata a yi havvasa, wa]ancan abubuwan nan da na lissafa, a faro su. Ka ga misali, gidan da aka ware domin yin Cibiyar Abubakar Imam, tun da muka je zuwan farko, ban da wancan taro fa da muka je, mun je an nuna mana cibiyar, amma daga baya gaskiya sai abin ya shiririce, domin ina jin kila ma an kwashe kayan, ko gidan haya ne ma ban sani ba, kila an sake shi. Amma dai ina jin wajen nan yanzu babu shi.<\/p>\n<p>To, ka ga ya kamata a dawo da wannan. Yanzu idan ka je Ingila, marubuci William Shakespeare, a garinsu idan ka je, za ka samu akwai wuri da aka ware, kana shiga wurin, wanda ya kai girman <em>Arewa House<\/em> Kaduna, za ka ga yanayin zamanin Sarauniya Victoria. Gidajen da aka yi da komai da aka yi, an shirya su ne daidai yanayin mutanen zamanin da ya yi wa rubutu. Da ka shiga wurin, hatta mutanen da suke gilmawa, suna yawo da tufafin da suka sanya, suna nuna irin tufafin da Shakespeare ya rubuta ne a littattafansa.<\/p>\n<p>Sannan akwai taurari na labarunsa, su <em>Macbeth<\/em>, su <em>Romeo and Juliet<\/em> da su <em>Julius Caeser<\/em> da sauran su, mutanen duk sun yi shiga irin tasu. Za ka je ka gaisa da mutum, kamar ka gaisa da <em>Julius Caeser<\/em>, domin irin shigarsa ya yi da yanayinsa. Wannan ne aikinsa a wurin, don haka aka ]auke shi aiki. Haka kuma duk wasannin kwaikwayon da Shakespeare ya rubuta, ana yin wasanninsu a wurin a kan dave. Mutane kan yanki tikiti, su shiga su kalla. To, irin wa]annan abubuwa ya kamata a yi domin tunawa da Abubakar Imam.<\/p>\n<p>A da can baya an fara, misali a gidan talabijin na NTA an fara yin fina-finan <em>Magana Jari Ce<\/em>, amma aka zo aka watsar. Yanzu idan kana neman duka wasannin da aka yi, ko a NTA ba za ka samu ba. To, ya kamata a dawo da havvaka ayyukan nan na Abubakar Imam ta wa]annan hanyoyi. Aiki ne na ni da kai da ya kamata mu zo mu yi, domin abin ya fi }afin iyalinsa, sai dai su yi jagora amma dai mu da su, mun zama iyalin Abubakar Imam ta fuskar kasancewarsa marubuci.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5569\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5569\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Fitaccen ]an jarida kuma marubuci, Malam Ibrahim Sheme ya bayyana cewa ba za a iya samun magajin Abubakar Imam a wannan zamani ba. Ya yi bayanin nan ne a yayin wata tattaunawa da Aminiya ta yi da shi kwanakin baya, a lokacin Arewa House Kaduna, yayin da aka karrama su da kambin tunawa da Abubakar [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5569\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5569\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5573,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-5569","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":11,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Fitaccen ]an jarida kuma marubuci, Malam Ibrahim Sheme ya bayyana cewa ba za a iya samun magajin Abubakar Imam a wannan zamani ba. Ya yi bayanin nan ne a yayin wata tattaunawa da Aminiya ta yi da shi kwanakin baya, a lokacin Arewa House Kaduna, yayin da aka karrama su da kambin tunawa da Abubakar [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2017-02-22T23:20:41+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-06-22T23:33:55+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg?fit=750%2C536&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"750\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"536\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Bashir Yahuza Malumfashi, a Kaduna\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"10 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme\",\"datePublished\":\"2017-02-22T23:20:41+00:00\",\"dateModified\":\"2025-06-22T23:33:55+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569\"},\"wordCount\":1951,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2017\\\/02\\\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569\",\"name\":\"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2017\\\/02\\\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg\",\"datePublished\":\"2017-02-22T23:20:41+00:00\",\"dateModified\":\"2025-06-22T23:33:55+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2017\\\/02\\\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2017\\\/02\\\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg\",\"width\":750,\"height\":536,\"caption\":\"Malam Ibrahim Sheme\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5569#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme - Ibrahim Sheme","og_description":"Fitaccen ]an jarida kuma marubuci, Malam Ibrahim Sheme ya bayyana cewa ba za a iya samun magajin Abubakar Imam a wannan zamani ba. Ya yi bayanin nan ne a yayin wata tattaunawa da Aminiya ta yi da shi kwanakin baya, a lokacin Arewa House Kaduna, yayin da aka karrama su da kambin tunawa da Abubakar [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2017-02-22T23:20:41+00:00","article_modified_time":"2025-06-22T23:33:55+00:00","og_image":[{"width":750,"height":536,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg?fit=750%2C536&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Bashir Yahuza Malumfashi, a Kaduna","Estimated reading time":"10 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme","datePublished":"2017-02-22T23:20:41+00:00","dateModified":"2025-06-22T23:33:55+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569"},"wordCount":1951,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569","name":"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg","datePublished":"2017-02-22T23:20:41+00:00","dateModified":"2025-06-22T23:33:55+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg","width":750,"height":536,"caption":"Malam Ibrahim Sheme"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5569#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Ba za a iya samun magajin Abubakar Imam ba\u00a0\u2013 Ibrahim Sheme"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2017\/02\/Ibrahim-Sheme-750x536-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5569","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5569"}],"version-history":[{"count":7,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5569\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5578,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5569\/revisions\/5578"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5573"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5569"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5569"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5569"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}