{"id":5433,"date":"2024-07-27T21:43:41","date_gmt":"2024-07-27T21:43:41","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5433"},"modified":"2025-11-27T11:33:03","modified_gmt":"2025-11-27T11:33:03","slug":"cikar-shehu-%c9%97ahiru-usman-bauchi-shekara-100","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433","title":{"rendered":"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100"},"content":{"rendered":"<p>A ranar Laraba, 28 ga Yuni, 2024, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1446 Bayan Hijira, mashahurin malamin nan Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi, wanda shi ne jagoran \u0257arikar Tijjaniyya a Nijeriya, ya cika shekara 100 cur da haihuwa. A yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar \u0198oli ta Al&#8217;amuran Musulunci (NSCIA). An haife shi a ranar 28 ga Yuni, 1927, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1346 Bayan Hijira. A tsarin kalandar Bature, a bana Shehi ya cika shekara 97 ne, to amma a lissafin Hijira ya cika shekara \u0257ari cur ne.<\/p>\n<p>Asalin Shehi Bafillace ne wanda aka haifa a garin Nafa\u0257a da ke cikin Jihar Gombe a yau. Mahaifin sa, Gwani Alhaji Usman Adam, babban malami ne, mahaifiyar sa kuma, wato Hajiya Maryam Ar\u0257o Sule, asalin ta daga garin Gamazo da ke Jihar Yobe take, amma a Nafa\u0257a aka haife ta.<\/p>\n<p>A lokacin haihuwar Shehi, garin Nafa\u0257a cibiyar koyon addinin Musulunci ce, kuma mahaifin sa Mu\u0199addam ne, wato shugaba a \u0257arikar Tijjaniyya wadda Shehu Ahmad Al-Tijjani, wanda ya rayu a \u0199arni na 17 miladiyya a \u0199asar Aljeriya, shi ne ya assasa ta. Lokacin da Shehu \u018aahiru yana yaro, ya yi karatu har ya yi haddar Al\u0199ur&#8217;ani a gaban mahaifin sa. Daga nan, bisa shawarar mahaifin nasa, sai ya kutsa kai ya shiga garuruwa domin neman \u0199arin ilimi. Ya yi karatu a \u0199ar\u0199ashin malamai da dama, wa\u0257anda suka ha\u0257a da Shehu Abdul\u0199adir Zariya, Shehu Usman Zangon Barebari, da Shehu Abubakar Atiku. Ya karantu sosai a cikin \u0257arikar Tijjaniyya, wadda a yau take da miliyoyin mabiya a \u0199asashen Afrika da dama har ma da wasu nahiyoyin. \u018aarikar ta samu tagomashi da ya\u0257uwa ne a yankin Afrika ta Yamma sakamakon hidimar da manyan shaihunnai suka yi mata tun bayan wafatin Shehu Ahmad Tijjani, irin su Shehu Umaru al-Futi, Shehu Usmanu \u018aanfodiyo da uwa-uba mashahurin malamin nan \u0257an \u0199asar Senegal, wato Shehu Ibrahim Inyass. A yau, an yi ittifa\u0199in cewa \u0257arikar Tijjaniyya ba ta da jagora da ya wuce Shehu \u018aahiru Bauchi, wanda tun yana matashin malami ya sadu da Shehu Inyass a birnin Kano.<\/p>\n<p>Shehu \u018aahiru Bauchi ya yi auren fari ne a cikin 1948 lokacin yana \u0257an shekara 21 da haihuwa. Allah ya yi masa nasibi wajen \u0257aukar ilimi da ya\u0257a shi, domin tun bai manyanta ba ya shiga \u0199waryar manya ana damawa da shi a fagen ilimi. Kuma ya samu tubarrakin malaman sa ta hanyar yi masu cikakkiyar biyayya, musamman ma dai Shehu Ibrahim Inyass, kuma ya sadaukar da rayuwar sa kacokam ga harkar koyarwa da wa&#8217;azi a duk fa\u0257in Nijeriya. Sunan sa ya ya\u0257u a Afrika ta Yamma ta hanyar watsa wa&#8217;azin sa da aka ri\u0199a yi a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a lokacin azumin watan Ramalana da sauran shirye-shirye na gidan rediyon. A shekarun da suka biyo baya ya kafa makarantu da masallatai a \u0199asashen Afrika ta Yamma. Kai, ayyukan Shehi sun ya\u0257u har zuwa \u0199asashen da ba na Afrika ba, misali Amurka.<\/p>\n<p>Wani abin lura game da Shehi shi ne, bayan tasa sadaukarwar, ya kuma sadaukar da rayuwar iyalin sa da almajiran sa ga hidimar koyarwa da wa&#8217;azantarwa, a ko yaushe suna kira ga Musulmi da su ri\u0199a karatun Al\u0199ur&#8217;ani da Hadisan Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Gidan Shehi a Bauchi, wanda kuma babbar makaranta ce, cike yake da manema ilimi. Haka kuma yana gudanar da aikin agajin jama&#8217;a ta hanyar Gidauniyar Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi. A yayin da ake ta zafafa kiraye-kirayen cewa a hana \u2018almajirci\u2019, wanda mutane da dama suka \u0257auka cewa tsarin barace-barace na \u0199ananan yara ne, Shehi ya yi ho\u0253\u0253asan kafa makarantu a garuruwan da iyayen yara suke saboda iyaye su ri\u0199a ba da gudunmawa wajen kula da &#8216;ya&#8217;yan su da ke karatu a makarantun nasa. Haka kuma an san Shehi da yawan kyautata wa mabiyan sa da mataimakan sa, kai har ma da matafiya. Wata kyakkyawar shaida da ke nuna cewa koyarwar Shehi ta zaman lafiya ce ita ce yadda ba a ta\u0253a jin almajiran sa, duk da \u0257imbin yawan su, a cikin ayyukan ta&#8217;addanci ko tsattsauran ra&#8217;ayi da suka addabi Nijeriya a wannan zamanin ba.<\/p>\n<p>Wani abu da ake saurin tunawa game da dogon zamanin Shehi shi ne rawar da ya taka a cikin zazzafar ta\u0199addamar nan da aka yi tsakanin \u018aarika da yake jagoranta da \u0199ungiyar Izala da marigayi Sheikh Abubakar Mahmood Gumi ya jagoranta, abin da ya jawo rarrabuwar kan al&#8217;ummar Musulmi a zangon shekarun 1980 da na 1990. Wannan rarrabuwar ba ta sa Shehi ya yi sanyin gwiwa ba ko ta karkatar da shi daga hanyar a\u0199idar da yake jagoranta ba. Miliyoyin mabiyan sa, kai har ma masu adawa da shi, sun ci gaba da girmama shi matu\u0199ar girmamawa daga wancan lokacin har zuwa yau \u0257in nan.<\/p>\n<p>Abin farin ciki ne a ce malami irin Shehu \u018aahiru Usman Bauchi ya cika shekaru \u0257ari a raye. Duk da yake a matsayin sa na \u0257an shekara \u0257ari za a ga ya tsufa ya yi tamoji tare da nuna alamun raunin jiki, wanda ba abin mamaki ba ne, to amma \u0199wa\u0199walwar sa ras take, ba ya da mantuwa, kuma muryar sa garau idan yana karatu. Har yanzu babu irin gigicewar nan ta tsufan \u0257an shekara \u0257ari a tare da shi.<\/p>\n<p>Ha\u0199i\u0199anin gaskiya, Shehi ya ba da gudunmawa sosai ga \u0199arfafa Musulunci a Nijeriya, kuma Nijeriya ta ci moriyar aikin da yake yi na tabbatar da zaman lumana da adalci a cikin al&#8217;umma. Ya gina al&#8217;adar karatu da karantarwa, tare da yin kira ga jama&#8217;a da su yi zaman lumana da ha\u0257in kai da juna, da bin tafarkin Manzon Allah \u2013 wanda wannan shi ne gundarin sa\u0199on Islama. A kan haka ake kallon sa a yanzu da ya cika shekara \u0257ari a doron \u0199asa, kuma a hakan za a ci gaba da tuna shi ko bayan babu shi.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5433\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5433\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ranar Laraba, 28 ga Yuni, 2024, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1446 Bayan Hijira, mashahurin malamin nan Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi, wanda shi ne jagoran \u0257arikar Tijjaniyya a Nijeriya, ya cika shekara 100 cur da haihuwa. A yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar \u0198oli ta Al&#8217;amuran [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5433\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5433\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5648,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[434,433],"class_list":["post-5433","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","tag-cika-shekaru-ari","tag-sheikh-ahiru-usman-bauchi"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":173,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100 - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100 - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A ranar Laraba, 28 ga Yuni, 2024, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1446 Bayan Hijira, mashahurin malamin nan Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi, wanda shi ne jagoran \u0257arikar Tijjaniyya a Nijeriya, ya cika shekara 100 cur da haihuwa. A yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar \u0198oli ta Al&#8217;amuran [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-07-27T21:43:41+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-11-27T11:33:03+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg?fit=720%2C633&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"720\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"633\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100\",\"datePublished\":\"2024-07-27T21:43:41+00:00\",\"dateModified\":\"2025-11-27T11:33:03+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433\"},\"wordCount\":1000,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2024\\\/07\\\/20251127_123113.jpg\",\"keywords\":[\"cika shekaru \u0257ari\",\"Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi\"],\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433\",\"name\":\"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100 - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2024\\\/07\\\/20251127_123113.jpg\",\"datePublished\":\"2024-07-27T21:43:41+00:00\",\"dateModified\":\"2025-11-27T11:33:03+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2024\\\/07\\\/20251127_123113.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2024\\\/07\\\/20251127_123113.jpg\",\"width\":720,\"height\":633,\"caption\":\"Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=5433#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100 - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100 - Ibrahim Sheme","og_description":"A ranar Laraba, 28 ga Yuni, 2024, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1446 Bayan Hijira, mashahurin malamin nan Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi, wanda shi ne jagoran \u0257arikar Tijjaniyya a Nijeriya, ya cika shekara 100 cur da haihuwa. A yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar \u0198oli ta Al&#8217;amuran [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2024-07-27T21:43:41+00:00","article_modified_time":"2025-11-27T11:33:03+00:00","og_image":[{"width":720,"height":633,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg?fit=720%2C633&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100","datePublished":"2024-07-27T21:43:41+00:00","dateModified":"2025-11-27T11:33:03+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433"},"wordCount":1000,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg","keywords":["cika shekaru \u0257ari","Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi"],"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433","name":"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100 - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg","datePublished":"2024-07-27T21:43:41+00:00","dateModified":"2025-11-27T11:33:03+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg","width":720,"height":633,"caption":"Sheikh \u018aahiru Usman Bauchi"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=5433#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Cikar Shehu \u018aahiru Usman Bauchi shekara 100"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/20251127_123113.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5433","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5433"}],"version-history":[{"count":8,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5433\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5650,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5433\/revisions\/5650"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5648"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5433"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5433"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5433"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}