{"id":4935,"date":"2019-06-04T22:39:21","date_gmt":"2019-06-04T22:39:21","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4935"},"modified":"2026-01-28T05:45:37","modified_gmt":"2026-01-28T05:45:37","slug":"ta%c6%99aitaccen-tarihin-malam-ibrahim-%c9%97anmani-caji","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935","title":{"rendered":"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em>Malam Ibrahim \u018aanmani Caji a Kaduna a cikin 1974<\/em><\/p>\n<p>Ba a san takamaiman shekarar da aka haifi Malam Ibrahim \u018aanmani Caji ba, amma ana hangen an haife shi ne a tsakanin shekarar 1905 zuwa 1909, wato jim ka\u0257an bayan Turawan mulkin mallaka sun \u0199wace \u0199asar Hausa. Inda za ka gane tsufan sa shi ne ya ta\u0253a fa\u0257a da bakin sa cewa ya fara wa\u0199a ne a wajen shekarar 1927.<\/p>\n<p>Malam Ibrahim \u018aanmani, wanda aka fi sani da Malam \u018aanmani Caji ko Malam \u018aanmani Bauchi, shahararren mawa\u0199in Hausa ne wanda ke ajin farko na maka\u0257a irin su Hamza Caji, Musa Da\u0253alo, Nagelu da Ibrahim Naramba\u0257a. Ya yi fice tun kafin a san da irin su Mamman Shata da Musa \u018aan\u0199wairo. Hasali ma dai, lokacin da ya fara wa\u0199a, Shata yana goye!<\/p>\n<p>An haifi \u018aanmani Caji a Sakkwato. A can ya yi makarantar allo har ya sauke, ya shiga littattafai. Ya yi zurfi \u0199warai a karatu, domin har ya fara zama matashin malami, kafin ya bar gida ya tafi garin Kaduna domin ya gano wani wan sa wanda ya jima da barin gida.<\/p>\n<p>Ba a sani ba ko ya ga wan nasa, amma a Kaduna ne ya fara rera wata wa\u0199a wadda ya shirya daga wani Hadisi na Manzon Allah (s.a.w.), wanda hakan ya sa ya kasance cikin mawa\u0199an bege wa\u0257anda masana adabi ke kiran su \u201cmawa\u0199an madahu\u201d. Su, Hadisi sukan \u0257auka su shirya wa\u0199a a kan shi, kuma a wa\u0199ar su babu ki\u0257a ko \u2018yan amshi. Idan suna yi, sai a ri\u0199a ba su kyautar ku\u0257i ko ta tufafi ko ta abinci. \u018aanmani ya zama mawa\u0199in madahu a wajen shekarar 1927.<\/p>\n<p>Daga Kaduna, sai ya koma Kano inda ya ci gaba da wa\u0199ar Hadisi. A can ya zama yaron mota, yana sana\u2019ar sa yana yin wa\u0199e-wa\u0199en sa na Hadisi. Ran nan sai ubangidan sa da suke aikin mota tare, mai suna Ibrahim Nadada, ya yi sanadin sanya shi fara wa\u0199a da ganga. Yadda abin ya faru shi ne, wasu maka\u0257a suka zo suna ki\u0257an caji a garejin da \u018aanmani yake aiki, sai Ibrahim Nadada ya kira \u018aanmani ya ce masa ya rera wa\u0199ar nan tasa ta Hadisi a ka\u0257a masa ganga. Shi kuma ba ya so, domin shi malami ne, ba maro\u0199i ba. Duk da haka, sai ya rera, ana ba shi ki\u0257a. Tun daga ranar, sai son ya rera wa\u0199a da ki\u0257an caji ya shiga ran shi. Amma idan an ba shi kyauta sai ya \u0199i kar\u0253a domin ba ya so a ce ya zama maro\u0199i.<\/p>\n<p>A wancan zamanin, maka\u0257an da ke tashe a Kano maka\u0257an kotso ne da na caji; su ne ke zuwa fada ko \u0199ofar gidan attajiri su yi wasa su samu ku\u0257i da tufafi. Manyan cikin su dai su ne Hamza Caji da \u0199anen sa Inu Caji, da Musa Da\u0253alo da Nagelo. Mamman Shata? Ina! A lokacin bai ma fara wa\u0199a ba!<\/p>\n<p>\u018aanmani ya koyi ki\u0257an caji daga wa\u0199o\u0199in Hamza Caji har ya kafa tasa rundunar ta masu buga masa ganguna da \u2018yan amshi, wato ya zama maro\u0199i. Ya watsar da aikin mota. Amma fa bai zauna a \u0199ar\u0199ashin Hamza ko Inu \u0257in ba, ya dai \u0257auki samfur \u0257in ki\u0257an Hamza \u0257in ne, ya tafi yana yi har wasu na zaton cewa Hamzan ne. \u018aanmani bai bi wani mawa\u0199i ba.<\/p>\n<p>Wa\u0199ar farko da ya fara yi da ki\u0257an caji, ya ji ta ne a wajen \u201cwani Alhaji\u201d mai wa\u0199ar bege, wanda bai san ko wanene ba. Ya dai ji shi yana rera ta. Abin mamaki, ita wannan wa\u0199a ita ce ta zama wa\u0199ar da ake kira \u201cWa\u0199ar \u018aanmani\u201d, mai amshin \u2018Ya Yi Magani, Mai Sama Ya Ba Da Magani Ba \u0198arya Ba\u2019. A cikin ta ne yake cewa, <em>\u201cA Sakkwato anka haifi Malam \u018aanmani, amma a Kano anka yaye Malam \u018aanmani\u201d.<\/em> Ka ta\u0253a jin inda wa\u0199ar farko ta mawa\u0199i ta zama bakandamiyar sa? Sai a wannan wa\u0199a ta \u018aanmani Caji. Wannan wa\u0199a dai ita ce wadda ta sa \u2013 wato ta yi \u201c<em>inspiring<\/em>\u201d \u2013 Malam Aliyu Namangi ya rera wa\u0199ar sa ta \u2018Basukur, Hawan Ka Sai Mai Zanzaro\u2019.<\/p>\n<p>A matsayin sa na mawa\u0199i, Malam \u018aanmani ya yi tafiye-tafiye cikin Nijeriya, daga Arewa har Kurmi. Kuma ya je Kamaru da Nijar. A Kamaru ma ya zauna a \u0199ar\u0199ashin Shugaban \u0198asa Ahmadu Ahidjo, har ya yi gidan kan sa a Gamdare. A can ya kasance mai masaukin ba\u0199in maro\u0199a da ke zuwa Kamaru daga Nijeriya domin su ci arzikin Ahidjo.<\/p>\n<p>Tun a zamanin Sardauna ne Malam \u018aanmani ya yi gida a Bauchi inda ya ci gaba da zama tare da iyalin sa har zuwa \u0199arshen rayuwar sa. A gidan sa akwai makarantar allo, kuma shi ma yakan koyar. A yanzu haka a gidan akwai wata tsohuwa, jikanyar sa, tana zaune tare da wasu dangin su a cikin gidan. \u018aaya daga cikin sanannun wa\u0199o\u0199in \u018aanmani ita ce wa\u0199ar Sarkin Bauchi Alhaji Adamu Jumba mai taken \u2018Mai Rabo Ga Allah \u018aan Sanda Mai Martabobi\u2019.<\/p>\n<p>Wasu wa\u0199o\u0199i fitattu na Malam \u018aanmani sun ha\u0257a da wa\u0199ar Sarkin Mubi mai taken, \u2018Babban Bajimi Mai Ratsa Maza, \u018aan Garba Shiri Nai Yai Da\u0257i\u2019, da \u2018Wa\u0199ar Shede\u2019, da wa\u0199ar Ahidjo, da kuma wata wadda ta \u0199ara fito da shi, wato wa\u0199ar \u2018Ayyaraye Akwara\u2019, wadda ya \u0199ir\u0199ira a garin Gusau. Wannan wa\u0199a ta \u2018Akwara\u2019 ta ja hankalin mutane matu\u0199a domin ya yi ta ne babu ki\u0257a. Ana ma jin cewa ita ce ta saka wa Shata tunanin yin wa\u0199a babu ki\u0257a shi ma, wato wa\u0199ar \u2018Kwalam!\u2019 da ma wani samfur na bakandamiyar sa. Dalilin fa\u0257in haka shi ne \u018aanmani ya yi wa\u0199ar \u2018Akwara\u2019 ne tsawon lokaci kafin Shata ya yi nasa babu ki\u0257a. A cikin \u2018Akwara\u2019 yakan ce:<\/p>\n<p><em>\u201cDa\u0257in duniya tuwo, da\u0257in duniya fura ba fa da\u0257in ba kenan,<\/em><\/p>\n<p><em>Da\u0257in duniya ka hau doki har kana ta gama, ba fa da\u0257in ba kenan,<\/em><\/p>\n<p><em>Da\u0257in duniya sa girken sa\u0199i da wando, ba da\u0257in ba kenan,<\/em><\/p>\n<p><em>Da\u0257in duniya kai kwance da masoyi ka karye ka \u0257an yi tuma!<\/em><\/p>\n<p><em>Mai kaza ba zai ci kai da \u0199afa ba, sai dai a sake rabo.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Idan kun tuna, Garba Liyo mai kukuma ma ya \u0257auki wa\u0257annan kalmomin ya rera wata wa\u0199ar sa da su, inda yake cewa:<\/p>\n<p><em>\u201cDa\u0257in duniya tuwo, ba da\u0257i ba ne ba,<\/em><\/p>\n<p><em>Da\u0257in duniya fura, ba da\u0257i ba ne ba,<\/em><\/p>\n<p><em>Da\u0257in duniya zama da masoyin ka.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Tun sama da shekaru arba\u2019in da suka gabata, Malam \u018aanmani ya hango ta\u0253ar\u0253arewar sana\u2019ar ro\u0199o da ka\u0257e-ka\u0257en gargajiya. A wata hira da Adamu Salihu ya yi da shi a Yerwa, Maiduguri, aka watsa a gidan Rediyo Talbijin Kaduna a cikin 1966, mawa\u0199in ya bayyana cewa ka\u0257e-ka\u0257en gargajiya suna gushewa, duk da yake akwai masu son su.<\/p>\n<h5>RIGIMA DA SHATA<\/h5>\n<p>Ba zan rufe ba sai na ce wani abu kan wani al\u2019amari wanda ya \u0199ara fito da sunan Malam \u018aanmani, wato rigimar su ko cacar bakin da suka yi da Alhaji Mamman Shata Katsina. Kamar yadda na labarta a littafin tarihin Shata mai suna \u2018Shata Ikon Allah!\u2019 hakan ta faru ne sanadiyyar adawar da \u018aanmani ya yi da wata wa\u0199a da Shata ya yi, mai taken \u2018Na Ga Sakarci Wurin Karuwai\u2019, a kan korar karuwai daga Kano da Sarki Muhammadu Sanusi ya yi, har \u018aanmanin ya maida masa da martani. Shata ya zafafa lamarin duk da yake bai kai inda ake tsammani ba. Ya yi wa \u018aanmani zambo fiye da biyu a kan lamarin, har abin ya zama kamar cin \u0199wan makauniya. Zambon farko shi ne \u2018Don Sallah Da Salatil Fatih, Don Allah Mata Ku Bi Aure\u2019. Hasali ma dai a cewar Shata, kafin lokacin bai ta\u0253a yi wa kowa zambo muraran ba. Kuma ma a binciken da na yi, Shata ba ya kama sunan mutumin da ya yi wa zambo kai-tsaye, sai dai ya sakaya ko ya kwatanta, amma sai a kan Malam \u018aanmani.<\/p>\n<p>A nazarin da na yi wa lamarin, ce-ce-ku-cen Shata da \u018aanmani yana da tarihi daban, ba wai kan wa\u0199o\u0199in korar karuwai ba ne. Tun daga bikin \u2018yan Sarki da aka yi a Kano a farkon shekarun 1950, inda Shata ya cinye kasuwar, aka \u0199ulla adawa wadda ta zama gaba a tsakanin sa da kusan dukkan maka\u0257an caji, wa\u0257anda har ya kama sunayen su a wata bakandamiyar sa, wato su \u018aanmani Caji, Hamisu da Da\u0253alo. Ya yi masu haka ne ganin \u0199ulle-\u0199ullen da suka yi masa don hana shi haskawa a bikin \u2018yan Sarki. Haka kuma maka\u0257an caji na jin haushin yadda Shata ya kar\u0253e fada a Kano, a matsayin sa na maka\u0257in kalangu, domin kafin hasken sa a Kano manyan maka\u0257a a \u0199asar Hausa su ne na caji da na kotso, musamman a gidajen sarakai; sai ga Shata ya kutso da kalangu ya ture su gefe \u0257aya.<\/p>\n<p>Don haka, ba abin mamaki ba ne da \u018aanmani, wanda ake masa kallon malamin allo a cikin da\u2019irar mawa\u0199a, ya yi musu da Shata kan korar karuwai. Wani abu kuma shi ne a lokacin, \u018aanmani ne sarki ko gogarma a fagen ki\u0257an caji, musamman tunda Hamza da Da\u0253alo sun kauce. Amma saboda Shata Shata ne, wannan cacar bakin ta \u0199ara fito da \u018aanmani.<\/p>\n<p>Kada mu manta, Shata ya yi irin wannan adawar da wani gungun maka\u0257an da suka ta\u0253o shi, har abin ya jawo ce-ce-ku-ce da hayagaga, wato maka\u0257an kukuma da banjo, wa\u0257anda ya kira sana\u2019ar su da \u201cwargin yara\u201d inda ya ce: <em>&#8220;Na gane banjo da kukuma wargin yara ne, \/ Su ci abinci kowane yai shakwara yai jamfa, \/ In sun samu kur\u0257i yai auren zamani.&#8221;<\/em> Ahmadu Doka ya ba shi amsa, daga baya kuma ya yi nadamar hakan.<\/p>\n<p>Malam \u018aanmani ya yi tsufan sa a Bauchi, ta yadda har wasu na tsammanin \u0257an asalin Bauchi ne. Sunan sa ma \u018aanmani Bauchi.<\/p>\n<p>Ban binciko shekarar da Malam \u018aanmani ya rasu ba, amma na san a Bauchi ya rasu a lokacin da tsufan sa ya kai tsufa matu\u0199a.<\/p>\n<p>Allah ya rahamshe shi, amin.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4935\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4935\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Malam Ibrahim \u018aanmani Caji a Kaduna a cikin 1974 Ba a san takamaiman shekarar da aka haifi Malam Ibrahim \u018aanmani Caji ba, amma ana hangen an haife shi ne a tsakanin shekarar 1905 zuwa 1909, wato jim ka\u0257an bayan Turawan mulkin mallaka sun \u0199wace \u0199asar Hausa. Inda za ka gane tsufan sa shi ne [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4935\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4935\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":4936,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[280,279,281,19],"class_list":["post-4935","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","tag-bauchi","tag-danmani-caji","tag-makaan-hausa","tag-mamman-shata"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":53,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"&nbsp; Malam Ibrahim \u018aanmani Caji a Kaduna a cikin 1974 Ba a san takamaiman shekarar da aka haifi Malam Ibrahim \u018aanmani Caji ba, amma ana hangen an haife shi ne a tsakanin shekarar 1905 zuwa 1909, wato jim ka\u0257an bayan Turawan mulkin mallaka sun \u0199wace \u0199asar Hausa. Inda za ka gane tsufan sa shi ne [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2019-06-04T22:39:21+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2026-01-28T05:45:37+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg?fit=107%2C300&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"107\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"300\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji\",\"datePublished\":\"2019-06-04T22:39:21+00:00\",\"dateModified\":\"2026-01-28T05:45:37+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935\"},\"wordCount\":1756,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/10\\\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg\",\"keywords\":[\"Bauchi\",\"Danmani Caji\",\"maka\u0257an Hausa\",\"mamman shata\"],\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935\",\"name\":\"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/10\\\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg\",\"datePublished\":\"2019-06-04T22:39:21+00:00\",\"dateModified\":\"2026-01-28T05:45:37+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/10\\\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/10\\\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg\",\"width\":107,\"height\":300},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4935#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji - Ibrahim Sheme","og_description":"&nbsp; Malam Ibrahim \u018aanmani Caji a Kaduna a cikin 1974 Ba a san takamaiman shekarar da aka haifi Malam Ibrahim \u018aanmani Caji ba, amma ana hangen an haife shi ne a tsakanin shekarar 1905 zuwa 1909, wato jim ka\u0257an bayan Turawan mulkin mallaka sun \u0199wace \u0199asar Hausa. Inda za ka gane tsufan sa shi ne [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2019-06-04T22:39:21+00:00","article_modified_time":"2026-01-28T05:45:37+00:00","og_image":[{"width":107,"height":300,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg?fit=107%2C300&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji","datePublished":"2019-06-04T22:39:21+00:00","dateModified":"2026-01-28T05:45:37+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935"},"wordCount":1756,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg","keywords":["Bauchi","Danmani Caji","maka\u0257an Hausa","mamman shata"],"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935","name":"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg","datePublished":"2019-06-04T22:39:21+00:00","dateModified":"2026-01-28T05:45:37+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg","width":107,"height":300},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4935#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Ta\u0199aitaccen Tarihin Malam Ibrahim \u018aanmani Caji"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/IMG-20200725-WA0000-2.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4935","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4935"}],"version-history":[{"count":4,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4935\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5658,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4935\/revisions\/5658"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4936"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4935"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4935"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4935"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}