{"id":4738,"date":"2007-08-29T13:27:05","date_gmt":"2007-08-29T13:27:05","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4738"},"modified":"2023-09-06T13:40:24","modified_gmt":"2023-09-06T13:40:24","slug":"ashe-naramba%c9%97a-bai-mutu-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738","title":{"rendered":"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba!"},"content":{"rendered":"<p>Duk wanda ya san abin da ake kira \u201cwa\u0199ar Hausa,\u201d to ya san Maka\u0257a Ibrahim Naramba\u0257a. Hasali ma dai akwai muhawara \u0199wa\u0199\u0199wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Naramba\u0257a da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Naramba\u0257a yawan wa\u0199o\u0199i ne kurum amma Naramba\u0257a ya fi zala\u0199a da fasaha, wasu na cewa ai shi Shata ya kere Naramba\u0257a, musamman da yake shi wa\u0199o\u0199in sa kowa zai iya fahimtar su \u2013 Basakkwace da wanda ba Basakkwace ko Bazamfare ba.<\/p>\n<p>A bara, wasu matasa sun \u0199addamar da kammalallen tarihin Shata, wanda hakan ya \u0199ara taimakawa wajen fahimtar ko waye mawa\u0199in. Shi kuwa Naramba\u0257a, yawancin wa\u0257anda su ka san shi, sanin shanu su ka yi masa. Kuma yawancin Hausawa su kan kasa gane wasu kalamai na wa\u0199o\u0199in sa, musamman wa\u0257anda ba su fito daga tsohon yankin \u0199asar Sakkwato ba. Bugu da \u0199ari, in ban da ta\u0199aitaccen tarihin sa da Farfesa Sa\u2019idu Muhammad Gusau na Jami\u2019ar Bayero ta Kano ya rubuta a littafin sa &#8216;Maka\u0257a Da Mawa\u0199an Hausa&#8217;, ba kowa ba ne zai ce maka ya san tarihin wannan fasihin mawa\u0199in.<\/p>\n<p>To, yanzu dai an taki sa\u2019a, domin kuwa aiki ya yi nisa wajen tattara kammalallen tarihin Naramba\u0257a. Kuma sai aikin ya fa\u0257a a hannun \u0257an gida, wanda ya san kan al\u2019amarin, wato Farfesa Aliyu Bunza.<\/p>\n<p>Shi dai Farfesa Bunza, fitaccen manazarci ne a \u0199asar Hausa. Ya yi rubuce-rubuce kan adabi da kuma al\u2019adun Hausawa, har ma da wasu wa\u0199o\u0199i na baka da kuma rubutattu. A yanzu shi ne ke rubuta tarihin Maka\u0257a Naramba\u0257a.<\/p>\n<p>Shin yaya wannan aiki nasa ya ke ciki? A ranar Lahadi da ta wuce, an yi hira da Farfesa Bunza, wanda babban malami ne a Jami\u2019ar Usmanu \u018aanfodiyo da ke Sakkwato, a sashen Hausa na gidan rediyon BBC. Wakilan gidan rediyon sun zanta da shi lokacin da ya je London kwanan nan. Mu a nan <em>Leadership Hausa<\/em> mun kalato maku wasu muhimman bayanai daga cikin wannan zantawa tasu ta musamman kan aikin da ya ke yi na rubuta tarihi da wa\u0199o\u0199in marigayi Alhaji Ibrahim Naramba\u0257a.<\/p>\n<p>Tun da farko sun sako wa\u0199ar Naramba\u0257a mai taken, \u201cMasu Gari Mazan Tabas Tsayayye, Sarkin Rwahi Ya Wuce A Ram Mai.\u201d Idan kun tuna, a wannan wa\u0199ar ce maka\u0257in ke cewa, \u201cGa wani \u0257an sarki da kunnuwa da hwa\u0257i&#8230;\u201d<\/p>\n<p>An tambayi Malam Bunza ya fa\u0257i wani abu kan wa\u0199ar. Sai ya amsa, \u201cSarki ne aka wa wa\u0199ai na Kuryar Dambo, ba Kurya ta Madaro ba. Ma\u2019ana, Kurya guda biyu mu ke da su a Zamfara: akwai wannan Kurya ta Madaro, akwai waccan Kuryar Dambo. To hakimin Kuryar Dambo ne ya ka wa wa\u0199a. Kuma wannan cewa \u2018Da takobi da garkuwa da ya\u0199i,\u2019 daga cikin \u0199a\u2019idar nazarin wa\u0199a, &#8216;lugude&#8217; mu ke kiran sa &#8211; luguden tarihi. Wani tarihi ne ya narke wurin, tarihin wani sarkin \u0257an tauri ne da aka yi a Kurya mai suna Mamman Ina, da ya kashe wani Bature. To shi ya sa ya ke cewa \u2018Kurya akwai mazan hwa\u0257a da arna&#8217;.&#8221;<\/p>\n<p><strong>BBC: Abin da ya sa na yi maka wannan tambaya, a da a Zariya idan mu ka ji wannan wa\u0199a akwai wani gari Kauru a kusa da Zariya, mun \u0257auka shi ake wa wa\u0199ar da ya ke cewa Makauru. Ashe ba Kauru ba ne. Wai me ake cewa ne a wurin? Ka san wani \u0257an sar\u0199e-sar\u0199e ne.<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Ai da ya ke cewa ya ke yi, \u201cAi Kurya ta Dambo ta Makauru an nan, \/ Zamfara babu makaye kama tai.\u201d<\/p>\n<p><strong>BBC: Za mu so ka \u0257an ba mu tarihin Naramba\u0257a, wata\u0199ila mutanen zamani ba su san ko wanene ba.<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Marigayi Naramba\u0257a shahararren mawa\u0199i ne a duniya. Kuma idan za a yi tarihin Ibrahim Naramba\u0257a, bisa \u0199a\u2019idar ilmi sai an wa mutane da yawa tambaya wa\u0257anda su ka gabace ni a cikin wannan fagen, kamar Farfesa Sa\u2019idu Muhammad Gusau, ya yi bincike musamman a kan Naramba\u0257a; Bello Sodangi ya yi bincike musamman a kan Naramba\u0257a; Sama\u2019ila Yawuri Mazawaje shi ma ya yi bincike musamman a kan Naramba\u0257a.<\/p>\n<p>To, sunan Naramba\u0257a na yanka Ibrahim. Sunan uban sa Maidangwale, shi kuma Maidangwale mutumin Nijar ne, cikakken \u0257an kokawa ne. Amma Naramba\u0257a ya gaji ki\u0257i wajen uwar sa. Don haka shi <em>karen maka\u0257a<\/em> ne kenan; uban sa bai yi ki\u0257i ba. An haife shi a garin Tubali, ya yi karatu a nan, ya rayu a nan, ya tashi a matsayin ba \u0257an gadon wa\u0199a ba. Ya iske kayan kotson ki\u0257in kakan sa na wajen uwa a \u0257akin mahaifiyar sa. Mahaifin sa mutumin \u0199asar Filinge ne, ya zo a garin Tubali, ya auri uwar Naramba\u0257a. Kuma ga shi shahararren \u0257an kokawa ne.<\/p>\n<p>Sai Naramba\u0257a ya \u0257auki kayan ki\u0257in mahaifin uwar sa ya fara ki\u0257an noma. To, wata shekara a fadar Sarkin Gobir na Isa ya yi ki\u0257in noman \u0199auyen su. Da jin yadda da\u0257in wa\u0199a ya ke da zala\u0199a da \u0199warewa, su ka ce ya fi \u0199arfin \u0199auye, sai aka mai da shi birni. Ya tashi daga mawa\u0199in noma ya koma maka\u0257in Gobir. Ka ji tarihin zuwan sa.<\/p>\n<p>BBC: Wato wannan ne kenan ya sa ya koma maka\u0257in na fada, na sarakuna.<\/p>\n<p>BUNZA: Gaba \u0257aya saboda an ga hikimar ta hi \u0199arhin ta manomi, dole sai an mai da shi fada. Don haka ya dawo ya ci gaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir wa\u0199a.<\/p>\n<p><em>(BBC sun sako wa\u0199ar \u201cYa Ci Maza Ya Kwan Ya Na Shire, Uban Zakara, Dodo Na Ummaru\u201d)<\/em><\/p>\n<p><strong>BBC: To Farfesa Bunza, me za ka ce dangane da wannan wa\u0199a?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Wannan wa\u0199a ta Sarkin Gobir ta na cikin manya-manyan wa\u0199o\u0199in da ya yi masa. Kuma wannan wa\u0199a ce wasu su ke ganin gabanin Naramba\u0257a ya yi bakandamiyar wa\u0199ar sa. Don a ciki har Naramba\u0257a na cewa duk abin da zai fa\u0257a ga Sarkin Gobir daidai ne, ba kure ba ne:<\/p>\n<p><em>\u201cNa aje \u0199arya ko ina ki\u0257i,<\/em><\/p>\n<p><em>Na bar \u0199arya ko ina ki\u0257i,<\/em><\/p>\n<p><em>Nai sittin, saba\u2019in ni ka hwa\u0257a,<\/em><\/p>\n<p><em>Mai saba\u2019in yai \u0199arya ana ta zun\u0257e nai,<\/em><\/p>\n<p><em>Ko yaran da ag garai duw wawwatse mashi su kai,<\/em><\/p>\n<p><em>Ya na yawo shi \u0257ai baram-baram.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Saboda haka, a cikin wannan wa\u0199ar ba mu zaton mu ji abin da ya sa\u0253a wa gaskiya. Don haka ne mu ke ganin wannan wa\u0199a ta Sarkin Gobir na cikin manyan wa\u0199o\u0199in sa. Amma dab baya da yai bakandamiya, sai ta shahe hasken ta.<\/p>\n<p><em>(BBC sun sako wa\u0199ar \u201cBatun Da Akai Na Yau Babu Sarki Yau Irin Ka,\/ Jikan Bello Arna Su Na Shakkak Ka\u201d)<\/em><\/p>\n<p><strong>BBC: Farfesa, ko wanda bai san Narambada ba ya san mutum ne wanda Allah ya ba basira. To amma kuma kamar yadda kowa ya sani, akwai shahararrun mawa\u0199a wa\u0257anda su ma sun yi suna. Ko dai kamar Naramba\u0257an ko kusa da shi. Me ya sa ka \u0257auki Naramba\u0257a a matsayin wanda za ka yi bincike a kai?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Akwai dalilai da yawa. Na farko shi ne, fitattun mawa\u0199an Hausa da mu ke da su \u0199asar Hausa an fara bincike a kan su \u2013 ko bincike ne na jami\u2019a, ko ma na gida ne, duk dai an yi. Shata an yi aiki a kan sa. Farfesa Sa\u2019idu Muhammad Gusau ya yi bincike kan Salihu Janki\u0257i. To, na ke ganin a dukkanin \u0199asar Zamfara ba a yi mawa\u0199in da ya kai Naramba\u0257a ba. Kuma ba a \u0199asar sa kawai ya ke wa\u0199a ba. Ma\u2019ana, duk duniyar \u0199asar Hausa. Amma abin takaici, idan an zo neman wa\u0199o\u0199i nai babu, sun wawwatse, ba a samun su. Ba a san tarihin sa ba, ba a san ina ya hito ba, ba a san hikimar sa da zala\u0199ar sa ba. Sai na ga ya na da kyau a yi wani aiki da a\u0199alla zai fito da shi, zai fito da falsafar sa, zai fito da wa\u0199o\u0199in sa, da wa\u0257anda ya yi wa wa\u0199o\u0199in, shi ma ya kasance wani taska daga cikin taskar adabin Hausa da za a aje.<\/p>\n<p><strong>BBC: Ban tari numfashin ka ba. Wasu kalmomi da Naramba\u0257a ke amfani da su a cikin wa\u0199o\u0199in sa, idan ba fassara wa mutum aka yi ba, ba a fahimtar abin da ya ke fa\u0257i. Ina ganin wannan ma ya na da mahimmanci a yi irin wannan bayani da ka yi. To zuwa yanzu ka rubuta wa\u0199o\u0199in sa guda nawa?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Sai dai in ce na samu wa\u0199o\u0199i guda nawa? In na samo su sai in rubuta su\u2026<\/p>\n<p><strong>BBC: Ban tari numfashin ka ba, rubutawar ka na rubuta duk abin da aka ce a cikin wa\u0199a?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: E, zan yi \u0199o\u0199ari duk abin da ya ce, zan yi \u0199o\u0199ari in rubuta kuma a irin lafazin da ya fa\u0257a. Kamar Sarkin Rafi, ai Sarkin <em>Rwahi<\/em> ya ke cewa. Ni ma <em>Rwahi<\/em> zan rubuta.<\/p>\n<p><strong>BBC: Wa\u0199o\u0199i nawa ka samu zuwa yanzu?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Wasu su kan ce ya yi wa\u0199o\u0199i sun kai \u0257ari ko \u0257ari da wani abu, amma iyakar binciken da mu ka yi, kusan sama da shekaru ashirin da wani abu, gaskiya ni hamsin na samu, wa\u0257anda na rubuta da kai na, na saurara, na tabbatar sun rubutu, na ajiye.<\/p>\n<p><strong>BBC: Wa\u0257anda aka \u0257auke su da faifai kenan?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Ma\u2019ana, shahararrun wa\u0199o\u0199in da aka sani a kaset, ba dab bakin wani aka ji su aka rubuta ba.<\/p>\n<p><strong>BBC: Dangane da wa\u0199o\u0199i ko mawa\u0199an Hausa, kamar Alhaji Mamman Shata ana cewa ya na tsayawa nan take ya yi wa\u0199a, don an sha gwada shi, ba tare da ya zauna ya shirya ta ba. Shin Naramba\u0257a ya yake tsara wa\u0199o\u0199in sa?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Wato ko wane irin mawa\u0199i da irin fasaha da hikima da zalaka da Allah ya hore masa. Allah ya hore masa wa\u0199a, amma shi (Naramba\u0257a) ba a nan take ya ke yin ta ba. Idan zai yi maka wa\u0199a, zai je gida ya tsara ta; a yinin da zai yi wa\u0199ar, ba zai yi hul\u0257a da kowa ba. Haka wasu yaran sa su ka shaida mana. In ya \u0199are tsara ta, sai ya kira yaran sa, sai su rera. Wa\u0199ar Naramba\u0257a in zai yi ta, zuba wa\u0199a ake zube-ban-\u0199warya.<\/p>\n<p><strong>BBC: Kamar yadda ya ce ta Alfazazi\u2026<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Cewa ya yi:<\/p>\n<p><em>\u201cKullum ji ni kai azanci na hudo min,<\/em><\/p>\n<p><em>Sai zuba wa\u0199a ni kai kama da ta Alfazazi.\u201d<\/em><\/p>\n<p><strong>BBC: Rubutawa ya ke yi?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Naramba\u0257a ba ya rubuta wa\u0199a, sai ya samu gindin wa\u0199a ya fara. Da ya \u0199are abi nai cikin zuciya, sai ya kira yara nai ya ce, \u201cTo, ga amshin wa\u0199a kaza,\u201d su ri\u0199a yi a sannu ana maimaitawa. Sai ya \u0199are sai aje a yi ta.<\/p>\n<p><strong>BBC: Wa\u0199ar Al\u0199ali Abu fa? Shin wanene Al\u0199ali Abu \u0257in nan?<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Al\u0199ali Abu asali mutumin \u0198auran Namoda ne, al\u0199alanci ya kai shi Moriki, kuma daga cikin \u2019ya\u2019yan sa akwai wanda ke raye a Sokoto yanzu. Amma dai zuri\u2019ar na can a \u0198aura. Ba Al\u0199ali Abubakar Mahmud Gumi ba ne kamar yadda mutane su ke zato. Ya yi masa wannan wa\u0199a a kan irin adalcin sa, gogewar sa da sanin shari\u2019a.<\/p>\n<p><em>(BBC sun sako wa\u0199ar \u201cAl\u0199alin Al\u0199alai Ta Aiki Nai Da Tsari\u2026\u201d)<\/em><\/p>\n<p><strong>BBC: To amma akwai inda ya ke cewa \u201cNaramba\u0257a ba ya zuwa lahira&#8230;\u201d Kamar ya bugi \u0199irji\u2026<\/strong><\/p>\n<p>BUNZA: Ya ce ko ya je dawowa ya kai. Ya na da hujja a wannan wurin. Sai an kamo kan wa\u0199ar za a gane me ya sa ba zai je lahira ba! Ya ce:<\/p>\n<p><em>\u201cHwadawa ku bugan in buge ku<\/em><\/p>\n<p><em>Mui ta fa\u0257an mu gidan duniya,<\/em><\/p>\n<p><em>Kun san ba a hwa\u0257a lahira,<\/em><\/p>\n<p><em>Kun san ku ka zuwa lahira,<\/em><\/p>\n<p><em>Naramba\u0257a ba ya zuwa lahira,<\/em><\/p>\n<p><em>Ko ya je dawowa ya kai,<\/em><\/p>\n<p><em>Gama kun san \u0257auke mai akai.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Maganar sa ta tabbata: fadawa ke mutuwa; da bafade ya mutu, a fada an manta da shi. Da Sarki ya mutu, a fada an manta da shi, an yi wani. Amma idan zakaran mawa\u0199a ya mutu, ba mutuwa ya yi ba. Har yanzu ga Naramba\u0257a ba shi duniya, ana maganar sa, ana jin maganar sa. Ina fadawa su ke? Saboda haka duk wani mawa\u0199i da ya san kan sa, ya yi luguden wa\u0199ar, to bai mutu ba, ya na nan a raye!<\/p>\n<p><strong>BBC: To, Farfesa Aliyu Bunza, mun gode \u0199warai.<\/strong><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4738\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4738\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Duk wanda ya san abin da ake kira \u201cwa\u0199ar Hausa,\u201d to ya san Maka\u0257a Ibrahim Naramba\u0257a. Hasali ma dai akwai muhawara \u0199wa\u0199\u0199wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Naramba\u0257a da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Naramba\u0257a yawan wa\u0199o\u0199i ne kurum amma Naramba\u0257a ya fi zala\u0199a da fasaha, wasu [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4738\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4738\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[31,81,153,19,152],"class_list":["post-4738","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa","tag-adabin-hausa","tag-bbc-hausa","tag-farfesa-aliyu-bunza","tag-mamman-shata","tag-narambaa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":33,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba! - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba! - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Duk wanda ya san abin da ake kira \u201cwa\u0199ar Hausa,\u201d to ya san Maka\u0257a Ibrahim Naramba\u0257a. Hasali ma dai akwai muhawara \u0199wa\u0199\u0199wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Naramba\u0257a da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Naramba\u0257a yawan wa\u0199o\u0199i ne kurum amma Naramba\u0257a ya fi zala\u0199a da fasaha, wasu [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2007-08-29T13:27:05+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2023-09-06T13:40:24+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Ibrahim Sheme da Ashafa Murnai Barkiya\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"11 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738\"},\"author\":{\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/4e92e772a28744c9e6e919688380d5c7\"},\"headline\":\"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba!\",\"datePublished\":\"2007-08-29T13:27:05+00:00\",\"dateModified\":\"2023-09-06T13:40:24+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738\"},\"wordCount\":2184,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"keywords\":[\"adabin Hausa\",\"bbc hausa\",\"Farfesa Aliyu Bunza\",\"mamman shata\",\"Naramba\u0257a\"],\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738\",\"name\":\"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba! - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2007-08-29T13:27:05+00:00\",\"dateModified\":\"2023-09-06T13:40:24+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4738#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba!\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/4e92e772a28744c9e6e919688380d5c7\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/0fd33676471394693ab4e5b25a59894353a830807ed446204cad56b9a8854bb2?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/0fd33676471394693ab4e5b25a59894353a830807ed446204cad56b9a8854bb2?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/0fd33676471394693ab4e5b25a59894353a830807ed446204cad56b9a8854bb2?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba! - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba! - Ibrahim Sheme","og_description":"Duk wanda ya san abin da ake kira \u201cwa\u0199ar Hausa,\u201d to ya san Maka\u0257a Ibrahim Naramba\u0257a. Hasali ma dai akwai muhawara \u0199wa\u0199\u0199wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Naramba\u0257a da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Naramba\u0257a yawan wa\u0199o\u0199i ne kurum amma Naramba\u0257a ya fi zala\u0199a da fasaha, wasu [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2007-08-29T13:27:05+00:00","article_modified_time":"2023-09-06T13:40:24+00:00","author":"Ibrahim Sheme","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Ibrahim Sheme da Ashafa Murnai Barkiya","Estimated reading time":"11 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738"},"author":{"name":"Ibrahim Sheme","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/4e92e772a28744c9e6e919688380d5c7"},"headline":"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba!","datePublished":"2007-08-29T13:27:05+00:00","dateModified":"2023-09-06T13:40:24+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738"},"wordCount":2184,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"keywords":["adabin Hausa","bbc hausa","Farfesa Aliyu Bunza","mamman shata","Naramba\u0257a"],"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738","name":"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba! - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2007-08-29T13:27:05+00:00","dateModified":"2023-09-06T13:40:24+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4738#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Ashe Naramba\u0257a bai mutu ba!"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/4e92e772a28744c9e6e919688380d5c7","name":"Ibrahim Sheme","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/0fd33676471394693ab4e5b25a59894353a830807ed446204cad56b9a8854bb2?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/0fd33676471394693ab4e5b25a59894353a830807ed446204cad56b9a8854bb2?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/0fd33676471394693ab4e5b25a59894353a830807ed446204cad56b9a8854bb2?s=96&d=mm&r=g","caption":"Ibrahim Sheme"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4738","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4738"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4738\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4741,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4738\/revisions\/4741"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4738"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4738"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4738"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}