{"id":4393,"date":"2007-05-19T19:26:47","date_gmt":"2007-05-19T19:26:47","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4393"},"modified":"2007-05-19T19:26:47","modified_gmt":"2007-05-19T19:26:47","slug":"bikin-kona-littattafai-amsar-abdalla","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393","title":{"rendered":"Bikin kona littattafai &#8211; Amsar Abdalla"},"content":{"rendered":"<p>Professor Abdalla Uba Adamu<\/p>\n<p>Sashen Horon Malaman Kimiyya da Fasaha<\/p>\n<p>Jami\u2019ar Bayero, Kano<\/p>\n<p>Hira da Maje el-Hajeej na Hausa Leadership wacce za ta fito a wannan satin (19 Mayu 2007).<\/p>\n<p><strong>1. Shin a matsayin ka na Furofesa ko bikin kona littafan Hausa da gwamnati ta yi ya dace?<\/strong><br \/>\n<strong><br \/>\n<\/strong>Ba a matsayina na furofesa zan yi magana ba \u2013 domin za ka samu furofesoshi da dama wadanda wanna abin ya zauna mu su daidai. Zan yi magana ne a matsayina na almajiri mai neman ilimi. Gaskiya a nawa ra\u2019ayin wannan bai dace ba, domin babu cikakken bayani game da laifin da littattafan da a ka kona a ka ce sun yi. Da zai yi kyau, kafin a kona, a yi wani sharhi a kan kowanne littafi domin nuni ga ire-iren abubuwan da hukuma ta haramta kuma wadanda suka fito a cikin wadannan littattafan. Ta haka za a tabbatar da cewa sun aikata wani laifi. Yin haka shi ne adalci.<\/p>\n<p>Amma ko da sun aikata laifi, konawar ba shi ne mafita ba \u2013 domin konawar zai jawowa gwamnati wata matsala inda za a funskance ta a kan maras son ci gaban al\u2019uma. Sannan kuma za a iya kwatanta wanna da ire-iren abubuwan da gwamnatin Taliban ta yi a Maris 2001 na dandake gumakan Buddha, wadanda sun fi shekaru dubu a kasar, har ma duniya ta dauke su a matsayin jarin al\u2019adun al\u2019ummatn duniya. Manazarta sun yi kuka da lamarin da nuni da cewa duk da wadannan gumakan na kafirci ne, wanda kuma ya sabawa gwamnatin Taliban ta wancan lokacin, amma adanasu na da humimmanci wajen tattara tarihin dan Adam da nuni da yadda rayuwarsa ta gabata, wannan ma kadai zai hana a sake yunkurin bauta musu domin da ganinsu ka ga sakakkun abubuwa wadanda ba su cancanti a bauta musu ba.<\/p>\n<p>Amma duk da cewa ban goyi bayan konawar littattafan kagaggun da aka yi ba, dole mu yi la\u2019akari da cewa gwamnati na da hakkin kula da rayuwar jama\u2019a ta yadda ya dace da jama\u2019ar. Saboda haka in bera na da sata, daddawa na da wari.<\/p>\n<p><strong>2. A matsayin ka manazarci ko irin wannan bikin kona littattafai ya na faruwa a wasu sassan duniya?<\/strong><\/p>\n<p>Bikin kona littattafai ba abu ne sabo a duniya ba. Tarihi ya nuna cewa hukumomi da dama a lokuta dabam-dabam sun shugabanci bikin kona littattafai saboda dalilai guda uku. Na farko tunanin cewa abin da aka rubuta ya sabawa akidar al\u2019ummar da aka rubuta a cikinta. Na biyu sabawa addinin da hukuma ta yarda da shi \u2013 ko da marubucin ba ya cikin addinin hukumar. Na uku siyasa tana sa hukuma ta jagoranci kona littattafai domin ganin an karya alkadarin \u2018yan adawa da gwamnatin da ke kan gado.<\/p>\n<p>Abin da ya sa ake kare fasihai (marubuta, mawaka, da kuma masu zane ko fim) daga bikin kona ayyukan fasaha shi ne wata rana ba rubutun za a kona ba \u2013 fasihan za a kona. An taba yin haka a China a karkashin masarautar Qin (shekaru 212 kafin bayyanar Annabi Isa (AS) wacce Qin Shi Huang ke shugabanta, inda shugaban lokacin ya ga kona littattafan bai isa ba, sai ya hada da kona masu rubutun littattafan; har ma da masu karatun \u2013 duk sai da ya sa a ka kona su, kimanin mutane 450.<\/p>\n<p>Haka ma sojojin Rumawa suka bi wannan salon kona littattafan da ke Laburaren Alexandari a jihar Alexandria da ke Masar (Egypt) shekaru 300 kafin bayyanar Annabi Isa (AS). A wannan lokacin a duk fadin duniya babu wata laburaren da ta fi wannan girma, yawan littattafai da kuma manazarta. Kar fa a manta duk tarin littattaan da hannu aka rubuta su, domin lokacin babu injin buga littafi.<\/p>\n<p>Da Hitilar ya zama shugaban Jamus kuma ya kafa akidar Nazism, shi ma ya shugabanci kona littattan da Yahudawa suka rubuta, a rukunayen shekarun 1930 da 1940. Misali, ranar 10 ga Mayu 1933 kusan littattafai 20,000 a ka saka daliban suka kona a Berlin.<\/p>\n<p>Babu inda ba a kona littattafai ba \u2013 daga kasar Amurka, inda ake ganin sun fi kowa walawa, zuwa kasashen da dama ana ganin kamar a takure su ke. A Ingila a shekar 1525 an kona littafin Injila wanda William Tyndale ya rubuta. Sannan a 1633 an kona Histiro-Mastix, littafin Willian Prynne wanda ya kalubalanci sarauniyar Ingila. Shi kansa marubucin, an kama shi, a ka yi masa dukan tsiya, aka yanke kunnuwansa, sannan a ka kulle shi a gidan yari. A Amurka a 1650 an kona littafin Willianm Pynchon, mai suna The Meritorious Price of Our Redemption saboda ana ganin ya yi sabo. Jaridar farko a Amurka, Public Occurences, haramta fitowarta a ka yi a 1650.<\/p>\n<p>Kada kuma a dauka wai jahiliyyar ilimi ce ta kawo wannan. A dai Amurka din, a jihar New Mexico, a 2001 an kona kagaggun labaran Harry Potter, labarin wani yaro mai yin shihiri.<\/p>\n<p>A Masar, a Janairu na 1991 hukumar kasar ta jagoranci kona duk littattafan Abu-Nuwas al-Hasan ben Hani al-Hakami ( wanda ya rayu daga\u00a0<a title=\"750 in\npoetry\" href=\"http:\/\/en.wikipedia.org\/wiki\/750_in_poetry\">750<\/a>\u00a0zuwa 810 miladiyya), wadanda ake ganin kamar sun shafi batsar luwadi da kuma sharholiyar shan giya.<\/p>\n<p>Saboda haka akwai misalai ratata inda a ka kona littattafai saboda rashin yarda da marubuci \u2013 daga kasashen da ake ganin sun ci gaba, zuwa kasashen da ke tasowa. Ba abu ne sabo ba; ba kuma abu ne da za a ce wai gwamnatin Shari\u2019a ce ta kawo shi ba \u2013 da ma yana can.<\/p>\n<p><strong>3. Shin a irin karatun wadannan littattafai da ka ke yi, ko kana ganin sun cancanci gwamnatin ta kona su?<br \/>\n<\/strong><br \/>\nKamar yadda na ce, ba mu san sunayen littattafan da a ka kona ba, da kuma hujjar da a kabi domin tantance wadanda za a kona. Tabbas a kwai littattafan da suke dauke da abubuwan batsa marassa kyau. Wadannan sun hada da, misali, Shu\u2019uma (Maje el-Hajeej), Maza Sai Sannu (Binta A. Wali), Guguwar So (Mukhtar Isa Adamu), Halacci (Sadiya Baba Yusuf), Maza Sai Sannu (Binta A. Wali), Mugun aboki (Dan Barno), Shan Koko (Jamila Abdulkadir) da sauransu. Kona su ba shi zai sa a daina irin wannan rubutun ba, domin konawar ba ta shiga zuciyar mutane ta inda za a fahimci dalilin konarwar saboda dalilai uku.<\/p>\n<p>Na farko dai wanda ya sayi littafin shi ya yi asara \u2013 ba marubuci ba, ba kuma dan kasuwa mai sayar da littafin ba. In da gaske a ke so a yi, da sai a je wajen dillalan littattafan a kasuwa, domin su ne suke bugawa, a tattara a kona a can. Amma ka ga ai ba haka a ka yi ba \u2013 makaranta aka je, aka sami dalibai wadanda suka sayi littattafan da kudinsu, ba da kudin hukuma ba, aka ce su fito a kona su. Ba ayi komai ba a nan, domin dama sun gama karanta littattafan \u2013 watakila ma sun rasa yadda za su yi da su; wadansu ma ba dole ne a ce littattafan da ake bukata a kona suka fito da su ba, sa iya fitar da littafin karatun da ba sa so (misali, Lissafi), su kawo a kona. A nan waye ya yi asara? Kuma wacce nasara a ka ci?<\/p>\n<p>Na biyu, in da so a ke a yi konar ta yadda za a isar da sako, da sai a tattara marubuta waje daya \u2013 misali laburaren Murtala Muhammad \u2013 sannan a ce kowa ya kawo littafin da ya rubuta, sannan a tara a banka musu wuta. Idan an yi haka, sai a ga mai zai faru? To amma ba a bi wadannan hanyoyin ba.<\/p>\n<p>Na uku, dole a tambayi marubuta ire-iren wadannan littattafan \u2013 menene manufar rubuta su? Kada a manta, kamar yadda wani marubuci ya taba fada, \u2018yancin ka na ka yi kutufo da hannunka a iska ya tsaya daidai inda hanci na ya fara. Saboda haka idan marubuci na da \u2018yancin rubuta abin da ya ga dama, dole ya nauyaya da sakamakon abin ya rubuta da kuma abin da zai haifar.<\/p>\n<p><strong>4. Kowacce hanya ce mafi dacewa da gwamnati ya kamata ta yi amfani da ita, domin daidaita sahun marubuta?<\/strong><\/p>\n<p>Nunawa su kansu marubutan muhimmancin jagorancin jama\u2019a wajen rubutu. Idan marubuci zai dauki cewa yana da \u2018yancin ya yi duk irin rubutun da ya ga dama, to dole ya auna sakamakon rubutun da zai yi. Yi wa fasihi takunkumi ko katanga ba shi ne mafita ba \u2013 domin da takunkumin da katangar duk ba sa aiki. Hasali ma dai dada lalata lamarin su ke yi, domin da zarar an ce an haramta wani abu, to tabbas za ka ga dangin shaidan na rububin abin. Kungiyar Marubuta ta Kasa, reshen Kano, ANA ta taba haramta wani littafi wai shi [ufana kusan shekaru shida da suka wuce. Kafin ka ce kwabo, kudin littafin ya tashi daga naira talatin zuwa naira dari, kuma aka dinga tururuwa neman sa. Dan-da-nan ya bace a kasuwa saboda rububi. To haka ma wadannan littafan da aka kona. Tabbas da mutane sun san sunayensu, to da marubutan sun zama miliniyoyi saboda rububin littattafan za a dinga yi. Abin la\u2019akari a nan shi ne, inda duniya na raye, to [an Adam na tare da Iblis. In kuwa haka ne, to ire-iren wadannan abubuwa za ci gaba da addabar jama\u2019ar har busa kaho.<\/p>\n<p>Saboda haka dole marubuta su yi la\u2019akari da hakkin jama\u2019a a kansu \u2013 wannan shi ne katangar da su za su iya yi da kansu, amma ba katangar hukuma ba. Sanin hanyar da za a yi wannan shi ne yadda hukumar A Daidaita Sahu za ta bi domin maganta lamarin. Af, ji nake ita dai wannan hukumar mai kona littattafai, ita ce ta gayyaci marubutan a 2005, ta ba su kwangilar rubutu irin wanda hukumar ke so? Sai yanzu ne kuma za su ce wadannan mutanen lalatattu ne? Ashe ka ga da sake kenan.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4393\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4393\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Professor Abdalla Uba Adamu Sashen Horon Malaman Kimiyya da Fasaha Jami\u2019ar Bayero, Kano Hira da Maje el-Hajeej na Hausa Leadership wacce za ta fito a wannan satin (19 Mayu 2007). 1. Shin a matsayin ka na Furofesa ko bikin kona littafan Hausa da gwamnati ta yi ya dace? Ba a matsayina na furofesa zan yi [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4393\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4393\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4393","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":28,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Professor Abdalla Uba Adamu Sashen Horon Malaman Kimiyya da Fasaha Jami\u2019ar Bayero, Kano Hira da Maje el-Hajeej na Hausa Leadership wacce za ta fito a wannan satin (19 Mayu 2007). 1. Shin a matsayin ka na Furofesa ko bikin kona littafan Hausa da gwamnati ta yi ya dace? Ba a matsayina na furofesa zan yi [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2007-05-19T19:26:47+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Bikin kona littattafai &#8211; Amsar Abdalla\",\"datePublished\":\"2007-05-19T19:26:47+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393\"},\"wordCount\":1601,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393\",\"name\":\"Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2007-05-19T19:26:47+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4393#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Bikin kona littattafai &#8211; Amsar Abdalla\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla - Ibrahim Sheme","og_description":"Professor Abdalla Uba Adamu Sashen Horon Malaman Kimiyya da Fasaha Jami\u2019ar Bayero, Kano Hira da Maje el-Hajeej na Hausa Leadership wacce za ta fito a wannan satin (19 Mayu 2007). 1. Shin a matsayin ka na Furofesa ko bikin kona littafan Hausa da gwamnati ta yi ya dace? Ba a matsayina na furofesa zan yi [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2007-05-19T19:26:47+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Bikin kona littattafai &#8211; Amsar Abdalla","datePublished":"2007-05-19T19:26:47+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393"},"wordCount":1601,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393","name":"Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2007-05-19T19:26:47+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4393#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Bikin kona littattafai &#8211; Amsar Abdalla"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4393","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4393"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4393\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4393"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4393"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4393"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}