{"id":4373,"date":"2007-07-24T15:41:41","date_gmt":"2007-07-24T15:41:41","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4373"},"modified":"2007-07-24T15:41:41","modified_gmt":"2007-07-24T15:41:41","slug":"agajin-harkar-rubutu-ya-kamata-gwamnati-ta-shigo-ciki-%c6%99amaruddeen-imam","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373","title":{"rendered":"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam"},"content":{"rendered":"<p><em>\u0198amaruddeen Imam ya na daga cikin \u2019ya\u2019yan kakan marubutan Hausa, wato marigayi Alhaji Dakta Abubakar Imam, marubucin littattafai kamar su \u2018Ruwan Bagaja, &#8216;Magana Jari Ce,\u2019 &#8216;Tafiya Mabu\u0257in Ilmi,\u2019 Tarihin Annabi Da Na Halifofi&#8217;, &#8216;Tambaya Goma Amsa Goma&#8217;, da sauran su. Shi ma Alhaji \u0198amaruddeen marubuci ne, kuma mawallafi, kuma shi ka\u0257ai ne daga cikin \u2019ya\u2019yan Imam da ya gaji mahaifin sa a fannin adabi.<\/em><\/p>\n<p><em>Kamar Baba Imam, shi ma Alhaji \u0198amaruddeen ya kwanta dama. Ya rasu a ranar Juma\u2019a, 12 ga Mayu 2006 a gidan Imam da ke Tudun Wada, Zariya, a Jihar Kaduna, bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon shekara biyar. Shekarun sa 56 a duniya.<\/em><\/p>\n<p><em>Ya rasu ya bar mahaifiyar sa da matar sa da \u2019ya\u2019ya shida da kuma jikanyar sa. Allah ya ji\u0199an sa, amin summa amin.<\/em><\/p>\n<p><em>Abin ikon Allah, na samu damar yin hira da \u0198amaruddeen a Zariya tun ya na da rai, wato a ranar 29 ga Agusta 2004. Mun tattauna a kaset lokacin da na halarci wani taro da iyalan Imam su ka kira don \u0199addamar da kwamitin Gidauniyar Tunawa da Alhaji Abubakar Imam (Abubakar Imam Foundation) tare da gina gidan yana a intanet. Ni memba ne a kwamitin. Mun yi tarurruka da dama don \u0257abbaka wannan muhimmin nufi, wanda a \u0199arshe an kafa cibiyar tattara bayanai kan Imam a wani gini da ke duban \u0198ofar Babban Dodo a birnin Zariya, sa\u2019annan an gina gidan yanar (www.abubakarimam.com).<\/em><\/p>\n<p><em>Malam \u0198amaruddeen mutumin kirki ne, mai sau\u0199in kai, mai sanyin murya, mai fara\u2019a \u2013 kamar dai dukkan \u2019ya\u2019yan Imam da na gani. Lokacin da na bu\u0199ace shi da mu tattauna, nan da nan ya amince, mu ka zauna mu ka tattauna kan sha\u2019awar sa ta rubuce-rubuce, da matsalolin sha\u2019anin wallafa a Nijeriya da kuma halin da ake ciki.<\/em><\/p>\n<p><em>Na so in wallafa hirar a jaridar Leadership lokacin ina editan ta, amma sai abubuwa su ka rinca\u0253e; haka lokacin da na ke babban editan jaridar Public Agenda, na so buga hirar, amma nan ma abubuwa su ka giggitta. Sai a yanzu ne Allah ya ba ni damar wallafa wannan tattaunawar da marubucin.<\/em><\/p>\n<p><em>Wannan hira ta na da muhimmanci, domin kuwa ita ce ta farko da Malam \u0198amaruddeen ya yi da wani \u0257an jarida a kan rubuce-rubucen sa, kuma ita ce ta \u0199arshe. Allahu Akbar!<\/em><\/p>\n<p><em>Bismillan ku:<\/em><\/p>\n<p><strong>SHEME: Zan so ka fa\u0257i sunan ka da kuma dangantakar da ke tsakanin ka da marigayi Alhaji Abubakar Imam.<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: To ni suna na \u0198amaruddeen Abubakar Imam, kuma ni \u0257an Alhaji Abubakar Imam ne.<\/p>\n<p><strong>SHEME: Yanzu aikin me ka ke yi?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Yanzu ni marubuci ne kuma ina buga littattafai, kuma ana ba ni gyaran rubutu kamar na \u2018manuscript\u2019.<\/p>\n<p><strong>SHEME: To ko za ka gaya mana yawan littattafan da ka rubuta da kuma sunan su?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Na rubuta littattafai da dama. Akwai &#8216;Tsaka Mai Wuya&#8217;, &#8216;Hannun Ka Mai Sanda&#8217;, sannan kuma na rubuta &#8216;Halaye Nagari a Cikin Musulunci&#8217;, &#8216;Sir Usman Nagogo&#8217; \u2013 amma da Turanci ne ni da (\u018aahiru) Coommassie mu ka rubuta shi \u2013 da kuma &#8216;To Use Knowledge&#8217;.<\/p>\n<p><strong>SHEME: Kamar daga wane lokaci ne ka fara rubuce-rubucen nan?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Na fara wannan rubuce-rubuce tun lokacin da marigayi Baba Imam ya ke da rai, har ma ya sa ni a kan wasu hanyoyi inda ya ke ce mani, &#8216;In za ka rubuta tarihin mutum, to rubuta abin kirkin da ya yi na alheri ga jama\u2019a, maimakon ka yi yabon shi.\u201d<\/p>\n<p><strong>SHEME: Yanzu kenan kai ka\u0257ai ne cikin \u2019ya\u2019yan marigayi ka gaji baban ka ta wajen rubuce-rubuce?<\/strong><\/p>\n<p>KAMARUDDEEN: I to, haka ne, don har yanzu ni ka\u0257ai ke yin irin wa\u0257annan ayyuka na rubuce-rubuce.<\/p>\n<p><strong>SHEME: A da, ka \u0257an rubuta littattafai na \u0199ir\u0199ira, amma kuma daga baya sai ka bari. Ko me ya kawo haka?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: To dalilin dai shi ne saboda rashin ku\u0257i, kuma in ka rubuta ka kai ma wasu su taimake ka sai su ce ba su da ku\u0257i, ko kuma su ce kai ka kawo rabi, in ka kawo ma in ba a yi sa\u2019a ba sai ka ga ku\u0257in ka ma ya ma\u0199ale.<\/p>\n<p><strong>SHEME: To ban da matsalar rashin ku\u0257i, ko za ka iya fa\u0257in wata matsala da ke iya shafar aikin wallafa, musamman a nan Arewa?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Akwai matsaloli mana. Misali irin yadda mutane ke rubuta littattafai barkatai ba tare da an tsara shi yadda ya kamata ba, musamman masu soyayya. Ba wanda bai iya soyayya ba, to amma ya kamata in za ka rubuta ka tabbatar da ka rubuta abin da yake mai kyau kuma mai inganci.<\/p>\n<p><strong>SHEME: Menene maganin abin?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Maganin abin shi ne gwamnati ta shigo ciki, ta zo ta ri\u0199a sayen littattafan. Ya kamata kuma a ri\u0199a sayar ma makarantun sakandare. Ta haka za a samu tarbiyya a makarantu, ba wai mutum ya je ya kalli fim ya zo ya maida shi littafi ba, ko kuma irin yadda ake cusa ma matasa ra\u2019ayin soyayya ba; misali, duk wanda ya karanta &#8216;Magana Jari Ce&#8217; ya san lallai wannan Bahaushe ne ke magana, kuma ba batsa, sannan ga tarbiyya a ciki.<\/p>\n<p><strong>SHEME: To Alhaji, ga shi Allah ya ha\u0257a mu a nan Zariya don tunawa da shi marigayi da \u0199addamar da kwamitin tunawa da shi. Ko za ka gaya mana abin da ya sa ku ke son a kafa wannan kwamiti?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: To, akwai wani \u0257an jarida wanda ake kira Ibrahim Sheme, ya na yawan rubutu a kan Dakta Abubakar Imam. A gaskiya ya nuna mana \u0199auna, ya nuna ya na son marigayi Dakta Abubakar Imam. To kwanan nan sai ya yi wani rubutu wanda ya zama mana kamar tuni ko \u0199alubale, don kuwa har wani shagu\u0253e ya yi mana inda ya nuna mana cewa \u2019ya\u2019yan marigayin kamar ma sun manta da shi. To jin haka sai mu ma mu ka harzu\u0199a mu ka fara shirin kafa wannan kwamiti don tunawa da marigayi Dakta Alhaji Abubakar Imam.<\/p>\n<p><strong>SHEME (dariya): Ya ka ke ganin wannan abin zai amfani mutane a nan gaba?<\/strong><\/p>\n<p>KAMARUDDEEN: In aka kafa wannan Foundation, to kowa da kowa zai zo ya zauna ya duba duk abin da ya ke bu\u0199ata na Dakta Alhaji Abubakar Imam, kuma wannan ya ha\u0257a kowa da kowa. Misali, akwai wata mata, mutuniyar Jamus ce, ta ke bincike a kan Dakta Abubakar Imam, yanzu haka har ma ta yi nisa ta kai wata matsaya babba. Ka ga yanzu in ta zo sai kawai mu nuna mata wannan wurin don kuwa da man an ta\u0253a yi mata bayanin ana wannan aiki.<\/p>\n<p><strong>SHEME: To a \u0199arshe, ko za ka iya ba ni \u0257an tarihin rayuwar ka?<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: To ni shekaru na 54 da haihuwa, kuma a nan Zariya aka haife ni. Bayan na gama karance-karance na na sakandire da jami\u2019a, na yi aiki da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, lokacin Edita Baban Zarah.<\/p>\n<p><strong>SHEME: Ai ina zaton kai a Katsina ka ke.<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Asali na shi ne Katsina, kuma mu na da yawa, misali su Shamsuddeeni Imam, Nuruddeen Imam, su su ke can Katsina; amma mu da aka haifa a nan Zariya \u2013 Najmuddeen Imam, \u0198amaruddeen Imam, Amadi Imam, Jalaladdeen Imam \u2013 nan Zariya mu ke.<\/p>\n<p><strong>SHEME: To Alhaji, na gode.<\/strong><\/p>\n<p>\u0198AMARUDDEEN: Ni ma na gode. Allah ya saka maka da alheri, amin.<\/p>\n<p><em>(BAYANI: Hoton \u0198AMARUDDEEN da ke wannan shafin ya da\u0257e da \u0257auka, wata\u0199ila sama da shekara 20 kafin rasuwar marigayin, domin ya zama dattijo lokacin rasuwar sa. Allah ya rahamshe shi, amin.)<\/em><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4373\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4373\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198amaruddeen Imam ya na daga cikin \u2019ya\u2019yan kakan marubutan Hausa, wato marigayi Alhaji Dakta Abubakar Imam, marubucin littattafai kamar su \u2018Ruwan Bagaja, &#8216;Magana Jari Ce,\u2019 &#8216;Tafiya Mabu\u0257in Ilmi,\u2019 Tarihin Annabi Da Na Halifofi&#8217;, &#8216;Tambaya Goma Amsa Goma&#8217;, da sauran su. Shi ma Alhaji \u0198amaruddeen marubuci ne, kuma mawallafi, kuma shi ka\u0257ai ne daga cikin \u2019ya\u2019yan [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4373\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4373\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4372,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4373","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":12,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"\u0198amaruddeen Imam ya na daga cikin \u2019ya\u2019yan kakan marubutan Hausa, wato marigayi Alhaji Dakta Abubakar Imam, marubucin littattafai kamar su \u2018Ruwan Bagaja, &#8216;Magana Jari Ce,\u2019 &#8216;Tafiya Mabu\u0257in Ilmi,\u2019 Tarihin Annabi Da Na Halifofi&#8217;, &#8216;Tambaya Goma Amsa Goma&#8217;, da sauran su. Shi ma Alhaji \u0198amaruddeen marubuci ne, kuma mawallafi, kuma shi ka\u0257ai ne daga cikin \u2019ya\u2019yan [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2007-07-24T15:41:41+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg?fit=356%2C498&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"356\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"498\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam\",\"datePublished\":\"2007-07-24T15:41:41+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373\"},\"wordCount\":1262,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/Kamaruddeen-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373\",\"name\":\"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/Kamaruddeen-1.jpg\",\"datePublished\":\"2007-07-24T15:41:41+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/Kamaruddeen-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/Kamaruddeen-1.jpg\",\"width\":356,\"height\":498,\"caption\":\"Marigayi \u0198amaruddeen Imam\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4373#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam - Ibrahim Sheme","og_description":"\u0198amaruddeen Imam ya na daga cikin \u2019ya\u2019yan kakan marubutan Hausa, wato marigayi Alhaji Dakta Abubakar Imam, marubucin littattafai kamar su \u2018Ruwan Bagaja, &#8216;Magana Jari Ce,\u2019 &#8216;Tafiya Mabu\u0257in Ilmi,\u2019 Tarihin Annabi Da Na Halifofi&#8217;, &#8216;Tambaya Goma Amsa Goma&#8217;, da sauran su. Shi ma Alhaji \u0198amaruddeen marubuci ne, kuma mawallafi, kuma shi ka\u0257ai ne daga cikin \u2019ya\u2019yan [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2007-07-24T15:41:41+00:00","og_image":[{"width":356,"height":498,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg?fit=356%2C498&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam","datePublished":"2007-07-24T15:41:41+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373"},"wordCount":1262,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373","name":"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg","datePublished":"2007-07-24T15:41:41+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg","width":356,"height":498,"caption":"Marigayi \u0198amaruddeen Imam"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4373#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki \u2013 \u0198amaruddeen Imam"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Kamaruddeen-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4373","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4373"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4373\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4372"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4373"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4373"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4373"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}