{"id":4368,"date":"2007-07-24T05:35:42","date_gmt":"2007-07-24T05:35:42","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4368"},"modified":"2007-07-24T05:35:42","modified_gmt":"2007-07-24T05:35:42","slug":"gasar-n300000-ga-marubutan-hausa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368","title":{"rendered":"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA"},"content":{"rendered":"<p>AN dad&#8217;e ba a samu tagomashi a fagen rubutun Hausa ba, musamman na k&#8217;irk&#8217;ira. An bar marubuta kowa tasa ta fisshe shi. Hakan yana tattare da matsaloli da dama, ta yadda littattafan mu sun kasance cikin k&#8217;ask&#8217;anci, babu inganci, kuma babu k&#8217;ok&#8217;arin kawo sabon abu. Idan ba a yi wankiyar finafinan Indiya da na Turawa da na \u2019yan Kudu ba, to kuwa za a d&#8217;auki littattafan su a fassara, a sata, a ce na Hausa ne.<\/p>\n<p>To, da alama zamanin ci-gaba ya fara kunno kai a fagen rubutu. Wata mata da ke zaune a Abuja, kuma babbar ma\u2019aikaciyar gwamnatin tarayya, ta d&#8217;auki nauyin shirya gasar rubuta littattafan Hausa daga bana, kuma za ta ba da zunzurutun kud&#8217;i har naira dubu d&#8217;ari uku (N300,000) ga zakarun gasar a kowace shekara.<\/p>\n<p>Wannan mata dai sunan ta Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, kuma ita ce Babbar Sakatare ta Hukumar Kula da Aikin Shari\u2019a ta Tarayya (Executive Secretary, National Judicial Service Commission). Ta d&#8217;auki nauyin gasar, abin da a Turance ake kira endowment, a dalilin son tunawa da mijin ta, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ran 18 ga Oktoba, 2006. Mijin nata dai shi ne Injiniya Bashir K&#8217;araye, wanda ya tab&#8217;a zama Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano, sa\u2019annan ya tab&#8217;a zama Kwamishinan Yad&#8217;a Labarai, Matasa da Al\u2019adu da Wasanni na jihar. Can a baya kuma ya tab&#8217;a zama shugaban Hukumar Muhalli ta Jihar Kano.<\/p>\n<p>Rasuwar Injiniya Bashir ta girgiza iyalan sa da masoyan sa matuk&#8217;a, musamman da yake ta zo ne ba zato ba tsammani; cikin awoyi kad&#8217;an ya kwanta ciwo, kafin ka ce kwabo ya ce ga garin ku. Shekarun sa 56 a duniya.<\/p>\n<p>A ranar Talatar nan da ta wuce, Hajiya Bilkisu ta fad&#8217;a wa membobin K&#8217;ungiyar Marubuta ta Nijeriya (Association of Nigerian Authors, ANA), reshen Babban Birnin Tarayya, da manema labarai, a ofishin ta a Abuja cewa marigayin mutum ne mai k&#8217;aunar harkar adabi da inganta harshen Hausa matuk&#8217;a. Don haka abin alfahari ne da farin ciki a gare ta a ce ta karrama shi ta hanyar saka gasar rubuce-rubucen Hausa da sunan sa.<\/p>\n<p>Sunan wannan gasa dai Engineer Bashir K&#8217;araye Memorial Prize in Hausa Literature.<\/p>\n<p>K&#8217;ungiyar ANA reshen Abuja, a k&#8217;ark&#8217;ashin jagorancin shugaban ta, Dakta Emman Usman Shehu, ita ce ta rubuta wa Hajiya Bilkisu takarda, ta buk&#8217;ace ta da ta d&#8217;auki nauyin gasar bayan sun fahimci cewa a shirye take da ta karrama marigayi ta kowace kyakkyawar hanya. Wani ma\u2019aikacin hukumar, Inyamiri, mai suna Mista Patrick Oguejiofor, wanda shi ma marubuci ne, shi ne ya yi wa \u2019yan k&#8217;ungiyar hanya ya sada su da Hajiya har wannan al\u2019amari ya tabbata.<\/p>\n<p>A ranar Talatar makon jiya, an taru ne a ofishin Babbar Sakataren domin a k&#8217;addamar da fara wannan gasa. \u2019Ya\u2019yan ANA a wurin sun had&#8217;a da shi Dakta Shehu da sakataren k&#8217;ungiya Mista Kanico da lauya Ahmed Maiwada da Mista Oguojifor da kuma Ibrahim Sheme, wanda ya tab&#8217;a zama sakataren yad&#8217;a labarai na k&#8217;asa na k&#8217;ungiyar ANA.<\/p>\n<p>Ba wani shagali aka yi ba. An dai yi bayanai da kuma mik&#8217;a takardun da ke nuna cewa Hajiya ta d&#8217;auki nauyin wannan gasa.<\/p>\n<p>Hajiya Bilkisu ta ce Mista Oguojifor ne ya ba ta k&#8217;warin gwiwa ta d&#8217;auki nauyin shirya gasar. Ta ce duk da yake ita ba marubuciya ba ce kuma ba ta samu isassshen lokacin karanta littattafai a yanzu, a shirye take ta yi dukkan abin da ya dace don tunowa da Injiniya Bashir. Ta ce, \u201cNa kuma samu k&#8217;arin farin ciki da na ji cewa ba ku da wani wanda ya d&#8217;auki nauyin shirya gasa don hab&#8217;aka adabin Hausa. Sai na ga wannan babbar dama ce a gare ni in taimaka a hab&#8217;aka Hausa, wato harshen da shi (Injiniya Bashir) yake matuk&#8217;ar so.\u201d<\/p>\n<p>Ta k&#8217;ara da cewa Hausa harshe ne mai albarka. \u201cNa yi mamaki da na ji cewa wai babu wani wanda ya d&#8217;auki nauyin hab&#8217;aka shi ta irin wannan hanyar. To, na yi murna da cewa ina daga cikin wad&#8217;anda za su taimaka wajen d&#8217;aukar nauyi irin wannan.\u201d<\/p>\n<p>A wajen amsa tambayoyin da \u2019yan jarida suka yi mata, Hajiya Bilkisu ta bayyana cewa ita kan ta dai ba Bahaushiya ba ce (an ce \u2019yar Jihar Kogi ce), to amma tana da kishin Hausa matuk&#8217;a, kuma mijin ta ya sha ba ta k&#8217;warin gwiwa wajen fahimtar harshen. Ta ce, \u201cDuk da yake ni ba k&#8217;wararriya ba ce wajen magana da Hausa, amma dai na iya Hausa sosai.\u201d<\/p>\n<p>Cikin alhini, har ta kusa fashewa da kuka, Hajiya Bilkisu ta k&#8217;ara da cewa Injiniya Bashir mutum ne mai son karanta Hausa, kuma ya kan ba iyalan sa \u2013 daga matan sa har \u2019ya\u2019yan sa \u2013 k&#8217;warin gwiwar su rik&#8217;a amfani da harshen. \u201cNa tabbatar kowa da kowa (a gidan) zai ji dad&#8217;in cewa za a iya yin wani abu wanda marigayi ke so ko da bayan ran sa,\u201d inji ta. \u201cShi ba marubuci ba ne, amma yana son inganta harkar rubutu. Duk wad&#8217;annan abubuwan su ne suka ba ni tunanin cewa lallai ya kamata in yi wannan abu.\u201d<\/p>\n<p>A yanzu dai ba a bayar da sanarwar fara gasar ba. To amma shugaban ANA na Abuja, Dakta Shehu, ya d&#8217;an nuna yadda gasar za ta kasance. Na farko dai k&#8217;ungiyar za ta zauna ta fito da k&#8217;a\u2019idojin gasar, sannan za ta nad&#8217;a alk&#8217;alan gasar; za a bayar da sanarwa a kafafen yad&#8217;a labarai ana kira ga marubuta da su shiga gasar. Ya ce za a shigar da littattafan hikaya wad&#8217;anda aka buga su daga shekaru biyar da suka gabata zuwa yanzu a gasar. A cikin littattafan, za a zab&#8217;i guda uku a matsayin zakaru, za a shirya k&#8217;warya-k&#8217;waryar walima a Abuja wajen watan Nuwamba mai zuwa inda za a mik&#8217;a wa zakaru kyautar da suka ci ta wad&#8217;annan kud&#8217;i da za a karkasa masu.<\/p>\n<p>\u201cA bana, za mu fara ne da littattafan hikaya,\u201d inji Dakta Shehu, \u201csannan a bad&#8217;i za mu saka gasar rubutattun wak&#8217;ok&#8217;i, sannan a shekara ta gaba kuma za mu yi gasar wasan kwaikwayo.\u201d<\/p>\n<p>\u201cMuna kuma fatan fito da wasu abubuwan da za su k&#8217;awata gasar,\u201d inji shi.<\/p>\n<p>Wakilin mu ya fahimci cewa idan Hajiya Bilkisu ta ba da mak&#8217;udan kud&#8217;in shirya gasar, za a saka su a wani asusu na musamman a banki, inda a duk shekara za a ciri _300, 000 na zakaru, kuma akwai yiwuwar cewa kud&#8217;in za su k&#8217;aru a nan gaba.<\/p>\n<p>Marubuta sun yi farin ciki da wannan abu da ya faru. Dakta Emman Shehu ya bayyana cewa wannan ba k&#8217;aramin k&#8217;ok&#8217;ari ba ne Hajiya Bilkisu ta yi.<\/p>\n<p>Shi ma tsohon shugaban k&#8217;ungiyar ANA reshen Jihar Kano, wanda kuma fitaccen marubuci ne kuma malami a Jami\u2019ar Bayero ta Kano, wato Dakta Yusuf Muhammad Adamu, ya yaba da k&#8217;ok&#8217;arin da Hajiya Bilkisu ta yi. A hirar da ya yi da Leadership Hausa shekaranjiya, malamin ya ce an jima ba a samu irin wannan lagwada ba a fagen rubutu \u201cduk da k&#8217;ok&#8217;arin da muka sha yi na neman wanda zai d&#8217;auki nauyin irin wannan gasa.\u201d<\/p>\n<p>Ya yaba wa k&#8217;ungiyar ANA ta Abuja saboda hob&#8217;b&#8217;asan da suka yi na samun wannan taimako ga marubuta. Ya yi nuni da cewa shirya gasar zai ba da gagarumar gudunmawa ga k&#8217;ok&#8217;arin da ake yi na inganta rubutun Hausa.<\/p>\n<p>Dakta Yusuf Adamu ya kuma ba da shawarar cewa ya kamata a d&#8217;auki alk&#8217;alan da suka dace don yin hukunci a gasar, ya ce \u201ckada a d&#8217;auki wad&#8217;anda suke da wani ra\u2019ayi na son rai.\u201d Ya kawo misali da malamai a jami\u2019o\u2019in Bayero, A.B.U. Zariya da kuma Danfodiyo Sakkwato, wad&#8217;anda suka jima suna koyar da adabi tare da yin nazarin sa. Ya ce kuma a had&#8217;a da tsofaffin marubuta maza da mata don a tabbatar da adalci a gasar.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4368\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4368\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>AN dad&#8217;e ba a samu tagomashi a fagen rubutun Hausa ba, musamman na k&#8217;irk&#8217;ira. An bar marubuta kowa tasa ta fisshe shi. Hakan yana tattare da matsaloli da dama, ta yadda littattafan mu sun kasance cikin k&#8217;ask&#8217;anci, babu inganci, kuma babu k&#8217;ok&#8217;arin kawo sabon abu. Idan ba a yi wankiyar finafinan Indiya da na Turawa [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4368\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4368\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4368","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":25,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"AN dad&#8217;e ba a samu tagomashi a fagen rubutun Hausa ba, musamman na k&#8217;irk&#8217;ira. An bar marubuta kowa tasa ta fisshe shi. Hakan yana tattare da matsaloli da dama, ta yadda littattafan mu sun kasance cikin k&#8217;ask&#8217;anci, babu inganci, kuma babu k&#8217;ok&#8217;arin kawo sabon abu. Idan ba a yi wankiyar finafinan Indiya da na Turawa [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2007-07-24T05:35:42+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA\",\"datePublished\":\"2007-07-24T05:35:42+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368\"},\"wordCount\":1383,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368\",\"name\":\"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2007-07-24T05:35:42+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4368#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA - Ibrahim Sheme","og_description":"AN dad&#8217;e ba a samu tagomashi a fagen rubutun Hausa ba, musamman na k&#8217;irk&#8217;ira. An bar marubuta kowa tasa ta fisshe shi. Hakan yana tattare da matsaloli da dama, ta yadda littattafan mu sun kasance cikin k&#8217;ask&#8217;anci, babu inganci, kuma babu k&#8217;ok&#8217;arin kawo sabon abu. Idan ba a yi wankiyar finafinan Indiya da na Turawa [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2007-07-24T05:35:42+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA","datePublished":"2007-07-24T05:35:42+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368"},"wordCount":1383,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368","name":"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2007-07-24T05:35:42+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4368#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4368","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4368"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4368\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4368"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4368"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4368"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}