{"id":4299,"date":"2018-10-05T12:13:09","date_gmt":"2018-10-05T12:13:09","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4299"},"modified":"2023-10-07T23:07:33","modified_gmt":"2023-10-07T23:07:33","slug":"yadda-na-jagoranci-rubuta-littafin-tarihin-mamman-shata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299","title":{"rendered":"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata"},"content":{"rendered":"<p>A ranar Juma\u2019a, 21 ga Satumba, 2018 jaridar Aminiya (ta kamfanin\u00a0<em>Media Trust Limited<\/em>) da ke Abuja ta soma buga wata tattaunawa da ta yi da ni. Daga nan ta ci gaba da buga hirar a makwanni biyu masu zuwa, wato a ranakun 28 ga Satumba da 5 ga Oktoba. A rana ta farko, kanun labarin hirar (<em>headline<\/em>) shi ne \u201cNi Na Fara Aikin Rubuta Littafin Tarihin Shata \u2013 Ibrahim Sheme\u201d, a mako na biyu kuma kanun labarin shi ne, \u201cAbin Da Ya Sa Na Sake Rubuta Littafin Tarihin Shata Karo Na Biyu \u2013 Ibrahim Sheme\u201d, sannan na \u0199arshen shi ne \u201cIna Shirin Samar Da Gidauniyar Adana Ayyukan Shata Da Na Sauran Mawa\u0199a \u2013 Sheme\u201d.<\/p>\n<p><strong>Wanda ya yi hirar da ni shi ne Bashir Yahuza Malumfashi.\u00a0 Ga yadda hirar ta kasance:<\/strong><\/p>\n<p>*<\/p>\n<p><strong>Ni na fara aikin rubuta littafin tarihin Shata \u2013 Ibrahim Sheme<\/strong><\/p>\n<p><strong>A kwanakin baya ne marubuci kuma \u0257an jarida, Ibrahim Sheme ya fitar da wani babban kundi da ke \u0199unshe da tarihin shahararren mawa\u0199in Hausa, marigayi Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana da shi, inda ya warware zare da abawa na fa\u0257i-tashin da ya sha wajen samar da wannan littafi mai suna SHATA IKON ALLAH!<\/strong><\/p>\n<p>Daga Bashir Yahuza Malumfashi<\/p>\n<p><strong>Ko za ka bayyana yadda ka fara tunanin tunkarar rubutu game da marigayi Mamman Shata?<\/strong><\/p>\n<p>Da farko dai,mahaifi na ne ya fara ha\u0257a ni da Alhaji Mamman Shata. Sun san juna matu\u0199a ta yadda zan iya cewa mutumin sa ne \u0199warai duk da yake bai yi masa wa\u0199a ba. Mahaifi na shi ya \u0257auke ni ya kai ni wajen Shata, ya ce masa, \u201cTo ga \u0257an ka.\u201d Har Shatan ya yi ta mamakin cewa na yi girma haka. A lokacin, ban da\u0257e da gama jami\u2019a ba. To ni kuma sai soyayyar Shata ta \u0257arsu a zuciya ta, ya kasance a ko yaushe ina so in je in gan shi. Don haka a duk lokacin da na samu sarari, na kan je in gaida shi a gida.<\/p>\n<p>Ana cikin haka, ina aiki a Kaduna a matsayin Mataimakin Editan jaridar mako-mako ta\u00a0<em>Nasiha<\/em>, sai na yi tunanin me zai hana a matsayi na na marubuci in rubuta tarihin Shata? A lokacin, ba a damu da rubuta tarihin mawa\u0199an Hausa ba, an fi yin \u0199o\u0199arin rubuta tarihin wasu manyan mutanen irin \u2018yan siyasa da ma\u2019aikatan gwamnati da \u2018yan kasuwa don a kira taron \u0199addamarwa a samu ku\u0257i. Ni kuma ina yi wa Shata wani irin kallo na fasihin mutum wanda ya kamata a taskance ayyukan da ya yi a rayuwar sa. Ni mutum ne mai yawan karance-karance, don haka na jima da ganin alfanun hakan a wasu al\u2019ummomin. A \u0199arshe, sai na tafi Funtuwa na samu Alhaji Shata har gida, na fa\u0257a masa niyya ta, kuma ya amince da bu\u0199ata ta. A cikin 1991 na fara aikin, kuma na fara yin hirar farko da shi.<\/p>\n<p><strong>Littafin da ku ka ha\u0257u ku ka samar na farko mai suna \u201cShata Ikon Allah!\u201d, yaya al\u2019amarin ya gudana kuma me ya biyo baya?<\/strong><\/p>\n<p>Ni dai na fara aikin a 1991, to har na yi shekaru da farawa sai Allah ya ha\u0257a ni da wani mutum mai suna Aliyu Ibrahim \u0198an\u0199ara. Bari ka ji yadda abin ya faru. Daga 1991 \u0257in nan har zuwa 1996 na \u0257an yi abubuwa bakin gwargwado. A 1992 na bar jaridar\u00a0<em>Nasiha<\/em>, na zama Editan mujallar\u00a0<em>Rana<\/em>\u00a0(ta kamfanin mujallar\u00a0<em>Hotline<\/em>). A 1993 na tafi \u0199asar Birtaniya domin yin digiri na biyu a Jami\u2019ar Cardiff. Da na dawo, na \u0257an yi aiki a matsayin Editan mujallar\u00a0<em>Hotline<\/em>\u00a0kafin in koma jaridar kullum-kullum ta\u00a0<em>New Nigerian<\/em>, inda har na yi Mataimakin Edita.<\/p>\n<p>Duk a tsawon wannan lokaci ban daina aiki kan tarihin Shata ba. A daidai lokacin ina da wani aboki mai suna Ibrahim Malumfashi, wanda malami ne a Jami\u2019ar Usmanu \u018aanfodiyo a Sakkwato, yanzu kuma farfesa ne a Jami\u2019ar Jihar Kaduna. Wata rana, ina jin a cikin 1997 ne, sai ya zo har gida na ya ce mani akwai wani mutum da ya ce masa ya na so ya gan ni kan aikin rubuta tarihin Shata. Ya ce mani mutumin ya ce shi ma ya na rubuta tarihin Shata kuma ya na so mu ha\u0257e mu yi littafi \u0257aya. Ya ce sunan mutumin Aliyu Ibrahim \u0198an\u0199ara, wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, wato Kaduna<em>\u00a0Polytechnic.<\/em><\/p>\n<p>Kamar ba zan amince ba, amma Malumfashi ya ja hankali na kan cewa mu dai ha\u0257u da wancan \u0257in, in ji da wacce ya zo, kafin in yanke shawara. Sai na ce to shi kenan, su zo tare, in ga abin da shi \u0198an\u0199ara ya rubuta.<\/p>\n<p>Washegari, su ka zo gida na. \u0198an\u0199ara ya zo da littafi inda ya yi rubutu mai yawa da biro. Na kar\u0253a na shiga dubawa. Sai na lura da cewa \u0198an\u0199ara na da irin azamar da na ke bu\u0199ata, kuma har ya yi hira da wasu mutanen da Shata ya yi wa wa\u0199a wa\u0257anda ina so in yi hira da su. A lokacin ni ma fa na yi hirarraki da mutane da dama wa\u0257anda shi bai kai gare su ba, irin su Indon Musawa, Shehu Maigidaje, Goshin \u018aangude, Ahmadu Doka, Garban Bichi, dangin Shata a Musawa, da sauran su. To, sai na ga lallai ha\u0257ewar mu za ta taimaki dukkan mu; ka ga ai ba sai na tafi wajen wa\u0257ancan mutanen da ya yi hira da su ba, shi ma ba sai ya je wurin wa\u0257anda na yi hira da su ba. Saboda haka nan take na ce na yarda mu yi littafi \u0257aya. Babban dalili na shi ne ni ba domin in samu ku\u0257i na ke yin aikin ba, buri na dai in cimma nasarar tattara tarihin Shata, saboda haka ko waye ya zo ya ce mu ha\u0257u mu kai gaci zan amince.<\/p>\n<p>A nan \u0198an\u0199ara ya bar mani wannan rubutu da ya yi, a matsayi na na jagoran aikin. Haka kuma, bayan wani lokaci, na \u0257auke shi a mota ta, na kai shi wajen Shata a Funtuwa na ce, \u201cBaba, wannan shi ne wane. Yanzu da shi mu ke rubuta tarihin ka, ya na taimaka mani.\u201d Shata ya ce to ba komai tunda ni na yarda da hakan.<\/p>\n<p>To, daga nan fa sai mu ka bazama aiki, shi ya yi nan, ni in yi can. Wani lokacin mu tafi waje tare. Da yake aikin tattara tarihin Shata kamar teku ne, sai dai ka \u0257ebi na \u0257iba ka bar sauran, haka mu ka dinga tafi da aikin bakin iyawar mu.<\/p>\n<p>Ina so ka sani cewa babu wata \u0199ungiya ko wani mutum da su ka \u0257au nauyin mu kan wannan aikin; ni ne ke \u0257aukar nauyin yawancin aikin, da yake bakin gwargwado na fi \u0198an\u0199ara samu. Duk inda za mu, ni ke \u0257aukar nauyin mu. Haka kuma na kan tura \u0198an\u0199ara wasu wuraren, in ba shi ku\u0257in zuwa da dawowa. Misali, na tura shi Bauchi ya wo mana hira da Garkuwan Bauchi Alhaji Ahmed Kari, na tura shi Gombe ya yi mana hira da Garkuwan Gombe Alhaji Bappa Ahmed, wanda Shata ya yi wa wa\u0199ar \u201c\u018aan Liman Uban Ciroma, \u018aan Shehu Garkuwa\u201d, na tura shi Musawa ya wo mana hira da Magajin Gari Abdullahi Inde da su Ayuba Mainama da sauran su dai. Amma ya kamata ka sani, ni ma fa ba a kwance na ke ba, ina nawa rangadin. Kuma dai ni ne ke zuwa wajen Shata a kai a kai, ina sanar da shi halin da ake ciki.<\/p>\n<p>Ana cikin haka, ran nan na je wajen Shata sai ya sanar da ni cewa wasu mutum biyu sun same shi a <em>Kabo Guest Inn\u00a0<\/em>a Kano, wato otal \u0257in Jarman Kano Alhaji Muhammadu Adamu \u018aankabo, sun fa\u0257a masa cewa su na rubuta tarihin rayuwar shi. Ya ce, \u201cKa san su?\u201d Na ce ban san su ba. Sai nan take wasu yaran Shata da na ke da matu\u0199ar kusanci da su, irin su Alhaji Ya\u2019u Wazirin Shata, su ka ce ai kuwa ya kamata a kira su nan Funtuwa a hana su ci gaba da aikin, domin dai ni aka sani, ni aka amince wa.<\/p>\n<p>Shata ya yarda. Ya ce to yaya za a yi a gano su? Na ce ina da abokai marubuta a Kano, zan iya zuwa in gano su. Aka sa ranar da za a ce su zo Funtuwa mu ha\u0257u mu duka idan na gano su. Daga Funtuwa, na ja mota ban zame ko\u2019ina ba sai Kano. Ta hanyar wani aboki na, marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino, na shiga bincike har aka kai ni wani gida a unguwar Daneji, aka ce nan ne gidan su Ali Malami, wato \u0257aya daga cikin wa\u0257anda aka samu labarin su na aiki kan tarihin Shata. Na yi masa sallama, ya fito. Da mu ka tattauna, ya tabbatar mani da cewa lallai shi da wani mai suna Yusuf Tijjani Albasu sun fara rubuta tarihin Shata. Na isar da sa\u0199on cewa to Shata na neman su a Funtuwa a rana kaza. Ya ce to in-sha Allah za su je. Ban fa\u0257a masa matsayi na a wajen rubuta tarihin Shata ba.<\/p>\n<p>Daga Kano, sai na zarce zuwa gida Kaduna. Na samu Aliyu na fa\u0257a masa abin da ake ciki. Da ranar ta zo, mu ka rankaya zuwa Funtuwa \u2013 ni da \u0198an\u0199ara da wani aboki na da na \u0257auka a Zariya, wato Yahaya Umar. Mu ka yi sa\u2019a, Alhaji Shata bai je ko\u2019ina ba. Da ya fito zaure ya zauna, aka taru kamar kullum, ana jiran isowar Kanawan nan. Can kuwa sai ga su sun iso tare da wani abokin su. Kuma sun zo da littafin su kamar yadda aka ce su yi. Abin da aka shirya shi ne idan sun zo, za a \u0199wace littafin ne, a kore su bisa hujjar cewa Shata bai ba su izinin rubuta tarihin rayuwar shi ba! To amma sai na ce a ba ni dama in duba aikin da su ka yi. Su duk ba su san shirin da aka yi ba.<br \/>\nNa kar\u0253i littafi biyu da su ka cika da rubutu da biro, mu ka koma waje, na jingina da mota na shiga dubawa. Littafi \u0257aya na \u0199unshe da matanonin wasu wa\u0199o\u0199in Shata, yayin da \u0257ayan \u2013 wanda shi ya fi jan hankali na \u2013 ya na \u0257auke da hirarraki da wasu mutane da Shata ya yi wa wa\u0199a. Kamar dai yadda na gano lokacin ha\u0257ewa ta da \u0198an\u0199ara, sai na ga cewa lallai Kanawan nan sun yi aiki irin wanda na ke so; sun yi hira da wasu mutane wa\u0257anda mu ke da burin ganawa da su, irin su Delun Kunya, Abubakar Uwawu, Umaru \u018aan \u018aanduna, Liman \u2019Yalleman, Laila Dogonyaro, da sauran su.<br \/>\nDa mu ka koma gaban Shata, sai na ce masa, \u201cBaba, ni ina ganin ya kamata mu ha\u0257e da wa\u0257annan su ma, a yi littafi \u0257aya.\u201d<br \/>\nSai mamaki ya kama kowa. Shata ya ce, \u201cHaka ka ke so?\u201d Na ce, \u201cE.\u201d Ya ce, \u201cTo ai shi kenan.\u201d Sai na ba da shawarar mu koma waje mu tattauna tare da Ali Malami da Yusuf Tijjani Albasu. Da mu ka koma, na fa\u0257a masu irin aikin da mu ka yi, kuma na nuna masu namu aikin tare da \u0257imbin hotunan da mu ka tara. Nan take su ma su ka amince da cewa mu ha\u0257e mu hu\u0257u mu yi littafi \u0257aya.<\/p>\n<p>Bayan mun tattauna, na rubuta takardar yarjejeniya, mu ka koma gaban Shata, na karanta ta kowa ya ji. Aka amince, kowa ya rattaba hannu a kan cewa mun ha\u0257e.<\/p>\n<p>Daga nan, aiki ya koma \u0257anye. A matsayi na na jagoran aikin, na kira taro a Kaduna, inda mu ka tattauna kan yadda aikin zai kasance, musamman abin da ya rage mana, da kuma yadda za a yi mu ci gaba da tunkarar aikin. Kowanen mu zai ci gaba da bincike kamar yadda mu ka faro, sannan ni ne marubucin littafin, wato ni ne zan karanta abin da kowanen mu ya farauto, in sa\u0199a shi cikin sassan littafin kamar yadda na tsara shi.<\/p>\n<p>A tsawon lokacin da mu ka yi, na lura da wani abu. Abokan aiki na sun damu matu\u0199a kan lallai in gama littafi a \u0199addamar da shi. Ni kuma gani na ke ta yi har yanzu ban samu kaiwa inda na ke so littafin ya kai ba; kullum gani na ke yi akwai gi\u0253i nan da can. Ana haka, har Shata ya fara ciwon ajali, ya koma ga Mahaliccin shi. A \u0199arshe, littafin bai fito ba sai a cikin 2006, wato shekara bakwai bayan rasuwar Shata.<\/p>\n<p><strong>Ga shi bayan wasu shekaru masu yawa, ka fito da sabon littafin \u201cShata Ikon Allah!\u201d Yaya aka yi haka ta faru?<\/strong><\/p>\n<p>Da aka \u0199addamar da littafin mu na farko a Gidan Arewa a Kaduna, sai mu ka lura da cewa ba mu samu ku\u0257i ba kamar yadda mu ke so. Yawancin mutanen da su ka yi al\u0199awarin ba da ku\u0257i a wurin, ciki har da babban mai \u0199addamarwa, ba su cika al\u0199awarin su ba \u2013 har yau \u0257in nan! Wasu ma cakin ku\u0257i na bogi su ka bayar a bikin \u0199addamarwar. Sannan kwafen littafin guda 1,000 da aka ce za a buga mana, ba mu samu ko da 600 ba, saboda haka babu ma na sayarwa. Aka bar mu da basussuka. Hakan ya sa mu ka kasa ba iyalin Shata ko sisi kamar yadda yarjejeniya ta bu\u0199aci mu yi.<\/p>\n<p>Sai mu ka zauna mu ka shawarta cewa mu yi \u0199o\u0199arin sake fito da littafin don mu sayar, mu ga ko za mu fanshe ta nan. Sai na ce kowanen mu ya je ya karanta littafin ya ga ko akwai kurakurai da ya kamata mu gyara, da yake ni na rubuta shi na bayar aka buga ba tare da sauran sun samu lokacin karanta shi kafin a buga ba. Haka kuma na ce ya kamata mu zurfafa bincike, tare da tattaunawa da wasu mutanen wa\u0257anda ba mu samu zantawa da su ba kafin a buga littafin. Mu ka rabu a kan haka.<\/p>\n<p>To, tun daga nan fa sai na fara Allahn-ba-ku da abokan aikin nawa. Kusan kowanen su ya \u0199i ba ni ha\u0257in kai kan abin da na ke so mu yi. A gani na, sun gaji da aikin. Mutum \u0257aya ne ma ya karanta littafin ya ba ni wuraren da ya gano an yi kuskuren rubutu, misali a rubuta \u2018Shta\u2019 maimakon \u2018Shata\u2019 ko \u2018Dara\u2019 maimakon \u2018Daura\u2019. Amma su kurakuran ma ba su da yawa sosai. Daga nan babu wanda ya ba ni ko kalma \u0257aya a matsayin \u0199arin bayani na bincike ko hira da wani mutum. Duk wanda na nemi ya yi wani abu, sai ya goce. Kai, akwai ma wanda ya turo mani da sa\u0199on tes daga Kano ya ce don Allah don Annabi in rabu da shi, shi ya fita in dai aikin littafin Shata ne, ba ya so! Na kira abokin aikin mu \u0257ayan, na fa\u0257a masa, ya ce e, shi ma ya fa\u0257a masa haka. Shi kenan, ni sai na ci gaba da bincike na.<\/p>\n<p>Abin ban-mamakin ma, sai na samu labarin cewa Aliyu Ibrahim \u0198an\u0199ara na can ya na \u0199o\u0199arin fito da wani littafin kan Shata. Da na tuntu\u0253e shi kan maganar, da farko ya ce \u0199arya ake masa. Mun \u0257au shekaru ina fama da shi a kai, domin an kai lokacin da na tabbatar da cewa lallai ya na kan aikin, ina nuna masa cewa sake fito da wani littafin zai kasance cin amanar mu duka. Na zauna da shi a Kaduna da Katsina ba sau \u0257aya ba, ina nuna masa cewa abin da ya ke so ya yi bai dace ba, musamman tunda babu yadda za a yi ya rubuta wani littafi ba tare da ya kwashe bayanan da ke cikin wanda na rubuta ba, kuma idan ya yi hakan zai kasance ya karya dokar ha\u0199\u0199in mallaka tare da satar basira. Na ce masa kamata ya yi ya ba ni duk wani sabon bincike da ya yi, in ha\u0257a da wanda na yi, a zuba cikin sabon littafin da mu ka amince mu yi.<\/p>\n<p>Da \u0199yar na samu ya ba ni wani sashe na littafin, daga babi na 1 zuwa na 6; ya aiko mani da shi ta hanyar Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, ya kawo mani a Kaduna. Ya ha\u0257o da hotuna ka\u0257an, sannan ya turo mani wasu hotunan ta imel.\u00a0 Da na duba, sai na kira shi na ce to ina sauran littafin? Ya ce iyakar abin da ya rubuta kenan. Na san ba haka ba ne. Duk da haka, na karanta na \u0257auki abin \u0257auka, na watsar da yawancin abin da ke ciki domin kuwa an kwaso wajen kashi 80 cikin \u0257ari ne daga bugun farko na \u201cShata Ikon Allah!\u201d A \u0199arshe ma dai, sai na bi wata hanya na samo sauran littafin da ya hana ni, wato babi na 7 zuwa \u0199arshe, kuma na kira shi na fa\u0257a masa, har na karanta masa abubuwan da ke ciki. Ya yi ta mamaki.<\/p>\n<p>Na \u0257auka zai karaya, ya bari mu ha\u0257e kamar yadda ya amince. Amma sai na ri\u0199a jin cewa ya na fa ci gaba da \u0199o\u0199arin fito da littafin, har ya rubuta takardu zuwa ga gwamnatin Jihar Katsina, ya na ro\u0199on ta ba shi ku\u0257i ya buga littafin. Duk na samu takardun da ya rubuta, kuma na sanar da shi.<\/p>\n<p>A \u0199arshe dai, kwatsam sai na ji Aliyu ya fitar da littafi. Ina jin ko a 2016 ne? Da na ga haka, sai na \u0199yale shi. Na ce in dai don ya na ganin zai samu ku\u0257i da littafin ne kamar yadda ya ke ta tsinkaya, to ya je ya samu. Ni dai ba domin ku\u0257i na ke fafutikar tattara tarihin Shata ba. Don haka sai na yi bakam, na ci gaba da nawa binciken ni ka\u0257ai, ina yi ina rubuta littafi, har tsawon shekarun nan goma sha biyu. A \u0199arshe, na \u0199are, na gamsu da cewa littafin ya kai matsayin a fito da shi.<\/p>\n<p>Kada ka manta, wannan littafin da ya fito ya \u0199unshi \u201cShata Ikon Allah!\u201d na farko, ya \u0199unshi littafin Aliyu \u0198an\u0199ara mai suna \u201cMahadi Mai Dogon Zamani\u201d &#8211; wanda shi ne sunan\u00a0 farko da na ra\u0257a wa namu littafin kafin Dakta Aliyu Modibbo Umar ya ba ni shawarar cewa in canja masa suna zuwa \u201cShata Ikon Allah!\u201d &#8211; sannan ya \u0199unshi sabon binciken da na yi. Saboda haka wannan sabon littafin da na fito da shi, in dai ka same shi, to ba ka bu\u0199atar wancan namu na farkon da kuma na \u0198an\u0199ara domin ya \u0199unshi dukkan su. Abin da babu a ciki daga na \u0198an\u0199ara yawanci shi ne irin almarorin nan da ya ke ya\u0257awa game da Shata, misali wai an yi wa mahaifin Shata girka har aljanu su ka yi bushara da haihuwar mawa\u0199in, ko a daren da aka haifi Shata an ji ki\u0257an kalangai na tashi a sararin samaniyar garin Musawa, ko kuma Shata ba mutum ba ne aljani ne.<\/p>\n<p><strong>Menene bambance-bambancen da ke tsakanin wannan sabon littafin da na farko?<\/strong><\/p>\n<p>Bambanci na farko shi ne wanda ido ke gani tun kafin mutum ya bu\u0257a littafin. A bugun farko, shafi sama da 600 ne, wannan kuwa shafi 921 ne; a da, ya ma haura shafi 1,000. Na biyu shi ne a wajen ingancin \u0257ab\u2019i ya ninka wancan. Na uku, za ka ga duk da yake sunayen mu hu\u0257u duk sun fito, amma suna na ne mafi girman rubutu domin in nuna cewa ni ne na rubuta littafin, to amma na amince da cewa akwai gudunmawar sauran masu binciken a ciki. Kuma ba handame littafin na yi ba, domin ko jiya mun yi waya da Yusuf Albasu cewa za mu kira taron mu hu\u0257u mu zauna mu tattauna kan ha\u0199\u0199in kowa a littafin. Na biyar, a wannan karon littafin kala biyu ne, wato mai \u0199arfin bango da mai laushin bango.<\/p>\n<p>Idan ka shiga cikin littafin, za ka ga shafuka masu kala fiye da na da, da \u0257aruruwan hotuna kuma masu fa\u0257i.<\/p>\n<p>To amma babban bambancin shi ne bayanan da littafin ya \u0199unsa. Sun fi na farkon yawa, da kuma inganci. A wannan sabon littafin akwai hirarraki da \u0199arin wasu mutanen wa\u0257anda Shata ya yi wa wa\u0199a ko ya yi hul\u0257a da su, akwai tarihe-tarihe na wasu mawa\u0199an da wasu mutanen. Sannan a littafin farko, akwai kurakurai na wasu bayanan. Misali, ko Jami\u2019ar Ahmadu Bello da za ta ba Shata digiri cewa ta yi mahaifiyar Shata \u201cFulata-Borno\u201d ce \u2013 wato Fulanin da su ka fito daga gabas, su ka zo \u0199asar Hausa kafin da bayan Jihadin Shehu Usmanu \u018aanfodiyo. Mu ma a littafin farko (da ma na \u0198an\u0199ara \u0257in) haka mu ka rubuta. To amma da na je Tofa, garin mahaifiyar Shata, sai na gano cewa ashe ita Babarbara ce, domin mahaifin ta Kanuri ne.<br \/>\nSannan a da, ana cewa wani aminin Shata tun su na yara a Musawa, mai suna Malam \u018aan\u0199ane, wai \u0257an\u2019uwan Shata ne na jini. Ashe ba haka ba ne, ba su ha\u0257a komai ba sai ma\u0199wabtaka da kuma amintaka. Na yi sabuwar hira da Alhaji Balan Guzun, \u0257an\u2019uwan Shata, da shi kan shi \u018aan\u0199ane \u0257in, mako uku kafin a buga littafin, inda na gano ashe ba \u0257an\u2019uwan su ba ne na jini. Sannan a da ana cewa mahaifiyar Shata ta ta\u0253a yin aure a Ingawa, ashe ba haka ba ne. Kai, ga su nan dai!<\/p>\n<p><strong>Ganin cewa marigayi Shata ya rasu bai ga littafin na farko ba balle wannan, yaya dangantakar ku ta ke da iyalan sa?<\/strong><\/p>\n<p>Tun farko ina da kyakkyawar dangantaka da iyalin Shata. Farkon mu\u2019amala ta da shi ma, &#8216;ya\u2019yan nasa yawanci \u0199anana ne, amma yanzu duk sun girma, sun hayayyafa. Yaran Shata irin su marigayi Alhaji Ya\u2019u Waziri da marigayi Alhaji Bawa Dungun-Mu\u2019azu sun san ni da Shata, don haka kowanen su har gida na ke samun shi mu yi hira. Sannan ina da amini a gidan Shata, wato Alhaji Mustapha Sulaiman Shata, wanda \u0257a ne ga mawa\u0199in, to ya taimaka \u0199warai wajen bu\u0257e mani \u0199ofofi a farkon fara bincike na.<\/p>\n<p>Bayan rasuwar Shata kuma, sai uwargidan shi, wato marigayiya Hajiya Furera, ta ri\u0199e ni kamar \u0257an ta; ko wane irin bayani na nema game da Alhaji, za ta ba ni ko da a waya ne. Akwai kuma kishiyar ta, Hajiya Dije, mahaifiyar Sanusi Shata, ita ma mu na zumunci sosai, kuma har zuwa daf da buga wannan sabon littafin ta taimaka mani sosai. Misali, lokacin da na ke neman wani hoto, sai ta tashi takanas daga Funtuwa ta tafi garin mahaifin ta, wato Falgore, ta kwaso dukkan hotunan ta na rayuwar ta da Shata, ta ba ni. Da yake Hajiya Furera kuma ta rasu, sai \u0257an ta, Bishir, wanda ke aiki a Maiduguri, ya ba da umurni ga matar sa cewa ta kwaso dukkan hotunan mahaifiyar tasa da ke cikin wani buhu, a ba ni. To ka ga akwai kyakkyawar dangantaka tsakani na da iyalin Shata. Kuma har yau \u0257in nan ina kallon kai na a matsayin \u0257an\u2019uwan su, tunda ni mai \u0199aunar Alhaji ne irin na har abada. Don haka ina matu\u0199ar son ganin cewa rayuwar zuri\u2019ar sa ta inganta \u0199warai da gaske.<\/p>\n<p><strong>Wane irin shiri ka ke yi game da wannan littafi na Shata yadda zai shiga duniya kuma ya zama wata sila na taskance ayyukan mawa\u0199an Hausa, ban a Shata ka\u0257ai ba?<\/strong><\/p>\n<p>Shekaru masu yawa da su ka gabata, na ta\u0253a jagorantar wani yun\u0199uri na kafa wata \u0199ungiya mai suna Gidauniyar Mamman Shata ko Cibiyar Mawa\u0199a Da Ka\u0257e-Ka\u0257e ta Mamman Shata, ba domin komai ba sai domin a taskance ayyukan da Shata da sauran mawa\u0199an Hausa su ka yi wajen adana adabin malam Bahaushe. Shugaban \u0199ungiyar shi ne Alhaji Hamisu Gamarali Funtuwa, ni kuma sakatare. \u0198ungiyar ba ta siyasa ba ce, kuma ba ta neman ku\u0257i ko riba ba ce. Amma tun tashin farko mun samu matsala domin wani kuskure da mu ka tafka. In-sha Allah za mu sake zama domin farfa\u0257o da \u0199ungiyar da gyara mata fasali.<\/p>\n<p>Burin \u0199ungiyar shi ne ta samar da wani gida inda za a ri\u0199a tara dukkan wa\u0199o\u0199in Hausa, ba na maka\u0257an zamanin da ba ka\u0257ai, har da na yanzu, irin su Aminu Ala da Mudassir \u0198asim da Fati Nijar da Maryam Fantimoti da Yahaya Makaho da Umar M. Shareef da sauran su, ta yadda duk mai nema zai je ya samu. Na yi la\u2019akari da cewa idan wasu mutane da ke rirri\u0199e da wa\u0199o\u0199in su ka shu\u0257e, to wasu wa\u0199o\u0199in sun salwanta kenan. A yanzu haka ma akwai wa\u0199o\u0199in Hausa da su ka \u0253ata, sai ka sha wuya kafin ka samu wata wa\u0199ar.<\/p>\n<p><strong>Wane kira za ka yi ga gwamnati da cibiyoyin ilimi da attajirai da ma al\u2019ummar Hausa gaba \u0257aya dangane da Shata?<\/strong><\/p>\n<p>Kiran da zan yi shi ne su yi \u0199o\u0199ari su ga an taskance dukkan ayyukan adabi na Malam Bahaushe. A nan, ba wa\u0199a ka\u0257ai ba, har ma finafinai da littattafai da hotuna da sauran su. Wa\u0257annan abubuwan su ne ke \u0257auke da tarihin al\u2019adun mu, wa\u0257anda zamani ke shafewa a hankali. Ba cewa na yi a kafe kan al\u2019ada ba, domin sauyawa ta ke yi, to amma a ri\u0199a adana ta saboda &#8216;yan baya su gani kuma su ji yadda kakannin su su ke a da. Misali, yanzu kayan ki\u0257an Hausawa da dama sun \u0253ace; haka abinci da sutura da magunguna. Ko gidan tattara kayan tarihi ka je ba za ka samu wani abin ba. Yanzu ina hoton Naramba\u0257a? Babu! Hotunan \u018aan\u2019anace guda nawa ka gani? Ba su da yawa! Ko Abubakar Imam hotunan shi guda nawa ake da su? Ba yawa! Shin akwai ma muryar sa a wani faifai kuwa? Ban ta\u0253a ji ba! To, ha\u0199\u0199i ne da ya rataya a wuyan duk wanda zai iya da ya bayar da tasa gudunmawar don adana irin wa\u0257annan abubuwan. Haka ake yi a duk \u0199asashen da su ka ci gaba.<\/p>\n<blockquote><p><strong>Bayan fitar da wannan babban kundi kan Shata, me kuma al\u2019umma za su tsimaya daga gare ka a nan gaba?<\/strong><\/p><\/blockquote>\n<p>Ina da wasu shirye-shirye na wa\u0257ansu abubuwan da na ke so in yi. Idan har Allah ya ara mani tsawon kwana da lafiya da lokaci, za a ji ni na sake fito da wani abin.<\/p>\n<figure id=\"attachment_4310\" aria-describedby=\"caption-attachment-4310\" style=\"width: 225px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" data-attachment-id=\"4310\" data-permalink=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?attachment_id=4310\" data-orig-file=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2018\/10\/IMG_20181008_235623-1.jpg\" data-orig-size=\"240,320\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"IMG_20181008_235623-1\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Shafin da Aminiya ta fara bugawa na hirar&lt;\/p&gt;\n\" data-large-file=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2018\/10\/IMG_20181008_235623-1.jpg\" class=\"size-medium wp-image-4310\" src=\"https:\/\/wip.ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2018\/10\/IMG_20181008_235623-1-225x300.jpg\" alt=\"\" width=\"225\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2018\/10\/IMG_20181008_235623-1-225x300.jpg 225w, https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2018\/10\/IMG_20181008_235623-1.jpg 240w\" sizes=\"auto, (max-width: 225px) 100vw, 225px\" \/><figcaption id=\"caption-attachment-4310\" class=\"wp-caption-text\">Shafin da Aminiya ta fara bugawa na hirar<\/figcaption><\/figure>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4299\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4299\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ranar Juma\u2019a, 21 ga Satumba, 2018 jaridar Aminiya (ta kamfanin\u00a0Media Trust Limited) da ke Abuja ta soma buga wata tattaunawa da ta yi da ni. Daga nan ta ci gaba da buga hirar a makwanni biyu masu zuwa, wato a ranakun 28 ga Satumba da 5 ga Oktoba. A rana ta farko, kanun labarin [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4299\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4299\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4297,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4299","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":112,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A ranar Juma\u2019a, 21 ga Satumba, 2018 jaridar Aminiya (ta kamfanin\u00a0Media Trust Limited) da ke Abuja ta soma buga wata tattaunawa da ta yi da ni. Daga nan ta ci gaba da buga hirar a makwanni biyu masu zuwa, wato a ranakun 28 ga Satumba da 5 ga Oktoba. A rana ta farko, kanun labarin [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2018-10-05T12:13:09+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2023-10-07T23:07:33+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg?fit=240%2C320&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"240\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"320\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"22 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata\",\"datePublished\":\"2018-10-05T12:13:09+00:00\",\"dateModified\":\"2023-10-07T23:07:33+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299\"},\"wordCount\":4497,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG_20180829_194312-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299\",\"name\":\"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG_20180829_194312-1.jpg\",\"datePublished\":\"2018-10-05T12:13:09+00:00\",\"dateModified\":\"2023-10-07T23:07:33+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG_20180829_194312-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG_20180829_194312-1.jpg\",\"width\":240,\"height\":320,\"caption\":\"Littafin \\\"Shata Ikon Allah!\\\"\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4299#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata - Ibrahim Sheme","og_description":"A ranar Juma\u2019a, 21 ga Satumba, 2018 jaridar Aminiya (ta kamfanin\u00a0Media Trust Limited) da ke Abuja ta soma buga wata tattaunawa da ta yi da ni. Daga nan ta ci gaba da buga hirar a makwanni biyu masu zuwa, wato a ranakun 28 ga Satumba da 5 ga Oktoba. A rana ta farko, kanun labarin [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2018-10-05T12:13:09+00:00","article_modified_time":"2023-10-07T23:07:33+00:00","og_image":[{"width":240,"height":320,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg?fit=240%2C320&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"22 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata","datePublished":"2018-10-05T12:13:09+00:00","dateModified":"2023-10-07T23:07:33+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299"},"wordCount":4497,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299","name":"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg","datePublished":"2018-10-05T12:13:09+00:00","dateModified":"2023-10-07T23:07:33+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg","width":240,"height":320,"caption":"Littafin \"Shata Ikon Allah!\""},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4299#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG_20180829_194312-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4299","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4299"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4299\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4878,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4299\/revisions\/4878"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4297"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4299"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4299"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4299"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}