{"id":4291,"date":"2010-10-05T10:40:43","date_gmt":"2010-10-05T10:40:43","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4291"},"modified":"2010-10-05T10:40:43","modified_gmt":"2010-10-05T10:40:43","slug":"malam-turi-ba-rabo-da-gwani-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291","title":{"rendered":"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026"},"content":{"rendered":"<p>A ranar 17 ga Satumba, 2010, Allah ya \u0257auki ran Malam Turi Muhammadu, a Kaduna. Shekarun sa 70 a duniya. Kafin rasuwar tasa, ya ta\u0253a ri\u0199e mu\u0199amin editan jaridar New Nigerian, sannan daga bisani ya zama manajan daraktan kamfanin da ke buga jaridar. Malam Turi fitaccen \u0257an jarida ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban aikin jarida a \u0199asar nan. Sai dai kash! yawancin mutane, ciki kuwa har da wa\u0257anda su ka san shi, farin sani, ba su kula sosai da nasarorin da malamin ya samu a wannan fagen ba har sai da ya koma ga Mahaliccin sa. Da ma akwai irin wa\u0257annan mutanen jingim a garuruwan mu \u2013 wa\u0257anda su ka yi abin a zo a gani amma ba a damu ba har sai wani abu ya faru gare su, musamman ma mutuwa.<\/p>\n<p>Kamar yadda mu ka gani a makon jiya, \u2019yan jarida da dama a Nijeriya sun ci moriyar tarayyar su da Malam Turi. Da yawa, ya kasance uba a gare su a lokacin da ya ke aikin jarida da kuma bayan ya bar aikin. Daga rubuce-rubucen ta\u2019aziyya da \u2019yan jarida irin su Sam Nda-Isaiah da Mohammed Haruna da Clem Baiye da Adamu Adamu da wasu su ka yi a jaridu, za mu iya fahimtar cewa Malam Turi babban masani ne a wannan fage, wanda ya yi amfani da \u0199warewar sa don ciyar da aikin jarida gaba, sannan mutum ne mai son ganin cewa an ci gaba da ya\u0257a \u0199udirorin dalilan kafa jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo, ba kawai ga kamfanin ba a yau, a\u2019a har ma ga maza da matan da su ka ta\u0253a yin aiki a kamfanin amma yanzu su na rubutu ko gudanar da wasu kafafen ya\u0257a labaran na Arewa. Don haka ne ma ya ke sa ido kan mutanen da ke aiki a wasu jaridu ko ko gudanar da jaridun da ke da ala\u0199a ta asali da kamfanin New Nigerian, wato jaridu irin su Daily Trust, Leadership da Peoples Daily. Na tabbatar da cewa \u2019yan jarida da dama da ke aiki a wa\u0257annan jaridun \u2013 da kuma wa\u0257anda har yanzu su ke a New Nigerian a yau \u2013 za su shaida cewa Malam Turi ya na daga cikin dattawa \u0199alilan da su ka damu da yin mu\u2019amala da su, su na tuntu\u0253ar su, ba don komai ba sai don ganin cewa sun ci gaba da yin aiki a bisa turbar kyakkyawar tarbiyya da bin \u0199a\u2019idojin aikin jarida. Wasu daga cikin su, ya \u0257auke su kamar \u2019ya\u2019yan sa a aikin, yayin da wasu kuma ya \u0257auke su jikokin sa.<\/p>\n<p>Ni \u0257in nan ina daga cikin irin wa\u0257annan mutanen. Na fara ha\u0257uwa da Malam Turi shekaru 13 daidai da su ka wuce, lokacin da ya aiko mani da wata wasi\u0199a da ya rubuta da hannun sa ya ce ya na so ya gan ni. Na yi mamaki \u0199warai, tare da jin da\u0257i, a ce babban mutum kamar sa ne ya ke so ya gan ni. A takardar, ya ce ya samu labarin cewa ina \u0199o\u0199arin rubuta tarihin sarkin mawa\u0199an Hausa, Alhaji Mamman Shata, kuma ya na so mu sadu don ya fa\u0257a mani wasu abubuwa wa\u0257anda \u0199ila su taimaka mani a aikin. A lokacin, ban ta\u0253a ganin Malam Turi ba, illa iyaka dai na kan ji labarin sa a matsayin fitaccen \u0257an jarida da ake girmamawa. To amma dai na san cewa \u2019yan jarida su kan yi sha\u2019awar abubuwa da dama a rayuwa, wato ban da aikin su, ciki kuwa har da son ka\u0257e-ka\u0257e da wa\u0199e-wa\u0199e. Da ma tun kafin lokacin, wani tsohon manajan daraktan kamfanin buga jaridun New Nigerian \u0257in, wato Alhaji Tukur Othman, ya ta\u0253a kira na ya yi doguwar hira da ni kan dangantakar Shata da wasu manyan \u2019yan bokon Arewa da ke zaune a Kaduna a lokacin da Shatan ya ke kan \u0199ololuwar tashe, irin su Alhaji Sani Zangon Daura.<\/p>\n<p>Na samu Malam Turi a gidan sa da ke unguwar Malali, Kaduna, a ran 22 ga Yuli, 1997, kamar yadda mu ka aje. Ba zan ta\u0253a mantawa da wannan ha\u0257uwar ba. Na farko, na yi sha\u2019awar rashin girman kan sa da \u0199o\u0199arin sa na faranta mani rai. Malamin ya ce lallai in tashi daga \u0199asa inda na zauna na har\u0257e don girmamawa, in koma kan kujera kusa da shi. Sa\u2019annan ya sa aka kawo mana abinci. Da \u0199yar na samu na \u0257an ci abincin domin gwarzantakar sa a fagen da na ke fafutikar yin nawa sunan duk ta miskile ni.<\/p>\n<p>A tattaunawar mu, Malam ya nuna mani cewa ya na biye da abubuwan da na ke yi a fagen aikin jarida. Ya san cewa na ta\u0253a ri\u0199e mu\u0199amin mujallar Rana da mujallar Hotline shekaru biyar da su ka gabata, bayan na yi wasu shekarun a kamfanin jaridar The Reporter, na kuma samo digiri na biyu a aikin jarida a \u0199asar Birtaniya, sannan yanzu kuma ina aiki a New Nigerian a matsayin \u0257aya daga cikin \u0199usoshin gidan. Ita ma tattaunawar da mu ka yi a kan Mamman Shata, ta karantar da ni abubuwa da dama. Ni a da na \u0257auka na san duk wani abu game da Shata ta yadda ba wani sabon abu da wani zai iya fa\u0257a mani kuma, ballantana kuma wani Banufe. To amma Malam ne ya fa\u0257a mani wani abu da ban sani ba: wato yawan wa\u0199o\u0199in zambo da Shata ya yi bai kai ko cikin cokalin wa\u0257anda ya yi na yabo ba, wanda hakan ya taimaka masa wajen samun \u0199arin farin jini da kuma \u0257aukaka. Da na dubi wannan magana da kyau, sai na ga gaskiya haka \u0257in ne. Wa\u0257annan bayanai da Malam Turi ya yi mani su na cikin littafin da mu ka yi mai taken &#8216;Shata Ikon Allah!&#8217; mai shafi 604, wanda aka wallafa a cikin 2006, kuma mun nuna cewa shi ne ya fa\u0257a.<\/p>\n<p>Mu\u2019amalar mu da Malam ta ci gaba ne kwan-gaba-kwan baya; sai a jima ba mu ha\u0257u ba, wanda laifi na ne. Ya kan so mu ha\u0257u a kai a kai, to amma sai in kasa kamar yadda na ke so. Na kan la\u0253e da cewa saboda ina da gida biyu ne, \u0257aya a Kaduna \u0257aya a Kano. Amma yanzu idan na tuna baya sai in ga cewa wannan ba \u0199wa\u0199\u0199warar hujja ba ce, kuma na yi nadamar rashin kusantar Malam kamar yadda ya ke so. Na yi nadamar rashin yin kiwo sosai a cikin faffa\u0257ar gonar ilimin sa don in \u0199aru da basirar sa, wanda a shirye ya ke ya \u0199osar da ni daga gare ta. Na kan \u0257an yi \u0199o\u0199arin ganin sa jefi-jefi. Kuma a ko yaushe ya kan kar\u0253e ni hannu biyu-biyu, tare da tambaya ta, \u201cShin wane ya fa\u0257a maka cewa ya gaida mani da kai lokacin da ya zo nan gidan?\u201d<\/p>\n<p>Ba shakka, idan abokai na sun je gidan sa su kan ce mani, \u201cNa je gidan Malam Turi kwanan nan, ya ce in gaida kai.\u201d Da zarar na ji haka, sai in ji kunya ta rufe ni. Nan da nan na kan yi al\u0199awarin cewa lallai zan ziyarce shi don mu ci gaba da wata tattaunawa wadda wata\u0199ila mu ka fara a zuwan da na yi gidan sa can a baya.<\/p>\n<p>A ko yaushe Malam ya na so in ci gaba da zama \u0257an jarida, ya kan ce Arewa ta na bu\u0199atar mutane iri na a aikin. Amma bayan na yi aikin shekara hu\u0257u a New Nigerian, inda na ri\u0199e mu\u0199amai daban-daban kamar su editan ma\u0199aloli, editan labaran \u0199asashen waje, editan adabi, sakataren kwamitin editoci, har zuwa mataimakin edita, sai na aje aikin. Dalili shi ne an yi wata shida ba a biya albashi ba, wanda ya sa na fara tunanin irin makoma ta idan na zauna a aikin da ba zai iya ba ni damar ci da iyali na ba. A \u0199arshe dai, na dawo aikin jaridar, kuma na ji da\u0257in hakan.<\/p>\n<p>Malam Turi mutumin } \u0199warai ne wanda ke son ganin ci-gaban Arewa. Abin ba\u0199in ciki shi ne bai yi tasiri a siyasa da ya shiga ba, bai samu cin za\u0253en zama sanata ba bayan ya bar aiki a New Nigerian a cikin 1980. Ya yi la\u2019akari da cewa siyasa mugun wargi ce, wadda bai kamaci mutane irin sa ba. Na san dai cewa \u0257aya daga cikin abubuwan da bai ji da\u0257in su ba shi ne koma-bayan da jaridar New Nigerian ta samu a matsayin babbar jarida daga Arewa. A rubutun ta\u2019aziyya da Malam Mohammed Haruna ya yi a Daily Trust ta ran Larabar makon jiya, ya yi nuni da cewa rugujewar \u0199imar jaridar da koma-bayan ta ya fara ne daga lokacin da Malam Turi ya bar aiki a kamfanin, domin shugabannin kamfanin da su ka zo bayan sa sun sauya turbar da wa\u0257anda su ka kafa kamfanin su ka \u0257ora kamfanin a kai. Ni ma na yarda haka ne. Manufar littafin da Malam Turi ya rubuta na tarihin jaridar, mai suna &#8216;Courage and Conviction&#8217;, ita ce a isar da wannan sa\u0199on ta hanyar bayar da cikakken tarihin jaridar a cikin shekarun ta ashirin na farko inda ta cimma gagarumar nasara. Ka dubi dai jaridar da ke buga kwafe 250,000 a kullum lokacin da ta ke tashe, sai da ta koma ta na buga kwafe 2,000 a wani lokaci. Duk da yake an sha yin ho\u0253\u0253asan dawo da martabar jaridar a baya, abin ya \u0199azanta a cikin shekaru kamar goma da su ka gabata. A gaskiya, babbar karramawar da za a yi wa Malam Turi (Allah Ya ji\u0199an sa) har ma da mutane irin sa da su ka yi aiki tu\u0199uru don gina New Nigerian, ita ce a yi dukkan abin da ya dace a yi don dawo da \u0199arfin jaridar kamar yadda ya ke a da.<\/p>\n<p>\u2014\u2013<\/p>\n<p>An buga wannan ma\u0199alar a LEADERSHIP HAUSA ta ran 1 ga Oktoba, 2010<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4291\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4291\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ranar 17 ga Satumba, 2010, Allah ya \u0257auki ran Malam Turi Muhammadu, a Kaduna. Shekarun sa 70 a duniya. Kafin rasuwar tasa, ya ta\u0253a ri\u0199e mu\u0199amin editan jaridar New Nigerian, sannan daga bisani ya zama manajan daraktan kamfanin da ke buga jaridar. Malam Turi fitaccen \u0257an jarida ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawa [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4291\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4291\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4292,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4291","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":62,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026 - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026 - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A ranar 17 ga Satumba, 2010, Allah ya \u0257auki ran Malam Turi Muhammadu, a Kaduna. Shekarun sa 70 a duniya. Kafin rasuwar tasa, ya ta\u0253a ri\u0199e mu\u0199amin editan jaridar New Nigerian, sannan daga bisani ya zama manajan daraktan kamfanin da ke buga jaridar. Malam Turi fitaccen \u0257an jarida ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawa [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2010-10-05T10:40:43+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg?fit=211%2C280&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"211\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"280\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026\",\"datePublished\":\"2010-10-05T10:40:43+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291\"},\"wordCount\":1688,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/turi-muhammadu-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291\",\"name\":\"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026 - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/turi-muhammadu-1.jpg\",\"datePublished\":\"2010-10-05T10:40:43+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/turi-muhammadu-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/turi-muhammadu-1.jpg\",\"width\":211,\"height\":280,\"caption\":\"Malam Turi Muhammadu\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4291#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026 - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026 - Ibrahim Sheme","og_description":"A ranar 17 ga Satumba, 2010, Allah ya \u0257auki ran Malam Turi Muhammadu, a Kaduna. Shekarun sa 70 a duniya. Kafin rasuwar tasa, ya ta\u0253a ri\u0199e mu\u0199amin editan jaridar New Nigerian, sannan daga bisani ya zama manajan daraktan kamfanin da ke buga jaridar. Malam Turi fitaccen \u0257an jarida ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawa [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2010-10-05T10:40:43+00:00","og_image":[{"width":211,"height":280,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg?fit=211%2C280&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026","datePublished":"2010-10-05T10:40:43+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291"},"wordCount":1688,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291","name":"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026 - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg","datePublished":"2010-10-05T10:40:43+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg","width":211,"height":280,"caption":"Malam Turi Muhammadu"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4291#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Malam Turi: Ba Rabo Da Gwani Ba\u2026"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/turi-muhammadu-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4291","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4291"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4291\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4292"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4291"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4291"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4291"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}