{"id":4289,"date":"2010-09-23T10:35:05","date_gmt":"2010-09-23T10:35:05","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4289"},"modified":"2010-09-23T10:35:05","modified_gmt":"2010-09-23T10:35:05","slug":"matasa-da-tashin-tashina","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289","title":{"rendered":"Matasa Da Tashin-Tashina"},"content":{"rendered":"<p>Ba tun yau ba aka san cewa \u0257aya daga cikin manyan matsalolin Nijeriya shi ne rashin aikin yi, sannan wannan matsalar ta na ba da gudunmawa ga tashe-tashen hankula na \u0199abilanci da na addini a cikin \u2019yan shekarun nan. A makon jiya, wani muhimmin rahoto da cibiyar ya\u0257a al\u2019adun \u0199asar Birtaniya, wato British Council, ta \u0257auki nauyin yin sa ya yi garga\u0257in cewa idan har Nijeriya ba ta samar da guraben aikin yi guda miliyan 25 a cikin shekaru 10 masu zuwa ba, to, tashe-tashen hankula da matasan mu ke yi za su \u0199aru matu\u0199a. Idan har mu ka yi kunnen uwar shegu da wannan rahoton, kaicon mu!<\/p>\n<p>Wasu manyan \u2019yan Nijeriya wa\u0257anda su ka ha\u0257a da tsofaffin ministoci da kuma masanan harkokin tattalin arzikin \u0199asa, irin su Ngozi Okonjo-Iweala, Frank Nweke Jr., Lami\u0257o Ado Bayero, Donald Duke, Pat Utomi da Maryam Uwais, su ne su ka yi bincike su ka rubuta rahoton mai suna \u201cThe Next Generation Nigeria\u201d. Haka kuma wasu masanan daga Amerika da Ingila sun taka rawar gani wajen ha\u0257a rahoton. A ranar Larabar makon jiya aka yi taron \u0199addamar da shi a Abuja. Tsohon Ministan Ya\u0257a Labarai, Mista Frank Nweke, Jnr., shi ne ya karanta gundarin abin da rahoton ya \u0199unsa a gaban jama\u2019a. Ya ce rahoton ya gano cewa Nijeriya ta na fuskantar \u201cbarazanar yawan jama\u2019a\u201d saboda rashin aikin yi tsakanin matasa. Rahoton ya \u0199ididdige cewa yawan mutanen Nijeriya zai \u0199aru daga mutum miliyan 150 da ke akwai yanzu, da \u0199arin mutum miliyan 63 ya zuwa shekarar 2050. Hakan zai sa Nijeriya ta kasance ta biyar a cikin \u0199asashen da su ka fi yawan jama\u2019a a duniya. Rahoton ya hango cewa kashi 40 cikin \u0257ari na \u2019yan Nijeriya matasa ne, wanda hakan zai sa a samu \u0199arin \u0257imbin masu bu\u0199atar aikin yi a nan gaba.<\/p>\n<p>Wannan rahoto dai ya nuna cewa yawan mutanen Nijeriya ya ninka a cikin shekaru ashirin da su ka gabata, wanda ya saka \u0199asar cikin mayuwacin hali idan har ba a dage wajen gyaran koma\u0257ar tattalin arziki ba. Ya ce, \u201cSamun \u0257imbin matasa marasa aikin yi ya kan jefa al\u2019umma cikin halin \u0199a\u0199a-ni-ka-yi, ta hanyar yawaitar aikata laifuffuka da kuma samar da yanayin da zai jawo tashin-tashina. Duk \u0199asar da ba ta shirya wa yin amfani da albarkar yawaitar matasan ta ba, za ta samu kan ta cikin fitinar yawan jama\u2019a, maimakon ta ci moriyar hakan.\u201d<\/p>\n<p>Idan mun lura, wannan rahoton bai tsaya kai da fata kan cewa bala\u2019i ka\u0257ai ya hango ba, a\u2019a, ya ba mu shawarwari kan hanyoyin da za mu bi don kauce wa bala\u2019i. Ya yi la\u2019akalari da cewa za a iya amfani da matasa don gina \u0199asa, tare da nuna cewa matasan mu su ne albarka mafi girma da Nijeriya ta ke da ita, ba man fetur ba. Ya ce: \u201cMatasa su ne albarka mafi girma a \u0199asa, ba fetur ba, a cikin \u0199arni na 21. Idan \u0199asar ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen tattalin arziki kamar yadda ta ke yi a yanzu, ta inganta harkar ilimi, ta samar da ayyukan yi, to, kowane \u0257an Nijeriya zai iya samun ninkin arzikin sa har sau uku kafin shekara ta 2030, sannan sama da mutum miliyan 30 za su fice daga \u0199angin fatara.\u201d<\/p>\n<p>Rahoton ya ba da shawarar cewa tilas ne \u0199asar mu ta fito da tsari mai kyau don samar da aikin yi a shekaru masu zuwa. Ya ce: \u201cIdan Nijeriya ta kasa yin tsari don inganta rayuwar matasa a nan gaba, to za ta fuskaci manyan matsaloli da za su \u0253ullo a dalilin yawaitar matasa masu jin haushin cewa ba su da aikin yi. Saboda haka za su iya zama wani abu da zai kawo barazana ga zaman lumana a \u0199asar.\u201d<\/p>\n<p>A gaskiya, rashin aikin yi a tsakanin matasan \u0199asar nan ya zama abin ban-tsoro a yau. Gwamnati ta ce wai kashi 20 cikin \u0257ari na matasan ne ba su da aikin yi, amma duk mai hankali ya san cewa zai kai kashi har 60 cikin \u0257ari, musamman da yake yawancin masana\u2019antu sun ruguje, sannan bankuna su na ta korar ma\u2019aikata. Na kan ji zafi matu\u0199a idan yaran da su ka gama jami\u2019a ko wata babbar kwaleji su ka same ni don in taimaka in sama masu aiki. Babu aikin. A shekarun baya, lokacin duniya ta na kwance lafiya, ma\u2019aikatu neman matasa su ke yi don su ba su aiki. Musamman za ka ga kamfanoni su na zuwa jami\u2019o\u2019i da kwalejoji, su na \u0257aukar sunayen \u0257aliban da su ka kusa fita daga makaranta domin su ba su aiki da zarar sun \u0199are. Hakan ta faru kafin zuwan tsarin tsuke bakin aljihu (SAP), da cin hanci da rashawa, da kuma dur\u0199ushewar tattalin arziki na duniya. Duniya juyi-juyi, kwa\u0257o ya fa\u0257a cikin ruwan zafi.<\/p>\n<p>Babban ofishin \u0198ididdiga na \u0198asa (Federal Office of Statistics, FOS) ya bayyana cewa yawancin marasa aikin yi, a biranen mu su ke. Sannan wani rahoto da Bankin Duniya ya wallafa ya ce yawancin matasa marasa aikin yi wa\u0257anda su ka gama makarantar sakandare ne. Ga kuma \u0257imbin jama\u2019a a karkara su na zaman warabbuka, ba abin yi sai kame-kame da kunge-kunge.<\/p>\n<p>A gani na, ba sai an bi tsarin \u0199ayyade iyali ba don kurum a rage yawan \u2019yan Nijeriya, kamar yadda rahoton British Council ya ce a yi. Dubi \u0199asar Chaina mana, wadda ta fi kowace \u0199asa yawan jama\u2019a. Chaina, mai mutum biliyan 1.3, har ta zarce Japan wajen \u0199arfin tattalin arziki, ta zama ta biyu a duniya (bayan Amerika). Ita ma Indiya, mafi yawan jama\u2019a ta biyu a duniya, haka ne. Me ya sa? Dalili shi ne su na da shugabanni masu son ci-gaban jama\u2019ar su, ba wawura ba ko bin tsarin \u0199asashen Turawa.<\/p>\n<p>Ai jama\u2019a albarka ce. Kada mu ji tsoro don jama\u2019ar mu na \u0199ara yawa. Dalili shi ne mu na da albarkatun \u0199asa masu tarin yawa da za a iya amfani da su wajen ciyar da \u0199asar mu gaba. Duk inda ka waiga a Nijeriya, ba abin da idon ka zai gane maka sai albarkatu iri-iri. Tun daga sararin samaniya mai cike da hasken rana, har zuwa \u0199asar noma mai dausayi wadda ke \u0199unshe da ma\u2019adinai, ga dabbobi, suke-shuke, mai, da sauran su, sannan ga jama\u2019a masu ji da lafiyar jiki, masu ilimi da son aiki tu\u0199uru. To, amma matsalar mu ita ce ba a yin amfani da wa\u0257annan albarkatun ta hanyar da ta dace. Ana banzatar da su ne. Mu na da yawaitar \u0253arayi masu sace albarkatun don kurum Allah Ya \u0257ora su a kai, sannan su na amfani da jama\u2019ar \u2013 musamman matasa \u2013 wajen ayyukan assha, irin su karuwanci da kuma rikicin addini ko \u0199abilanci.<\/p>\n<p>Shugabannin mu sun yi watsi da aikin noma, sun maida hankali ga man fetur, wanda ya sa sun kasa fahimtar alfanun da ke \u0199unshe jingim cikin sauran albarkatun da Allah Ya ba \u0199asar nan. Ba su ba harkar ilimi muhimmanci, wadda ita ce \u0199ashin bayan gina \u0199asa mai nagarta. Muguwar fa\u0257uwar da \u2019yan makaranta su ka yi a jarabawar WAEC kwanan nan hujja ce da ke nuna cewa shugabannin mu ba su tunanin abin da ya dace da ci-gaban \u0199asa. Hujja ce da ke nuna irin ha\u0257arin da mu ke fuskanta \u2013 wato ta al\u2019umma marasa ilimi ko makamar aiki, wadda za ta iya jawo rigingimu a \u0199asa a kowane lokaci.<\/p>\n<p>Rahoton na British Council ya kuma gano wani abu da ya kamata shugabannin Arewa su sani: wato duk da yake an san cewa har yanzu jahilci \u0199aruwa ya ke yi, tazarar da ke tsakanin sashin Kudu da na Arewa na \u0199asar nan ya na \u0199ara \u0199aruwa ne. \u2019Ya\u2019yan Kudu sun fi samun shiga makaranta fiye da na Arewa.<\/p>\n<p>Barazanar cewa rigima ta na nan tafe sai \u0199aruwa ta ke yi a yayin da za\u0253en 2011 ya ke \u0199aratowa. Rashin aikin yi ya \u0199aru saboda dur\u0199ushewar da masana\u2019antu su ka yi a sanadiyyar rashin wutar lantarki. Hakan ya sa a yau akwai bataliyoyin matasa marasa aikin yi, su na jiran kawai a \u0257auke su aikin tada husuma. Masu \u0257aukar su aikin rigimar ba wasu ba ne illa shugabannin mu wa\u0257anda su ka wawuri dukiyar jama\u2019a kuma za su yi amfani da ita don za\u0253en ta hanyar \u0199arfi.<\/p>\n<p>Abin ban-haushi, maimakon ka ji ana maganar samun \u2019yan takarar da za su magance manyan matsalolin \u0199asar nan irin su rashin aikin yi, an koma kawai ana cacar baki kan tsarin kar\u0253a-kar\u0253a na PDP. Manufar wannan tsari fa kawai wanene zai zama shugaban \u0199asa, kuma daga ina ya fito, ba wanene zai yi \u0199o\u0199arin magance \u0257imbin matsalolin \u0199asar nan ba.<\/p>\n<p>\u2014<\/p>\n<p>An buga a jaridar LEADERSHIP HAUSA<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4289\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4289\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ba tun yau ba aka san cewa \u0257aya daga cikin manyan matsalolin Nijeriya shi ne rashin aikin yi, sannan wannan matsalar ta na ba da gudunmawa ga tashe-tashen hankula na \u0199abilanci da na addini a cikin \u2019yan shekarun nan. A makon jiya, wani muhimmin rahoto da cibiyar ya\u0257a al\u2019adun \u0199asar Birtaniya, wato British Council, ta [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4289\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4289\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4289","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":13,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Matasa Da Tashin-Tashina - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Matasa Da Tashin-Tashina - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ba tun yau ba aka san cewa \u0257aya daga cikin manyan matsalolin Nijeriya shi ne rashin aikin yi, sannan wannan matsalar ta na ba da gudunmawa ga tashe-tashen hankula na \u0199abilanci da na addini a cikin \u2019yan shekarun nan. A makon jiya, wani muhimmin rahoto da cibiyar ya\u0257a al\u2019adun \u0199asar Birtaniya, wato British Council, ta [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2010-09-23T10:35:05+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Matasa Da Tashin-Tashina\",\"datePublished\":\"2010-09-23T10:35:05+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289\"},\"wordCount\":1466,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289\",\"name\":\"Matasa Da Tashin-Tashina - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2010-09-23T10:35:05+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4289#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Matasa Da Tashin-Tashina\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Matasa Da Tashin-Tashina - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Matasa Da Tashin-Tashina - Ibrahim Sheme","og_description":"Ba tun yau ba aka san cewa \u0257aya daga cikin manyan matsalolin Nijeriya shi ne rashin aikin yi, sannan wannan matsalar ta na ba da gudunmawa ga tashe-tashen hankula na \u0199abilanci da na addini a cikin \u2019yan shekarun nan. A makon jiya, wani muhimmin rahoto da cibiyar ya\u0257a al\u2019adun \u0199asar Birtaniya, wato British Council, ta [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2010-09-23T10:35:05+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Matasa Da Tashin-Tashina","datePublished":"2010-09-23T10:35:05+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289"},"wordCount":1466,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289","name":"Matasa Da Tashin-Tashina - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2010-09-23T10:35:05+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4289#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Matasa Da Tashin-Tashina"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4289","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4289"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4289\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4289"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4289"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4289"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}