{"id":4287,"date":"2011-02-24T10:26:47","date_gmt":"2011-02-24T10:26:47","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4287"},"modified":"2011-02-24T10:26:47","modified_gmt":"2011-02-24T10:26:47","slug":"maanar-%c6%99arfin-ikon-jamaa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287","title":{"rendered":"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a"},"content":{"rendered":"<p>DA \u0199arfe 6:43 na yamma a birnin Al\u0199ahira a ranar Juma\u2019a ta makon jiya, wani jagoran masu zanga-zangar \u0199in amincewa da mulkin Shugaba Hosni Mubarak mai suna Wael Ghonim ya tura sa\u0199o a dandalin Twitter da ke intanet, ya na fa\u0257in: \u201cMu na taya ki murna, Masar, babban mai laifin nan ya arce daga fadar sa.\u201d Ya na nufin Mubarak wani babban \u0253arawo ne ko mai kisan kai da sauran manyan laifuffuka wanda mulkin sa ya zo \u0199arshe har ya gudu daga fadar shugaban \u0199asa. Hakan ya biyo bayan tumbu\u0257in da al\u2019ummar \u0199asar su ka shafe kwana 18 su na yi, inda a \u0199arshe, ran Juma\u2019a da ta wuce, zamanin Muhammad Hosni Mubarak a karagar Jamhuriyar Larabawa ta Masar ya kawo \u0199arshe. \u0198arfin jama\u2019a ya tabbata. Idan kun tuna, a rubutun da na yi a wannan shafin a makon jiya mai taken, \u201cFir\u2019auna Na \u0198arshe Ya Fa\u0257i!\u201d na bayyana cewa, \u201cTuni muguwar gwamnatin sa ta shiga garari, ta fara tarwatsewa, domin kuwa iyalan sa da manyan jami\u2019an gwamnatin sa tuni su ka fara arar takalmin kare su na arcewa.\u201d<\/p>\n<p>Tarin jama\u2019ar da ta taru a Dandalin Tahrir ta wuce maridan gwamnati su maida ita abar wasa ko su yi mata ri\u0199on sakainar kashi, domin jama\u2019a ce wadda ta san ciwon kan ta kuma ta ke da zummar lallai sai an biya mata bu\u0199atar ta. Yawancin mutanen da ke cikin taron matasa ne wa\u0257anda ba su gama ko ta-ta-ta ba lokacin da Mubarak ya \u0257are karagar mulki a 1981. To amma mutane ne masu ilimi, wayayyu a lamurran duniyar mu ta yau, masana intanet, masu fushi da gur\u0253acewar mulki, wa\u0257anda su ka gaji da salon tafiyar hawainiyar mulki, kuma sun gaji da salon mulkin mutum \u0257aya, sannan su na son canji ko ta halin \u0199a\u0199a. Matasa ne \u2019yan Facebook wa\u0257anda su ka san yadda za su yi amfani da intanet da kuma tashoshin talabijin na satalayit don cimma bu\u0199atun su. Duk wani mai ba\u0199in mulki da ya yi kunnen uwar shegu da irin wa\u0257annan \u2019yan taratsin, to jiki magayi.<\/p>\n<p>Mubarak ya yi duk wasu kame-kame don ya li\u0199e a jikin she\u0199ar sa. Saboda lallai ya san tsiyar wa\u0257annan nau\u2019urorin ya\u0257a labarai da Turawa su ka \u0199ir\u0199ira, ya dakatar da Facebook da gidan talabijin na Aljazeera na wani \u0257an lokaci, amma duk a banza. Babu abin da ya yi masa amfani; misali barazanar da kwamandojin sa na soja su ka yi wa masu zanga-zangar, da soki-burutsun da Mataimakin Shugaban \u0198asa Omar Suleiman (mutumin da shugaban \u2019yan zanga-zanga Mohammed El-Baradei ya kira da \u201cabokin tagwaicin\u201d Mubarak) ya yi masu, da hare-haren da magoya bayan Mubarak su ka kai wa \u2019yan zanga-zangar ko kuma jawaban yaudara da shi Mubarak \u0257in ya yi wa jama\u2019ar \u0199asar a ran 1 da ran 10 ga Fabrairu, inda ya sha alwashin wai zai ci gaba da mulki har na tsawon watanni bakwai masu zuwa. Da alama, bai gane zurfin tsanar da mutane su ka yi wa azzalumar gwamnatin sa ba. Tunda dai duk \u0199asar ta na kuka da shi, sannan dubban mutane sun shiga yajin aiki, inda su ka ja wa \u0199asar birki, don haka bai fi awoyi ka\u0257an \u2013 ba ma kwanaki ba \u2013 kafin \u0199arshen sa ya zo.<\/p>\n<p>Aje aikin da ya yi ran Juma\u2019a wata shaida ce da ke \u0199ara gabbata da \u0199arfin ikon jama\u2019a. Irin haka ta taba faruwa a \u0199asar Filifins a 1986, wanda ya sa aka dinga yin juyin juya hali a \u0199asashe da dama a Gabashin Turai a 1989, ana rusa gwamnatocin gurguzu. Amma an jima irin hakan ba ta faru a nahiyar Larabawa ko ta Afrika ba ma, inda masu mulki ke kallon kan su a matsayin wani abin bauta. To amma yanzu ta fara sauya zani. A yau, Larabawa su na yin tambaya kan halin da rayuwar su ta ke ciki, kuma su na yun\u0199urin kifar da azzaluman shugabannin su. A watan jiya, hakan ta faru a \u0199asar Tunisiya inda jama\u2019a su ka yi zanga-zanga su ka ham\u0253arar da shugaban \u0199asar, har sai da ya tsere zuwa gudun hijira. To amma fa ba wanda ya ta\u0253a tunanin cewa irin wannan za ta iya faruwa a Masar, \u0199asar da ke kan gaba wajen yin ala\u0199a da Yammacin Turai a \u0199asashen Labarawa duka, musamman ma da yake Mubarak ne shugaban \u0199asar, mutumin da ake ganin ya na da \u0199arfin mulki tamkar Fir\u2019auna, wanda sai dai a kwatanta shi da shugaban Ira\u0199i na da, wato marigayi Saddam Hussein. To, duk da haka sai da ta faru ta \u0199are, wai an yi wa mai zani \u0257aya sata! Jama\u2019a sun fa\u0257i abin da su ke so, kuma sun samu.<\/p>\n<p>To amma fa tsugune ba ta \u0199are ba, an sayar da kare an sayi biri. An dai fidda Mubarak, amma kuma ginshi\u0199in gwamnatin sa \u2013 wato sojojin da su ka \u0257aure masa gindi \u2013 har yanzu su na nan daram damdam, sun maida \u0199asar maras dimokira\u0257iyya. Har yanzu za a iya ci gaba da cin mutuncin jama\u2019a. Za a iya mur\u0199ushe duk wani \u0257an adawa.<\/p>\n<p>Na biyu, tsoron da gwamnatocin Yammaci su ke yi na cewa wai babbar jam\u2019iyyar adawar \u0199asar, wato Muslim Brotherhood, za ta hau kujerar mulkin \u0199asar wata babbar barazana ce ga abin muradin jama\u2019ar Masar. Turawa da Yahudawa su na so Masar ta ci gaba da kasancewa a tafin hannun su saboda kawai ta na dakushe abin da su ke kira da tsattsauran ra\u2019ayin addini. A ranar da Mubarak ya fa\u0257i, Firayim Ministar \u0199asar Jamus, wato Angela Markel, ta yi garga\u0257in cewa tilas ne Masar ta ci gaba da yin abokantaka da Isra\u2019ila. Sannan wani fitaccen \u0257an jaridar Amurka wai shi Glenn Beck, wanda tsattsauran ra\u2019ayin sa bai da bambanci da na \u2019yan Al\u0199a\u2019ida wajen tada hankalin jama\u2019a, ya bayyana cewa yun\u0199urin fidda Mubarak wani babban gangamin ha\u0253aka addinin Islama ne na duniya wanda ya taso tun daga nahiyar Asiya har zuwa Ingila. Beck, wanda ke da \u0257imbin mabiya shirin sa na talabijin a Amurka, ya ce, \u201cWannan ba zancen Masar ba ne. Wannan magana ce ta dukkan wani mutum da ya ta\u0253a yin shiri, ko ya ke so, ya canza ainihin rayuwar Turawa da Yahudawa baki \u0257ayan ta.\u201d Manyan masu fa\u0257a a ji a Amurka da dama su na da wannan ra\u2019ayi, ciki kuwa har da babban \u0257an jam\u2019iyyar Republican \u0257in nan mai suna Newt Gingrich, wanda ya furta cewa, \u201c\u2019Yan Muslim Brotherhood su ne manyan ma\u0199iyan rayuwar mu da jinsin mu.\u201d<\/p>\n<p>Shin wai ba abin mamaki ba ne kuwa a ce \u2019yan ra\u2019ayin ri\u0199au na Yammacin Turai ba su son ganin mulkin dimokira\u0257iyya ya wanzu a yankin Gabas ta Tsakiya don kawai irin shugabannin da talakawan Larabawa ke so ba su ba ne Turawa da Yahudawa ke so, sun \u0257auke su masu tsattsauran ra\u2019ayi? \u2019Yan ri\u0199au \u0257in Yammaci sun fi son shugabannin Larabawa masu \u0199aryar son jama\u2019ar su sun ci gaba da mulki, a yayin da su ke kau da kai daga matsalolin rayuwa da su ka addabi jama\u2019ar su saboda kawai shugabannin duk \u2019yan koren su ne.<\/p>\n<p>Sa\u2019annan sai maganar tattalin arziki, wanda Mubarak ya kasa gyarawa domin ya fi maida hankali ga harkar tsaro. Shi kullum abin da ya fi damun sa shi ne dangantakar \u0199asashe, wadda ta ha\u0257a da shiri da Isra\u2019ila da kuma ya\u0199ar \u2019yan kishin Islama. Saboda haka, duk wanda ya zama sabon shugaban \u0199asar Masar ya na da babban aikin gyaran koma\u0257ar tattalin arziki a \u0199asar sa. Bayan haka, wani abu mai muhimmanci kuma shi ne batun yadda za a gina ingantaccen tsarin mulkin dimokira\u0257iyya bisa ginshi\u0199in addinin jama\u2019ar \u0199asa. Hujjoji da dama sun nuna cewa tsarin mulkin dimokira\u0257iyya ya na iya ginuwa a \u0199asashen Musulmi. Shugaban Amurka, Barack Obama, ya fara amincewa da bin hanyar da gwamnatocin Amurka da dama su ka \u0199i aminta da ita, wato bu\u0199atar gina tsarin mulkin dimokira\u0257iyya a \u0199asashen Larabawa.<\/p>\n<p>Idan an bi wannan hanyar bil ha\u0199\u0199i da gaskiya, to za a ga ci-gaba sosai. Domin fa rashin samun za\u0253i, da kuma cusa wa jama\u2019a shugabannin da ba su so ta hangar ci da addini ko batun tsaro ya na taimakawa wajen sa wasu su \u0257auki tsattsauran mataki, wanda ya ha\u0257a da tada bam a cikin jirgin sama ko kuma fasa motar safa da gurnati. Don a cimma nasara, tilas ne Turawa da Yahudawa su \u0199yale Larabawa su za\u0253a wa kan su shugabannin kan su ta hanyar za\u0253e na fisabilillahi. Juyin juya hali da aka yi a Masar ya nuna cewa zamanin da Turawa su ke cusa wa Larabawa shugabanni don biyan bu\u0199atar su ta son rai ya shu\u0257e. A yau, matasa za su ri\u0199a bin bahasi da babbar murya.<\/p>\n<p>Mu ma a nan Afrika ya kamata mu farka daga barci. Don me? Dalili shi ne mu na da masu mulkin mur\u0257iya amma masu kiran kan su da sunan masoya dimokira\u0257iyya. Wasu ma su na ta \u0199ara \u0253ullowa a fagen. Ya kamata matasan Afrika, Ba\u0199ar Fata, su yi koyi da takwarorin su da ke arewacin nahiyar mu; kada a manta, su ma \u2019yan Tunisiya da \u2019yan Masar duk \u2019yan Afrika ne. Ya kamata su farka daga gyangya\u0257i, su yi bin bahasi ga shugabannin su, su bu\u0199aci sauyi a duk inda hakan ya dace.<\/p>\n<p>Ku kuma \u2019yan Masar mu na taya ku murna. Fir\u2019auna ya fa\u0257i.<\/p>\n<p>\u2014<\/p>\n<p>An buga a LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma\u2019a da ta ga bat<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4287\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4287\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>DA \u0199arfe 6:43 na yamma a birnin Al\u0199ahira a ranar Juma\u2019a ta makon jiya, wani jagoran masu zanga-zangar \u0199in amincewa da mulkin Shugaba Hosni Mubarak mai suna Wael Ghonim ya tura sa\u0199o a dandalin Twitter da ke intanet, ya na fa\u0257in: \u201cMu na taya ki murna, Masar, babban mai laifin nan ya arce daga fadar [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4287\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4287\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4286,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[12],"tags":[],"class_list":["post-4287","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-online-musings"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":22,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"DA \u0199arfe 6:43 na yamma a birnin Al\u0199ahira a ranar Juma\u2019a ta makon jiya, wani jagoran masu zanga-zangar \u0199in amincewa da mulkin Shugaba Hosni Mubarak mai suna Wael Ghonim ya tura sa\u0199o a dandalin Twitter da ke intanet, ya na fa\u0257in: \u201cMu na taya ki murna, Masar, babban mai laifin nan ya arce daga fadar [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2011-02-24T10:26:47+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg?fit=1280%2C852&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1280\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"852\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a\",\"datePublished\":\"2011-02-24T10:26:47+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287\"},\"wordCount\":1633,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Online Musings\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287\",\"name\":\"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg\",\"datePublished\":\"2011-02-24T10:26:47+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg\",\"width\":1280,\"height\":852,\"caption\":\"Shugaba Hosni Mubarak a birnin Berlin, cikin Maris 2006. (Hoto daga: Michael Hanschke)\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4287#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a - Ibrahim Sheme","og_description":"DA \u0199arfe 6:43 na yamma a birnin Al\u0199ahira a ranar Juma\u2019a ta makon jiya, wani jagoran masu zanga-zangar \u0199in amincewa da mulkin Shugaba Hosni Mubarak mai suna Wael Ghonim ya tura sa\u0199o a dandalin Twitter da ke intanet, ya na fa\u0257in: \u201cMu na taya ki murna, Masar, babban mai laifin nan ya arce daga fadar [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2011-02-24T10:26:47+00:00","og_image":[{"width":1280,"height":852,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg?fit=1280%2C852&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a","datePublished":"2011-02-24T10:26:47+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287"},"wordCount":1633,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg","articleSection":["Online Musings"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287","name":"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg","datePublished":"2011-02-24T10:26:47+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg","width":1280,"height":852,"caption":"Shugaba Hosni Mubarak a birnin Berlin, cikin Maris 2006. (Hoto daga: Michael Hanschke)"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4287#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Ma\u2019anar \u0198arfin Ikon Jama\u2019a"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0009-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4287","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4287"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4287\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4286"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4287"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4287"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4287"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}