{"id":4283,"date":"2011-01-21T10:17:46","date_gmt":"2011-01-21T10:17:46","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4283"},"modified":"2011-01-21T10:17:46","modified_gmt":"2011-01-21T10:17:46","slug":"hattara-da-ramuka-a-gaba-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283","title":{"rendered":"Hattara Da Ramuka A Gaba!"},"content":{"rendered":"<p>A jiya Alhamis ne \u0257imbin \u2019ya\u2019yan jam\u2019iyyar PDP, musamman dalaget, su ka yi kwamba a Abuja domin gudanar da za\u0253en fitar da gwani na wanda zai yi takarar zama shugaban \u0199asa a \u0199ar\u0199ashin inuwar jam\u2019iyyar su. Tun kafin ranar, dalaget da sauran membobin PDP \u0257in su ka dinga antayowa zuwa cikin babban birnin na tarayya, ta yadda ko ya zuwa ran Talata da wuya mutum ya samu \u0257aki a dukkan otal-otal na garin. Su ma wuraren cin abinci sun cika ma\u0199il da ba\u0199in.<\/p>\n<p>In ba domin batun ya shafi PDP ba ne, to da wata\u0199ila sai mu zuba na mujiya kurum, mu yi kallon bada\u0199alar da ake yi. To amma PDP ta na kurarin cewa ita ce jam\u2019iyyar siyasa da ta fi kowace girma a nahiyar Afrika. Haka kuma ita ce jam\u2019iyyar da ke mulki a Nijeriya. Ta haifar da shugabannin \u0199asar har guda uku daga lokacin da aka fara Jamhuriya ta Hu\u0257u, domin kuwa ita ce aka ce ta lashe za\u0253u\u0253\u0253ukan shugaban \u0199asa da aka yi a cikin 1999 da 2003 da kuma 2007. Sannan ita ce ke da rinjaye a yawancin jihohin tarayyar \u0199asar nan, da kuma Majalisar Tarayya. \u0198ungiyar Gwamnonin Nijeriya yawanci membobin PDP ne su ka cika ta, kuma ta na daga cikin \u0199ungiyoyi masu fa\u0257a a ji a \u0199asar nan. Bugu da \u0199ari, duk wasu tsare-tsare na mulkin \u0199asa wa\u0257anda PDP ta fito da su kuma ta ke aiwatarwa, wa\u0257anda aka \u0257ibiya a kan \u0257imbin ku\u0257a\u0257en shiga da ke zuwa daga safarar man fetur, su na shafar rayuwar jama\u2019ar \u0199asar nan. Saboda haka, ko an \u0199i ko an so, za\u0253en wanda zai tsaya takarar zama shugaban \u0199asa na jam\u2019iyyar ya na da matu\u0199ar tasiri a rayuwar \u2019yan Nijeriya, ya Allah tasirin nan mai kyau ne ko akasin haka. Don haka, tilas ne mu damu kan wannan lamari, domin duk shukar da za a yi a wannan gangami zai iya shafar rayuwar mu kusan ta kowane \u0253angare.<\/p>\n<p>Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan ne karo na farko da shugaba mai ci yanzu, wato Dakta Goodluck Jonathan, ya ke takarar wani mu\u0199ami da sunan sa. A da, shi sifiya-taya ne kurum \u2013 inda a Jihar Bayelsa ya yi mataimakin gwamna, sannan a 2007 ya zama mataimakin shugaban \u0199asa. A yanzu ne ya ke gwajin farin jinin sa a karo na farko. Idan har ya na so ya zama za\u0253a\u0253\u0253en shugaban \u0199asa, to, na farko sai ya tsallake sira\u0257in za\u0253en da aka taru a yi a jiya, 13 ga Janairu. Idan ya ci, sai kuma shallake sira\u0257i na biyu: wato kada abokan hamayyar sa wa\u0257anda sauran jam\u2019iyyu za su tsayar. Duk wa\u0257annan sira\u0257an, ba wasan yara ba ne. Aiki ne wurjanjan. Ko a kogin farko da ya ke \u0199o\u0199arin hayewa yanzu, akwai maridan kadoji a ciki; Jonathan ya na bugawa ne a za\u0253en fidda gwani mafi tsauri a takarar zama shugaban \u0199asa da aka ta\u0253a yi a tarihin siyasar Nijeriya.<\/p>\n<p>Hakan na faruwa ne saboda abin da masu nazarin al\u2019amuran yau da kullum su ke kallo a matsayin da\u0253a wa ciki wu\u0199a da PDP ta yi: wato yarjejeniyar kar\u0253a-kar\u0253ar shugabancin \u0199asa tsakanin arewa da kudu da ta rattaba hannu a kai. Jonathan ya \u0257are kujerar shugaban \u0199asa ne ta hanyar sa\u2019a kurum lokacin da maigidan sa, Shugaba Umaru Musa Yar\u2019Adua, ya kwanta dama. A yarjejeniyar da aka yi, kamata ya yi shugaban \u0199asa da zai maye gurbin Yar\u2019Adua ya fito daga arewa domin kuwa shi Yar\u2019Adua bai kammala wa\u2019adin da ya kamata yankin ya yi ba. To amma shi Jonathan da magoya bayan sa, sun za\u0253i su yi fatali da wannan yarjejeniyar. Su kuwa manyan \u2019yan takarar PDP daga arewa, sai su ka janye, su ka goyi bayan tsohon mataimakin shugaban \u0199asa, Alhaji Atiku Abubakar (Turakin Adamawa), sakamakon yarjejeniyar fidda \u0257an takara \u0199waya \u0257aya na arewa a jam\u2019iyyar da aka yi, kuma akwai yiwuwar shi za su ci gaba da goyon baya a wannan za\u0253en fidda gwanin da kuma bayan za\u0253en.<\/p>\n<p>A yayin da ake cikin haka, sai \u0253angarorin biyu su ka shiga ya\u0199in watsa wa juna \u0199asa a ido. A kullum sai ka ga wanin su ya na yi wa \u0257an\u2019uwan sa \u0253atanci a jarida, da zargi iri-iri na cin hanci da rashawa da kuma ambaton wasu kalamai maras da\u0257i da wani daga cikin su ya ta\u0253a yi a baya. Manufa ita ce a nuna cewa wane bai dace da zama shugaba ba. \u018aaya daga cikin wannan zargin na kwana kwanan nan shi ne inda aka ruwaito Atiku ya na ragargazar jam\u2019iyyar ta PDP, aka ce wai ya yi kalamin ne a cikin watan Nuwamba na shekarar 2006.<\/p>\n<p>Shin Atiku bai da hurumin yin irin wannan maganar a WANCAN lokacin, wanda kowa ya san cewa da gaske ne PDP jam\u2019iyya ce inda ba a bin doka da oda? Kalamin da aka ce Atikun ya yi, wai ya yi shi ne a sashen Hausa na Muryar Amurka inda ya ce PDP \u201cba ta da \u0199a\u2019ida; ba ta bin doka da oda da kuma shugabannin ta.\u201d Amma idan mun duba da kyau, za mu ga cewa duk abin nan da Atiku ya fa\u0257a game da PDP a wancan lokacin, gaskiya ne. Akwai ma mutanen da su ka fa\u0257i abin da ya fi haka. Shahararren marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana jam\u2019iyyar PDP da cewa she\u0199ar ba\u0199a\u0199en macizai ce kawai.<\/p>\n<p>An shafe shekaru PDP ta na cikin rigingimu, ba don kurum \u2019ya\u2019yan ta sun \u0257auke ta a matsayin hanya mafi gajarta wajen ku\u0257ancewa a dare \u0257aya ba, a\u2019a har ma da yadda babu tsarin dimokira\u0257iyya a cikin ta. A PDP, ana cusa wa masu za\u0253e \u0257an takara, a ce shi ake so a za\u0253a ko da kuwa jama\u2019a ba su son shi, kuma lallai ne duk wanda aka tsayar sai ka ji shi ne ya lashe za\u0253en. Sakamakon haka, a yayin da ake ta kiraye-kirayen cewa ya kamata a kimtsa jam\u2019iyyar, sai \u2019ya\u2019yan ta da yawa su ka dinga sauya she\u0199a. Kuma jam\u2019iyyar ta fa\u0257i a sababbin za\u0253u\u0253\u0253uka da aka yi a wasu jihohin. A yau ma da hukumar za\u0253e ta ke ta yayata cewa za ta gudanar da za\u0253e fisabilillahi, ai ga shi nan \u2019yan PDP da dama sun yi hijira zuwa wasu jam\u2019iyyun, inda su ka tsaya takara. Alamun cewa an fara dawowa daga rakiyar jam\u2019iyyar ta bayyana \u0199arara a za\u0253u\u0253\u0253ukan fidda gwani na takarar zuwa Majalisar Tarayya da aka gudanar a \u0199arshen makon jiya, inda sanatoci da \u2019yan Majalisar Wakilai da dama su ka sha kaye a hannun abokan adawar su. To, kallo ma bai \u0199are ba har sai an zo za\u0253e tsakanin jam\u2019iyya da jam\u2019iyya; a nan ne idon wasu \u2019yan takara \u2013 ciki kuwa har da gwamnoni \u2013 zai raina fata. Sai ga shi a yau PDP ta shiga gargada, duk da cika-bakin da shugaban ta na \u0199asa na lokacin, wato Prince Vincent Ogbulafor, ya ta\u0253a yi na cewa sai sun yi mulki har na tsawon shekara 60 ba tsinkewa; yanzu akwai alamun za ta fa\u0257i ba nauyi.<\/p>\n<p>Wannan za\u0253en fidda gwanin da \u2019yan PDP ke yi a Abuja zai iya haifar da alheri ko sharri ga jam\u2019iyyar, har abin ya shafi \u0199asa baki \u0257aya. Akwai \u0257ar-\u0257ar \u0257in da ake yi na abin da zai iya wakana idan har Jonathan ya fa\u0257i a za\u0253en ko idan Atiku ne ya fa\u0257i. Tambayar da ake yi ita ce, shin idan shugaban \u0199asar ya sha \u0199asa, zai koma koyarwar sa a makaranta ne ko kuwa zai samu wata mafaka ne inda zai ri\u0199a cin duniyar sa da tsinke? Ma\u2019ana, zai yarda ya sauka daga karagar mulki kuwa kamar yadda ya ta\u0253a al\u0199awartawa? Ko kuwa zai yi irin na Shugaba Laurent Gbagbo na \u0199asar Cote d\u2019Ivoire ne, ya ce atafau ba zai sauka ba? Sa\u2019annan ko kuwa shi Atiku, angulu za ta koma gidan ta na tsamiya ne ko kuma zai sake dabarar da ake ra\u0257e-ra\u0257in zai bi, idan har aka tandara shi da \u0199asa? Ku sani cewa ita wannan sabuwar dabarar, ba fa wadda \u2019yan \u0253angaren Jonathan ke ya\u0257awa ba ce, cewa wai Atiku ya ce zai janyo fitina idan ba a za\u0253e shi ba. Dabarar dai ita ce wata\u0199ila shi da magoya bayan sa su fice daga PDP su koma wata jam\u2019iyyar su mara wa \u0257an takarar ta baya, misali jam\u2019iyyar CPC ta su Janar Muhammadu Buhari, ba don komai ba sai don a tabbatar da cewa an ta\u0257iye Jonathan.<\/p>\n<p>Shahararren marubucin nan \u0257an \u0199asar Ingila wanda ya rasu \u0257aruruwan shekaru da su ka gabata, wato William Shakespeare, ya rubuta a littafin sa na wasan kwaikwayo mai suna &#8216;Julius Caesar&#8217; cewa a tabbatar an yi kaffa-kaffa da ranar 13 ga Maris ko ranar 13 ga Janairu, domin kuwa wani mugun abu na iya faruwa a ranar ko a sakamakon ta. Sai ga shi \u2019yan PDP sun taru domin yin za\u0253e a ran 13 ga Janairu. To, mu dai addu\u2019ar mu ita ce ko ma wace irin waina aka toya a jiya Alhamis, Allah ya sa ta alheri ce ga Nijeriya. Manyan kurayen da ke mulki a kan dokin PDP sun da\u0257e su na yi wa \u2019yan Nijeriya hawan \u0199awara, bayan kuwa a baki su na i\u0199irarin wai sun zo ne su ceci talaka daga fatara da yunwa. Sai ga shi fatara da yunwar ba su ragu ba. Ci-gaban mai ginar rijiya kawai ake yi. Nijeriya ta ci gaba da kasancewa \u0199asa mai koma-baya ta fuskar tattalin arziki, sannan ta na daga cikin jerin \u0199asashe wa\u0257anda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu. Ya Allah, mu na ro\u0199on Ka da kada mu fa\u0257a cikin ramukan da mu ke hangowa a gaban mu. Amin summa amin.<\/p>\n<p>\u2014<\/p>\n<p>An buga a LEADERSHIP HAUSA ta makon jiya<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4283\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4283\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A jiya Alhamis ne \u0257imbin \u2019ya\u2019yan jam\u2019iyyar PDP, musamman dalaget, su ka yi kwamba a Abuja domin gudanar da za\u0253en fitar da gwani na wanda zai yi takarar zama shugaban \u0199asa a \u0199ar\u0199ashin inuwar jam\u2019iyyar su. Tun kafin ranar, dalaget da sauran membobin PDP \u0257in su ka dinga antayowa zuwa cikin babban birnin na tarayya, [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4283\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4283\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4282,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4283","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":18,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Hattara Da Ramuka A Gaba! - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Hattara Da Ramuka A Gaba! - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A jiya Alhamis ne \u0257imbin \u2019ya\u2019yan jam\u2019iyyar PDP, musamman dalaget, su ka yi kwamba a Abuja domin gudanar da za\u0253en fitar da gwani na wanda zai yi takarar zama shugaban \u0199asa a \u0199ar\u0199ashin inuwar jam\u2019iyyar su. Tun kafin ranar, dalaget da sauran membobin PDP \u0257in su ka dinga antayowa zuwa cikin babban birnin na tarayya, [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2011-01-21T10:17:46+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg?fit=480%2C278&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"480\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"278\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Hattara Da Ramuka A Gaba!\",\"datePublished\":\"2011-01-21T10:17:46+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283\"},\"wordCount\":1706,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283\",\"name\":\"Hattara Da Ramuka A Gaba! - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg\",\"datePublished\":\"2011-01-21T10:17:46+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg\",\"width\":480,\"height\":278,\"caption\":\"Cif Jojin Nijeriya, Aloysius Katsina-Alu, ya na rantsar da Dakta Goodluck Jonathan a matsayin shugaban \u0199asa bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ... a watan Mayu, 2010\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4283#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Hattara Da Ramuka A Gaba!\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Hattara Da Ramuka A Gaba! - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Hattara Da Ramuka A Gaba! - Ibrahim Sheme","og_description":"A jiya Alhamis ne \u0257imbin \u2019ya\u2019yan jam\u2019iyyar PDP, musamman dalaget, su ka yi kwamba a Abuja domin gudanar da za\u0253en fitar da gwani na wanda zai yi takarar zama shugaban \u0199asa a \u0199ar\u0199ashin inuwar jam\u2019iyyar su. Tun kafin ranar, dalaget da sauran membobin PDP \u0257in su ka dinga antayowa zuwa cikin babban birnin na tarayya, [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2011-01-21T10:17:46+00:00","og_image":[{"width":480,"height":278,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg?fit=480%2C278&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Hattara Da Ramuka A Gaba!","datePublished":"2011-01-21T10:17:46+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283"},"wordCount":1706,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283","name":"Hattara Da Ramuka A Gaba! - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg","datePublished":"2011-01-21T10:17:46+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg","width":480,"height":278,"caption":"Cif Jojin Nijeriya, Aloysius Katsina-Alu, ya na rantsar da Dakta Goodluck Jonathan a matsayin shugaban \u0199asa bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ... a watan Mayu, 2010"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4283#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Hattara Da Ramuka A Gaba!"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0007-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4283","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4283"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4283\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4282"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4283"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4283"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4283"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}