{"id":4280,"date":"2010-12-08T09:11:24","date_gmt":"2010-12-08T09:11:24","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4280"},"modified":"2010-12-08T09:11:24","modified_gmt":"2010-12-08T09:11:24","slug":"tsugunne-ba-ta-%c6%99are-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280","title":{"rendered":"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba"},"content":{"rendered":"<p>Akwai alamun cewa sau\u0199i ya fara zuwa masana\u2019antar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, domin kuwa mako uku da su ka wuce ne Shugaban \u0198asa Goodluck Jonathan ya yi wani ho\u0253\u0253asa na kyautatawa ga masu aikin fasaha da basira na \u0199asar nan. Ku\u0257i ne zunzurutu wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 200 ya bayyana bayarwa ga masu sana\u2019ar nisha\u0257antarwa a matsayin rance don ha\u0253aka sana\u2019ar su. A ku\u0257in Nijeriya, sun kama kimanin naira biliyan 30.<\/p>\n<p>Shugaban \u0199asar ya fa\u0257i haka ne a Legas, a wurin bikin cikar shahararren kamfanin nan masu gidajen silima da shirya gasar sarauniyar kyau mai suna Silverbird Group shekara 30 da kafawa. Mamallakin kamfanin, wato tsohon Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Mista Ben Murray-Bruce, shi ne ya ro\u0199i shugaban da ya yi wani abu don karrama masana\u2019antar, wadda ta \u0199unshi masu shirya fim da kuma mawa\u0199a. Jonathan, wanda ya halarci taron da kan sa, ya ce wannan jari da gwamnati ta zuba an yi shi ne \u201cba don komai ba sai don a mara wa masu sana\u2019ar fasaha baya da kuma ha\u0253aka masana\u2019antar mu ta nisha\u0257antarwa.\u201d<\/p>\n<p>Mutane da yawa da ke da ruwa da tsaki a masana\u2019antar sun yi murna da wannan ku\u0257in, su na ganin su a matsayin agajin da ya zo a daidai lokacin da ake bu\u0199atar sa, wato a daidai lokacin da ruwa ya kusa \u0199are wa \u0257an kada. Su na ganin sa a matsayin wata babbar karramawa da amintaka ga gudunmawar da wa\u0257annan \u0257imbin masu basirar su ka bayar wajen sa a \u0199ara sanin Nijeriya a fagen ayyukan nisha\u0257i, wato fim da wa\u0199a.<\/p>\n<p>Nollywood, wadda masana\u2019anta ce da ke bun\u0199asa a ko yaushe, ta na tafiya kafa\u0257a-da-kafa\u0257a da masana\u2019antar da ta girme ta a fagen, wato ta ki\u0257a da wa\u0199a. Duk an san su a duniya. A wani rahoto da hukumar UNESCO ta buga a cikin watan Mayu 2009, an bayyana cewa masana\u2019antar Nollywood ce ta uku a duniya wajen fito da yawan finafinai, wato ta na bin masana\u2019antar Hollywood ta \u0199asashen Turawa da kuma Bollywood ta \u0199asar Indiya. An \u0199iyasta cewa darajar Nollywood ta fuskar ku\u0257i ta kai kimanin dala miliyan 250, kuma akwai mutum a\u0199alla miliyan \u0257aya da ke aiki a masana\u2019antar. Wannan masana\u2019anta ta haifar da \u2019yan wasa wa\u0257anda sunan su ya zama ruwan dare a cikin \u0199asar nan da \u0199asashen waje. Sunaye irin su Genevieve Nnaji, Omotola Jalade-Ekeinde, Ramsey Nouah, Kate Henshaw-Nuttal, Pete Edochie, Ali Nuhu, Segun Arinze, Funke Akindele, da sauran su, sanannu ne. Akwai kuma irin wa\u0257annan sunayen a fagen wa\u0199a. A dalilin haka, akwai manazarta da dama da ke tururuwa daga \u0199asashen duniya su na zuwa nan domin yin nazarin irin tashin gwauron zabon da wannan masana\u2019anta ke yi. Abu sai ka ce tsafi! A yau \u0257in nan akwai tashoshin talabijin na satalayit da dama da ke nuna finafinan Nollywood dare da rana, ciki kuwa har da shahararriyar tashar Africa Magic, kwatankwacin yadda tashar Fox Movies ke nuna finafinan Hollywood da kuma yadda tashoshin B4U da Zee Aflam ke nuna na Indiya. Wa\u0257annan mutane, mazan su da matan su, wa\u0257anda yawanci matasa ne, su na rayuwa cikin jin da\u0257i a matsayin attajirai, a cikin aikin da su ka \u0199ir\u0199ira da kan su, ba tare da sa hannun hukuma ba.<\/p>\n<p>To amma kuma akwai mutanen da ke kallon wannan gara\u0253asa da Jonathan ya yi ga \u2019yan fim da mawa\u0199a a matsayin wani abu bambarakwai. Su na ganin cewa ya yi abin ne da ka kawai, ba tare da ya numfasa ya yi tunani ba, don kawai Mista Murray-Bruce ya ro\u0199e shi da ya yi masu ko ma menene don nuna kulawa. Tun daga lokacin da aka bayyana gara\u0253asar, na ji \u2018yan fim da mawa\u0199a da dama su na yin wasu tambayoyi a kan ta: Shin wannan kyautar yaudara ce ko kuwa? Shin siyasa ce? Shin Jonathan ya na \u0199o\u0199arin samun goyon bayan masu sana\u2019ar nisha\u0257antarwa a daidai lokacin da \u2019yan adawa ke girgiza kujerar sa? Shin kishin \u0199asa ne ya sa ya ba da wannan babbar kyautar? Ko kuwa ma gwamnati ta na so ta yi wa \u2019yan fim da mawa\u0199a \u0199ofar raggo ne, wato ta biyo ta bayan fage domin ta mamaye harkar saboda gudun irin sa\u0199wannin da ake iya jefawa a cikin finafinai da wa\u0199o\u0199i?<\/p>\n<p>Bayan haka, wa zai kar\u0253o ku\u0257in daga hannun gwamnati a madadin \u2019yan fim da mawa\u0199an, wa\u0257anda ba su da wasu tsayayyun shugabanni da kowa da kowa ya yarda da su? A yanzu dai, ba a ma san yadda za a raba ku\u0257in ba. Shugaban \u0199asa dai ya ce gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) tare da ministan ku\u0257i su ne za su je su fito da hanyar da za a bi a fito da ku\u0257in da kuma yadda za a yi da su. Jonathan, a jawabin sa, ya ambaci kalmar Nollywood ne a matsayin masana\u2019antar finafinan Nijeriya, to amma don Allah ainihi su wanene Nollywood \u0257in? Da yawa in an ce Nollywood, to ana nufin \u2019yan fim na Kudu kenan, wa\u0257anda ke zaune a Legas da Anacha. To su kuma \u2019yan fim na Hausa fa da ke Arewa, wa\u0257anda sunan tasu masana\u2019antar Kannywood? Sannan kuma ina sauran Wood Wood da ke akwai \u2013 misali masana\u2019antar finafinai ta Nupawa, wadda \u0199arama ce kuma ba ta kallon kan ta a matsayin wani yanki na Kannywood, da sauran wuraren da ake shirya fim cikin harsunan mu na gado? Su yaya za a yi da su? Bugu da \u0199ari, me ake nufi idan an ce maka\u0257an Nijeriya? Shin sun ha\u0257a da masu wa\u0199o\u0199i da harsunan gargajiya, irin su Nasiru Garba Supa na Kano da Musa \u018aanbade na Kaduna, ko kuma ana nufin mawa\u0199a na zamani masu wa\u0199o\u0199in Naija irin su Dapo Oyebanjo (D\u2019banj), Abolere Akande (9ice), Innocent Idibia (Tuface), 2-Effects da Sound Sultan? Sannan ina za a saka su Aminu Ala, Fati Nijar, Maryam A. Baba da ire-iren su? A gaskiya, akwai bu\u0199atar a fito a yi wa jama\u2019a bayani, kuma a fito da hanyoyin da za a bi wa\u0257annan ku\u0257in su kai ga \u2019yan fim da mawa\u0199a. Idan har ba a bi a sannu ba, to wannan gara\u0253asa ta gwamnati za ta haifar da babban rikicin shugabanci a industiri, ta jawo rarrabuwar kai tsakanin masu fasaha a \u0253angarori daban-daban.<\/p>\n<p>Ni a nawa ganin, har yanzu tsugunne ba ta \u0199are ba ga masu shirya finafinai da kuma buga wa\u0199o\u0199i a Nijeriya. Industiri ba ta bu\u0199atar wa\u0257annan ku\u0257in. Dalili: an yanke shawarar ba da su ne kurum a cikin irin tunanin gwamnati da ya da\u0257e ya na addabar \u0199asar nan, wato inda za ka ga an watsa ku\u0257i ga matsala a matsayin magani maimakon a gano dalilin faruwar cutar. Abin da masana\u2019antar nisha\u0257antarwa ke bu\u0199ata shi ne a samar da kyakkyawan sararin da mutum zai yi sana\u2019a har ya ci riba. Mu tuna, wasu \u2019yan kasuwa masu tarar aradu don fa\u0257in kai ne su ka haifar da industirin Nollywood da rana tsaka kimanin shekara 18 da ta gabata lokacin da su ka fitar da fim mai suna &#8216;Living in Bondage&#8217;, kuma tun daga lokacin ta ke ta \u0199ara bun\u0199asa ba tare da jarin gwamnati ba. Na san cewa masana\u2019antar ta na fama da manyan matsaloli. Na farko, matsalar da ke damun Nijeriya ma ita ke damun ta, domin abin da ya ci Doma ba ya barin Awai. Matsalolin sun ha\u0257a da satar basira da wasu \u0253arayin zaune ke tafkawa, ga rashin tsaro da kuma ta\u0253ar\u0253arewar tattalin arzikin \u0199asar nan. \u018aaya daga cikin manyan matsalolin ita ce satar basira, inda wani zaunannen \u0253arawo zai \u0257auki kayan ka ya gurza ya ri\u0199a sayarwa, kai kuwa ko oho. Rashin \u0199arfin doka da oda ya sa masu aikin basira sun kasa cin moriyar shukar su. \u0181arayin zaune sun yi masu talala. Ya kamata a fitar da su daga wannan \u0199angin, su samu sa\u2019ida.<\/p>\n<p>Lokacin da hukumar UNESCO ta ce Nollywood ce ta uku a duniya, ta ba ta wannan matsayin ne a kan yawan finafinan da ake shiryawa kawai, ba wai saboda \u0199arfin arziki ko kuma ingancin finafinan ba. Su finafinan mu na Nijeriya, ana shirya su ne bisa ku\u0257i \u0199alilan, tare da yin amfani da kayan aiki masu araha. Yawanci babu ilimin abin domin su masu ruwa da tsakin ba wani horo su ka samu a makaranta ba; duk a lokeshin ake koyon komai. Shi ya sa za ka ga a finafinan ana nuno abu a duk yadda aka ga dama. Idan ka na kallon finafinan Kudu, sai ka yi tunanin cewa a \u0199asar mu ba abin da ake yi sai tsafe-tsafe da aikata laifuffuka da kuma tsiraici. Rashin doka mai \u0199arfi da kuma han\u0199oron samun \u0199azamar riba sun sa lamarin ya \u0199azanta. Don haka babu mamaki, finafinan Nollowood \u0199alilan ne ake \u0257aukar su da wata daraja a \u0199asashen da su ka ci gaba, in ban da a unguwannin da \u2019yan Nijeriya ke zaune, masu \u0199awazucin tunowa da gida. Yanzu dubi wani fim da aka yi a Afrika ta Kudu wai shi &#8216;Tsotsi&#8217;, da wani da aka yi a Indiya mai suna &#8216;Slumdog Millionaire&#8217;. Wa\u0257annan finafinai ne da ake ji da su a duniya. Shi &#8216;Tsotsi&#8217;, dalar Amurka miliyan 3 aka kashe wajen shirya shi, to amma an samu dala miliyan 10 daga nuna shi a silima. Haka kuma ya ci manyan gasa guda biyu na duniya, wato lambar Oscar (a cikin 2005) da lambar Golden Globe (a 2006) a matsayin gwarzon fim cikin harsunan \u0199asashe ban da Ingilishi.<\/p>\n<p>Amma mu finafinan mu na Nijeriya, ba su da labarai masu \u0199arfi, sannan da an fara fim za ka iya cankar inda zai \u0199are. Sakamakon haka, za ka ji ana kuka da finafinan a gida da waje. Yanzu haka a Uganda har wata mata \u2019yar Majalisar Dokokin \u0199asar mai suna Sarah Wasike Mwebaza ta \u0257ora laifin \u0199aruwar ayyukan tsafe-tsafe a \u0199asar ga yawaitar finafinan Nijeriya a \u0199asar. Gwamnatin Uganda ta na nan ta na shirin kafa dokar da za ta magance matsalar. Wannan ya nuna cewa ya kamata masu shirya finafinan mu su yi karatun ta-natsu, su mayar da hankali wajen shirya finafinai masu inganci, da nuna gwaninta wajen ba da labari, da kyan hoto da sauti. Ya kamata su nuna wa sauran \u0199asashen duniya cewa ba wai neman ku\u0257i kawai ya sa su ke shirya fim ba, a\u2019a har ma don su nuna bajinta a basira da fasaha. Saboda haka, kada a dubi gara\u0253asar da Shugaba Jonathan ya bayar a matsayin ku\u0257i kawai, maimakon haka a \u0257auka cewa alama ce ta nuna goyon baya da kuma karramawa. Idan har aka saka ido a kan ku\u0257in, to ba abin da zai biyo baya sai cacar baki da rarrabuwar kai da fa\u0257ace-fa\u0257ace, daga nan kuma zancen bizines ya \u0199are kenan.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4280\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4280\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Akwai alamun cewa sau\u0199i ya fara zuwa masana\u2019antar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, domin kuwa mako uku da su ka wuce ne Shugaban \u0198asa Goodluck Jonathan ya yi wani ho\u0253\u0253asa na kyautatawa ga masu aikin fasaha da basira na \u0199asar nan. Ku\u0257i ne zunzurutu wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 200 ya bayyana [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4280\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4280\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4278,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4280","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":21,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Akwai alamun cewa sau\u0199i ya fara zuwa masana\u2019antar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, domin kuwa mako uku da su ka wuce ne Shugaban \u0198asa Goodluck Jonathan ya yi wani ho\u0253\u0253asa na kyautatawa ga masu aikin fasaha da basira na \u0199asar nan. Ku\u0257i ne zunzurutu wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 200 ya bayyana [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2010-12-08T09:11:24+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg?fit=1024%2C682&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1024\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"682\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba\",\"datePublished\":\"2010-12-08T09:11:24+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280\"},\"wordCount\":1869,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280\",\"name\":\"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg\",\"datePublished\":\"2010-12-08T09:11:24+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/03\\\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg\",\"width\":1024,\"height\":682,\"caption\":\"Wasu daga cikin sama da fayafayen dibidi 10,000 da aka \u0199wace daga wa\u0257ansu shaguna tara na \u0253arayin zaune a lokacin wani samame a birnin Brooklyn na \u0199asar Amurka kwanan nan. Hoto daga Daniel Barry na jaridar The New York Times\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4280#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba - Ibrahim Sheme","og_description":"Akwai alamun cewa sau\u0199i ya fara zuwa masana\u2019antar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, domin kuwa mako uku da su ka wuce ne Shugaban \u0198asa Goodluck Jonathan ya yi wani ho\u0253\u0253asa na kyautatawa ga masu aikin fasaha da basira na \u0199asar nan. Ku\u0257i ne zunzurutu wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 200 ya bayyana [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2010-12-08T09:11:24+00:00","og_image":[{"width":1024,"height":682,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg?fit=1024%2C682&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba","datePublished":"2010-12-08T09:11:24+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280"},"wordCount":1869,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280","name":"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg","datePublished":"2010-12-08T09:11:24+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg","width":1024,"height":682,"caption":"Wasu daga cikin sama da fayafayen dibidi 10,000 da aka \u0199wace daga wa\u0257ansu shaguna tara na \u0253arayin zaune a lokacin wani samame a birnin Brooklyn na \u0199asar Amurka kwanan nan. Hoto daga Daniel Barry na jaridar The New York Times"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4280#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tsugunne Ba Ta \u0198are Ba"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/IMG-20230314-WA0006-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4280","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4280"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4280\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4278"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4280"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4280"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4280"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}