{"id":4200,"date":"2008-06-09T08:16:00","date_gmt":"2008-06-09T08:16:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4200"},"modified":"2024-02-03T19:08:42","modified_gmt":"2024-02-03T19:08:42","slug":"hafsatu-abdulwahid-gwagwarmayar-jikanyar-mujaddadi-a-fagen-rubutu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200","title":{"rendered":"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu"},"content":{"rendered":"\r\n<h6 class=\"wp-block-heading\">\u00a0<\/h6>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafin hikaya da aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, &#8216;So Aljannar Duniya&#8217;, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama wa\u0257anda ba su fito ba, kuma ta da\u0257e ta na fa\u0257i-tashin ganin yadda littattafan ta za su fito, amma rashin ku\u0257i ya hana.<\/em><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Kwanan nan, abubuwa biyu sun faru ga Hajiyar. Na farko, ana nan ana shirin fito da wasu daga cikin littattafan ta, ciki har da wani na gajerun \u0199ir\u0199irarrun labarai. Na biyu, lokacin da aka yi wani gagarumin bikin karrama marubutan Arewa a Minna, Jihar Neja, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin marubutan Hausa da aka karrama da kyautar lambar girma.<\/em><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Ba wannan ba ne karo na farko da na yi hira da Hajiyar, domin idan kun tuna a &#8216;yan shekarun baya mun ta\u0253a kawo maku wata hira da ita. A wannan karon, mun tattauna ne kan wa\u0257annan abubuwa biyu da su ka faru gare ta, wa\u0257anda duk na alheri ne.<\/em><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Wani abu da ya kamata ku sani shi ne Hajiya Hafsatu ta na daga cikin manyan mutanen \u0199asar nan. Na farko, ita jinin Mujaddadi Shehu Usmanu \u018aanfodiyo ce. A Jihar Zamfara kuma, fitacciyar \u2018yar siyasa ce, domin a za\u0253en 2003 da aka yi, ta yi takarar zama gwamnar jihar. Ta na da &#8216;ya\u2019ya maza da mata; babba daga cikin &#8216;ya\u2019yan ta, Hajiya \u0198adaria Ahmad, ta ta\u0253a aiki a gidan rediyon BBC a London, yanzu kuma babbar ma\u2019aikaciya ce a wani kamfanin kula da filayen jiragen sama a Legas. Haka kuma wata \u0257iyar ta Hajiya Hafsatu, wato Hajiya Asiya, ta na auren tsohon Ministan Abuja, Malam Nasir Ahmad El-Rufa\u2019i. Hasali ma dai, mun yi wannan tattaunawar ne da ita a gidan shi Malam Nasir da ke unguwar Jabi, a Abuja, kwana \u0257aya bayan an karrama ta. To bugu da \u0199ari kuma Hajiya Hafsatu ta kafa tarihin kasancewa mace ta farko da ta wallafa littafin hikaya a Arewa.<\/em><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>IBRAHIM SHEME: Ran ki ya da\u0257e, ki na daga cikin marubuta na Arewa wa\u0257anda aka karrama su da lambar girma a Minna. Yaya ki ka ji a kan wannan karramawa da aka yi maki?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU AHMAD ABDULWAHID: Alhamdu lillahi, na ji da\u0257i sosai. Sai dai ba\u0199in ciki na kawai shi ne, uba na da uwa ta da miji na ba su da rai, balle su san abin da na samu. Amma murna kam na yi murna \u0199warai da gaske. Alhamdu lillahi.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Wannan shi ne karo na farko da aka karrama ki a kan harkar rubutu?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: E, an ta\u0253a yi a Kano, har su ka ba ni kamar lambar girma haka. Amma gaskiya na manta lokacin. Ina jin bara ne ko bara waccan.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Su waye su ka yi waccan karramawar?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Wata \u0199ungiya ce ta matasa marubuta.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Yaya ki ke ganin batun karrama marubuta, wanda ba a cika yi ba, yanzu ga shi ana yi? A farkon shekarar nan an yi a Abuja, sai kuma ga shi an yi a Minna. Shin wannan ya fara sauya tunanin mutane ne game da marubuta?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Ina ganin \u2019yan Arewa sun fara gane muhimmancin marubutan su. Ka san a da mutanen mu ba su damu da marubuta ba, musamman ma dai mata, ba a cika gane muhimmancin mu sosai ba, saboda an \u0257auka rubuce-rubucen mu shirme ne; na soyayya kawai. To, ina ji yanzu lokaci ya zo da aka soma gane muhimmancin mu. Saboda haka aka \u0199ir\u0199iro wannan. Ya yi daidai, kuma ya kamata a ci gaba da yin haka \u0257in.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: A wurin bikin wannan karramawar a Minna, lokacin da ake karanta ta\u0199aitaccen tarihin ki, an nuna cewa ke jikanya ce ko jinin Mujaddadi Shehu Usman \u018aanfodiyo ce. Mutane za su so ki yi \u0199arin bayani a kan wannan salsala taki.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, ni dai sunan uba na Alhaji Abubakar Garba, sunan baban sa Sa\u2019idu. Sa\u2019idu kuma Hayatu ne ya haife shi. Hayatu kuma Sa\u2019idu ne ya haife shi. To, shi kuma Sa\u2019idu, Muhamman Bello ne ya haife shi. Muhamman Bello kuma \u0257an Shehu Usmanu \u018aanfodiyo ne. Saboda haka ya zamana ni jikanyar jikanyar Shehu ce.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: To, ko daga nan za ki ba mu ta\u0199aitaccen tarihin ki?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: An haife ni a 1952 a Kano, cikin unguwar \u0198ofar Mata. Kuma na yi karatu a Shahuci da Provincial Girls School da Shekara Secondary School. Bayan nan na yi aure, inda miji na a da shi ne manajan John Holt a Kano, daga baya aka mayar da shi Gusau. Bayan nan na yi \u2018enrolling\u2019 a Beneth Correspondence College, London, inda na \u0257an \u0199o\u0199arta na sami difiloma. To, bayan nan dai na ci gaba da rubuce-rubuce. Na yi \u0257an aiki ta\u0199aitacce a Kano, kamar &#8216;part-time&#8217; haka, a gidan Rediyon Kano, amma ban da\u0257e ba, saboda ban da\u0257e da somawa ba na koma Gusau \u0257in. To, bayan nan dai sai rubuce-rubuce kawai da na ci gaba da yi a gida.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: A binciken da na yi na fahimci cewa ke ce mace ta farko a Arewa da ta fara wallafa littafin \u0199ir\u0199ira, wato littafin ki &#8216;So Aljannar Duniya&#8217;. Shin ki na da masaniyar cewa mata sun yi rubutu kafin ke ko kuwa a iyakar sanin ki ke ce ki ka fara \u0257in?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, gaskiya ni dai ban ta\u0253a ganin littafin wata ba ko da a jarida ko a wani guri da aka ce ta yi rubutu, sai da nawa ya fito tukuna. To, kuma bayan nawa ya fito \u2013 ina ji da kusan shekara 12 ma \u2013 na Zaynab Alkali ya fito. Koda ya ke akwai bambanci tsakanin nawa da ita, don ita na Turanci ta yi, ni kuwa da Hausa na yi.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ko za ki gaya mana tarihin rubuta &#8216;So Aljannar Duniya&#8217;? Na farko ma dai, menene ya fara ba ki tunanin rubuta littafi a lokacin da mata ba sa yi?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, gaskiya a makarantar da na yi an \u0257an ba mu \u0199arfin gwiwar rubuta \u2019yan labarai a aji, har mu kan kar\u0253i \u2019yan kyautuka a kai. A lokacin da na rubuta wannan ma da Turanci na soma rubuta shi duk da cewa Turancin nawa bai nuna ba, saboda yaya ta da ta auri Balaraben Libya ta sami \u2019yan tangar\u0257o\u0257i wajen dangi, haka da iyaye, wa\u0257anda ba su so ta auri wani ba\u0199o ba. To, daga baya kuma bayan na rubuta wannan sai na zo na auri wani Balaraben Yemen. To, sai labarin ya zamo kusan iri \u0257aya ne. To, da na rubuta shi da Turanci ban sami bugawa ba har lokacin da kamfanin NNPC Zaria ya yi gasa \u0257in nan, sai na fassara shi da Hausa na shiga gasar. A 1970 kenan. Na sami zuwa ta biyu a matsayi na na mace ka\u0257ai da ta shiga wannan takara. To, bayan nan ne aka buga shi a 1972.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Tunda da Turanci ki ka fara rubuta shi, da yaya sunan sa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Wallahi a lokacin ban sanya masa suna ba, don \u0257aya daga cikin abin da su ka hana ita yayar tawa a buga littafin shi ne mu na ta \u0199o\u0199arin mu ga wanne irin suna ya kamata a sanya masa. Saboda haka a lokacin ban sanya masa suna ba. <em>(Murmushi)<\/em> Amma dai Malam Sheme ya sanya masa suna a jarida (<em>Weekly Trust<\/em>); na gani. To, ina jin idan za mu yi shi da Turanci abin da za mu kira shi kenan!<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Akwai yiwuwar za a fassara shi ne nan gaba?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: E. An ma fassara shi da Turanci da Fulatanci, kuma Jami\u2019ar Usmanu \u018aanfodiyo, Sokoto, sun yi shi da Arabiyya. To, amma dai duk da haka har yanzu babu wanda aka rubuta a ciki.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Me ya tsayar da aikin bugun?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Gaskiya rashin ku\u0257i ne a lokacin. Amma shi na Arabiyyar na samu wani mutumin Saudiyya da ya ce zai buga. To, amma abin ba\u0199in ciki na yi gobara a 1995, saboda haka wannan kwafen na Arabiyya \u0257in ya \u0199one, kuma na yi \u0199o\u0199arin samun kwafe a hannun jami\u2019ar ta Sokoto, don in kwafa, ban samu ba. Amma yanzu wani yaro ya sake buga shi da Larabci \u0257in. Saboda haka yanzu ina da rubutun hannu na Larabci \u0257in.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Labarin &#8216;So Aljannar Duniya&#8217; labari ne na Fulani, ku kuma ga shi a gari ku ke. Me ya ba ki tunanin ki rubuta labarin Fulani maimakon labarin Hausawa wanda ki ka fi sabawa da shi?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, ai ni Bafulatana ce, kuma duk da yake mu na cikin Hausawa, gidan mu ba mu zubar da yawancin al\u2019adun mu na Fulani ba, domin ba a ma Hausa a gidan mu. Idan yaro ya tashi ba ya yin Hausa sai ya kai irin shekara bakwai \u0257in nan; sannan ya soma fita waje, ya koyi Hausa. Saboda haka ba wai wani abin a zo a gani ba ne don na rubuta al\u2019adun mu.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Bayan wannan littafi sai aka \u0257auki tsawon lokaci ba ki yi wani littafin ba har zuwa lokacin da ki ka yi &#8216;\u2019Yar Dubu Mai Tambotsai&#8217;. Me ya sa aka samu wannan tsawon lokaci, kuma shekara nawa aka yi a wannan tsakanin?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Gaskiya ban san yawan shekarun ba, amma ina da littattafan da ma a rubuce; bugawa ne kawai ba a yi ba, saboda yanayin yadda babu ku\u0257in da mutum zai buga \u0257in.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Wani abu da mu ka yi la\u2019akari da shi shi ne, a matsayin ki na wacce ta soma rubuta littafin \u0199ir\u0199ira a Arewa, sai ya kasance \u0199waya biyu ka\u0257ai ki ka rubuta, ban da littattafan addini da mu ka san kin rubuta daga baya. Me ya sa ba ki rubuta littattafai da yawa ba kamar yadda sauran marubuta su kan yi?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU <em>(murmushi)<\/em>: A\u2019a! don littattafai ina da littattafai da dama; matsalar dai yadda na gaya maka ita ce bugawa. Domin ni ina ganin in buga su da \u0199arko sosai, wato abin da Bature ya ke cewa da &#8216;quality&#8217;, ya fi in buga su irin yadda sauran mutanen mu su ke yi da araha \u0257in nan su shiga kasuwa. To, shi ne kawai matsalar da ta hana ni bugawa da yawa, su fito. Amma akwai su nan a ajiye.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ki na ta kukan rashin ku\u0257i, amma wasu za su kalle ki a matsayin attajira, saboda \u2019ya\u2019yan ki manya ne; an san su na auren manyan mutane da sauran su, kuma ke \u0257in ma dai babba ce. Anya za a yarda da maganar rashin ku\u0257in nan, na dai a buga \u0257an littafi?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: A\u2019a, to ai kamar nawa da na ke yi su na da tsada da yawa. Ka ga kamar wanda za a fitar wannan watan \u2013 &#8216;Saba \u018aan Sababi&#8217; \u2013 na \u0199ir\u0199irarrun \u0199ananan labarai, abin da na biya mai bugawar shi ne N200,000 a kan kwafe 1,000 kacal. To, ka ga kuwa ku\u0257in ba ka\u0257an ba ne kenan. Kuma yara su na yin iyakar gwargwadon iyawar su, amma kowa ya na da iyali na kan sa; ba za ka \u0257auki nauyin da ya fi \u0199arfin mutum ka \u0257ora masa ba, ballantana tunda baban su ya rasu. Kuma duk ba su da\u0257e da kawo \u0199arfi ba ai, saboda ba su da\u0257e da gama makaranta da kama aiki ba. To, ka ga akwai matsaloli da yawa a irin wannan.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sannan kuma kallon ku\u0257i da ake yi min, to alhamdu lillahi, sai in ce Allah ya \u0199ara min! Amma dai suna ne. Sarakuta kuma da masu ku\u0257i, wannan ba hujja ba ce ta mutum ya na da shi, domin sai surukin ya bayar sannan za ka kar\u0253a. To, saboda haka ana dai \u0199o\u0199artawa. Yanzu dai mun yi da su za a tara duk \u2019yan rubuce-rubucen a tsinci wanda za a tsinta, su ha\u0257a ku\u0257i su buga, wanda su ka ga ya dace da wanda za su iya.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Yanzu kin nuna mana cewa ana aiki a kan sabon littafin ki. Shi ma na \u0199ir\u0199ira ne kenan?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: E, na \u0199ir\u0199ira ne. Wato na rubuta \u0199ananan labarai guda 46, wa\u0257anda mu ka ce za mu kasa su kamar kashi uku ko hu\u0257u. Ya danganta da dai yadda abin yake. To, kashi na farko ne zai fito; ya kamata ma a ce tun bara ya fito. To, harkar masu bugawa \u0257in ce\u2026, sai dai ya yi min al\u0199awari, ya ce \u0199arshen watan nan idan Allah ya yarda zai fito. To, akwai kuma da yawa littattafan ai. Akwai biyu ma da Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano su ka \u0257auka za su buga, wanda na yi a kan mu\u2019ujizojin Al\u0199ur&#8217;ani mai girma. Sannan akwai \u0257aya da na yi kan wani labari na gaskiya da na \u0199ir\u0199iro na rubuta, na sanya masa suna &#8216;Aibun Doka&#8217;. To, sun \u0257auki wa\u0257annan biyun za su buga.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Akwai yiwuwar ki rubuta wa\u0199o\u0199i ko wasan kwaikwayo?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: E to, biyu daga cikin \u0199ananan labaran nawa na mayar da su wasan kwaikwayo, sannan kuma ina da rubutattun wa\u0199o\u0199i \u2013 amma na Turanci \u2013 da yawa, domin gaskiya na gwada rubutawa da Hausar, na kasa!<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ashe ki kan yi rubutu da Turanci? Amma har yanzu ba a ga ko guda \u0257aya ba!<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Wallahi ina yi, amma duk dai harkar idan aka juya ta batun dai bugawa \u0257in ce. Har yanzu ban samu wanda zai \u0257auki nauyin bugawar ba. Ni ku\u0257in ba su dame ni ba, amma dai a ce aikin ya fito, shi ne muhimmanci a wuri na, amma har yanzu ban samu wanda zai \u0257auki nauyin ba. Amma na Turancin dai a kwanan nan mu ka zauna da yara mu ka tsinci wa\u0257anda za a buga \u0257in. To, ban san dai abin da su ke ciki ba dai yanzu, amma sun yi min al\u0199awarin za su buga, to amma ban san lokacin ba.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Me ya sa kamfanin Gaskiya Corporation ko NNPC Zariya ba su buga littattafan ki da yawa ba, musamman tunda a wancan lokacin su na cikin aikin buga littattafai da yawa, ba kamar yadda daga baya su ka dur\u0199ushe ba?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Wallahi ni dai abin da su ka gaya min shi ne ba su da ku\u0257i. Duk dai magana guda ce a lokacin da na kai masu nawa guda biyu, wa\u0257anda har da ma na \u2018Dare Dubu Da \u018aaya\u2019 da na rubuta yadda yara za su iya karantawa, saboda na farkon nan bai kamata yara \u0199anana su karanta shi ba. To, na rubuta daga na 1 zuwa na 5 kamar yadda aka yi shi na Hausa \u0257in nan. Har yanzu ma kwafen ya na hannun su, ba su dawo min da shi ba, don sun ce min yanzu su na &#8216;yan shirye-shiryen soma buge-bugen littattafai.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Yaya ki ke ganin harkar wallafa a Arewa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, gaskiya abin ya na da ciwo. Kuma duk a wasu taruka da aka yi na marubuta na kan bayar da shawarar cewa su kan su marubutan su na da laifi, saboda za a iya ha\u0257in gwiwa, a saka &#8216;yan ku\u0257a\u0257e; kowa ya bayar da gudunmuwar sa, a ha\u0257a ku\u0257in nan a ajiye. Idan marubuci ya rubuta littafi a duba, idan ya cancanta a buga shi, sai a \u0257auki nauyin bugawar. In ya so bayan an buga, an sayar ko an \u0199addamar, abin da aka sayar, sai a mayar a ajiye. Kuma nan gaba sai a sake samun wani ya yi. Amma duk shawarwarori na da na ke bayarwa, har yanzu babu wacce ta samu shiga.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ita gwamnati da masu hannu da shuni fa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, gwamnati dai ba ta san da zaman marubuta ba, sai dai kwanan nan da ake ta abubuwan nan na ga gwamnatin Neja ta \u0257auki nauyi. To, kuma gwamnatin mu ma ta Jihar Zamfara ta yi al\u0199awarin za ta bu\u0257e mana wani asusu wanda idan an yi littafi, a bincika shi a gani; idan ya cancanta, a buga. Sai mu yi fatan sauran gwamnoni za su yi koyi da su.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Wane kira za ki yi ga marubuta wa\u0257anda ke kasa fito da littattafan su, har ma wani sai ya yi fushi ya daina?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: Bai kamata mutum ya yi fushi ya daina ba, domin idan Allah ya ba ka basira, (idan) ka daina amfani da ita, kamar ka yi masa butulci ne. Shi kuma rubutu ko da mutum ba shi da rai ya na da amfani. Kamar yadda mu ka ga littattafan Shehu da Asma\u2019u \u0257aruruwan shekaru ga su nan yanzu ana morar su. Saboda haka kada mutum ya bari. Kada rashin bugawar nan ya karya masa gwiwa; ya yi ta rubutun ya na ajiyewa har Allah ya kawo wanda zai zo ya buga masa. Saboda komai ya na da lokaci; idan lokacin abu bai yi ba, babu yadda za a yi ka tilasta lokacin ya yi.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: To, Hajiya, mun gode, \u0199warai.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">HAFSATU: To, madalla. Ni ma na gode.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>(An ciro daga mujallar Fim ta watan Yuni 2008)<\/em><\/p>\r\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_4200\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4200\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u00a0 HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafin hikaya da aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, &#8216;So Aljannar Duniya&#8217;, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama wa\u0257anda ba [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4200\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4200\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4199,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"Hajiya Hafsatu Abdulwahid da littafin 'So Aljannar Duniya'","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[31,402,404,403],"class_list":["post-4200","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","tag-adabin-hausa","tag-hafsat-abdulwaheed","tag-hafsatu-abdulwaheed","tag-so-aljannar-duniya"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":79,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"\u00a0 HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafin hikaya da aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, &#8216;So Aljannar Duniya&#8217;, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama wa\u0257anda ba [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2008-06-09T08:16:00+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-02-03T19:08:42+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg?fit=1035%2C739&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1035\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"739\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"14 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu\",\"datePublished\":\"2008-06-09T08:16:00+00:00\",\"dateModified\":\"2024-02-03T19:08:42+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200\"},\"wordCount\":2872,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2008\\\/06\\\/IMG-20230302-WA0005.jpg\",\"keywords\":[\"adabin Hausa\",\"Hafsat Abdulwaheed\",\"Hafsatu Abdulwaheed\",\"So Aljannar Duniya\"],\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200\",\"name\":\"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2008\\\/06\\\/IMG-20230302-WA0005.jpg\",\"datePublished\":\"2008-06-09T08:16:00+00:00\",\"dateModified\":\"2024-02-03T19:08:42+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2008\\\/06\\\/IMG-20230302-WA0005.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2008\\\/06\\\/IMG-20230302-WA0005.jpg\",\"width\":1035,\"height\":739},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4200#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu - Ibrahim Sheme","og_description":"\u00a0 HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafin hikaya da aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, &#8216;So Aljannar Duniya&#8217;, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama wa\u0257anda ba [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2008-06-09T08:16:00+00:00","article_modified_time":"2024-02-03T19:08:42+00:00","og_image":[{"width":1035,"height":739,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg?fit=1035%2C739&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"14 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu","datePublished":"2008-06-09T08:16:00+00:00","dateModified":"2024-02-03T19:08:42+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200"},"wordCount":2872,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg","keywords":["adabin Hausa","Hafsat Abdulwaheed","Hafsatu Abdulwaheed","So Aljannar Duniya"],"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200","name":"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg","datePublished":"2008-06-09T08:16:00+00:00","dateModified":"2024-02-03T19:08:42+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg","width":1035,"height":739},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4200#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2008\/06\/IMG-20230302-WA0005.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4200","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4200"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4200\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5309,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4200\/revisions\/5309"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4199"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4200"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4200"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4200"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}