{"id":4080,"date":"2008-02-17T18:44:00","date_gmt":"2008-02-17T18:44:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4080"},"modified":"2026-08-21T08:41:26","modified_gmt":"2026-08-21T08:41:26","slug":"ashe-mace-ma-mutum-ce-hira-da-rahma-abdulmajid","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080","title":{"rendered":"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid"},"content":{"rendered":"\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hajiya Rahama A. Majid tana daga cikin fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ta rubuta littattafan hikaya masu damar gaske, kuma ta ci moriyar su, ciki kuwa har da littafin ta da ta fi so, wato <em>\u2018Za Ta Iya.\u2019<\/em> A yanzu haka \u0257aliba ce a Jami\u2019ar Al-Azhar ta \u0199asar Masar. To, kwanan nan ta yi wani ho\u0253\u0253asa, inda ta fito da wani jibgegen littafin hikaya mai suna<em>\u00a0&#8216;Mace Mutum&#8217;<\/em>, wanda girman sa ya fi na kowane littafin Hausa da aka ta\u0253a bugawa, domin kuwa ya haura shafi 520 ne. Kamfanin Gidan Dabino Publishers ne suka wallafa littafin.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shin wacece Rahama A. Majid? Menene tunanin ta game da rubuce-rubucen Hausa, da rayuwar mata a \u0199asar Hausa, da kuma makarantan littattafan Hausa? Rahma dai za a iya cewa mace ce mai kamar maza, kwari ne babu! Tana da kazar-kazar da nuna \u0199wazo da bajinta a duk harkar da ta sa kan ta. Idan aka ce maka za ta iya yin abu kaza na bajinta, to kai da ganin ta ka san za ta iya.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan hirar da za ku karanta, mun yi ta da Rahma ne tun a cikin shekarar 2005, a lokacin da ake ta yin kici-kicin buga littafin <em>\u2018Mace Mutum.\u2019<\/em> An buga hirar a mujallar Fim ta Nuwamba da Disamba 2005. Kafin mu kawo muku sabuwar hira da marubuciyar, mun ga ya dace ku fara karyawa da wannan, domin kuwa ko me za ta fa\u0257a a yanzu, bai dai wuce wanda ta fa\u0257a a wannan hirar ba.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A sha karatu lafiya.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Hajiya Rahama Abdulmajid, mu fara da jin ta\u0199aitaccen tarihin ki.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Assalamu alaikum. Suna na Rahma Abdulmajid. An haife ni a shekarar 1980 a Agege, Legas, kuma a can na yi makarantar firamare, na fara sakandare, amma daga bisani na \u0199arasa karatun sakandare \u0257ina a Zariya, bayan da aka yi mana canjin wurin aiki a shekara ta 1998. A Zariya ne na yi difloma a Shari\u2019a, \u0199ar\u0199ashin Jama\u2019atu Nasril Islam.<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: A wace makaranta kenan?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: A <em>Jama\u2019atu Institute<\/em> ne na yi karatun difloma daga shekarar 1999 zuwa 2000. Bayan nan ne na koma gida Legas, na yi kwasakwasai irin na komfuta har zuwa shekarar 2002, lokacin da muka fara cuku-cukun neman tallafin karatu zuwa \u0199asar Misra. A halin yanzu ina karatu a Jami\u2019ar Al-Azhar, shekara ta 3 zuwa ta 4, ina \u0253angaren Tarihi da Al\u2019adu. Wannan shi ne ta\u0199aitaccen tarihi na.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;<\/p>\r\n<p><strong>SHEME: Bari mu koma baya ka\u0257an; ki gaya mana sunayen makarantun da kika yi na boko.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Da farko dai na yi makarantar firamare \u0257ina a <em>KK Primary School<\/em> da ke Agege \u0257in, kuma bayan kammalawa ta a dai nan Agege \u0257in na ci gaba a <em>Dairy Farm Secondary School.<\/em> Wannan kenan ta \u0253angaren boko. A \u0253angaren Arabiyya kuma na soma a makarantar gidan mu ne da ake ce wa Nubrasul Huda, wacce bayan mun yi sauka na sake shiga wata wadda ake ce mata Rahmatu Islamiyya wadda take Ikeja. Bayan na kammala aji shida sai na wuce Danmarkazul Illumi Islami ta Sheikh Adam El-Uluriy na yi aji 3, lokacin ne kuma ya yi daidai da tafiyar mu Zariya.<br \/><strong><br \/>SHEME: A bayanin ki, kin ce an haife ki a Legas, to ko za ki iya bayyana asalin jihar ki?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Gaskiya idan aka cire Legas to sai dai a yi waje da ni, domin mahaifin mu mutumin Sudan ne, mahaifiyar mu kuma \u2019yar asalin Jihar Adamawa ce. Amma na tashi ne a matsayin cikakkiyar Bahaushiya ko in ce cikakkun Hausawa a gidan mu, domin ita ce al\u2019adar da mahaifin mu ya kar\u0253a tun zuwan sa a matsayin sa na Musulmi.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ku nawa ne a gidan ku, kuma ke ta nawa ce?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Mu 22 ne, kuma ni ce ta cikon 22 \u0257in.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Idan muka koma \u0253angaren rubutun adabi, da yaushe kika fara yin rubutu?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Sanannen abu ne ga duk wanda ya yi makaranta a Kudu cewa yaren Nijeriya da zai iya \u0257auka zai zama Yarbanci ne. Ni dai Yarbanci na koya kuma shi na iya rubutawa, to amma a wannan lokutan da wasu littattafai ke tashe, akwai wasu gidajen rediyo a Legas \u0257in, Sashen Hausa, suna karanta littattafan Hausa, mu kuma mukan \u0257an bi. To amma da yake yana \u0257aukar sati kafin mutum ya ji ina aka kwana a wannan labarin, to bayan zuwan mu Kano wata ziyara, sai na sayi wasu littattafan na ri\u0199a bi ina karantawa, wanda ta cikin su ne zan iya cewa na koyi Hausa. Kuma abin da ya ja hankali na wajen yin rubutun littafi shi ne wani littafi da na ta\u0253a karantawa, wato \u2018In Da So Da \u0198auna&#8217; na Ado Ahmed. A wannan littafi da akwai wani babi na musamman wanda aka ce &#8220;Kishi Kumallon Mata.&#8221; A gani na, wannan karin magana ta sa\u0253a al\u2019ada, ganin ba mata ka\u0257ai ne suke yin kishi ba. A wannan lokacin ne na fara rubuta duk wani labari da na ji, ko ya zo kai na, a kan kishin maza da na mata. To wannan sai ya zama kamar wani raddi ne a kan wancan karin magana, wanda a kan sa na fitar da littafi na na farko, \u2018Wa Ya Fi Kishi?\u2019<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na samu masu \u0199alubalanta, suna ta yin kira a kan cewa ya kamata marubuta su juya suna yin rubutu mai yawa saboda a kawo canji a adabin Hausa, ya zamanto ya samu \u0199ima daidai da adabi na duniya. Sannan kuma abu na biyu, ya zamanto ya kawar da kasala ta karatu, to amma sai aka kasa samun wanda zai bugi \u0199irji har yau ya yi, kowa ya koma daga gefe yana jiran wani ya yi tukunna. Sai na ga cewa a wannan lokaci ana bu\u0199atar wani ya bugi \u0199irji ya ce bari in je in yi wannan.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Wasu na ganin idan suka yi littafi mai yawa, wai \u2019yan kasuwa ba za su amince ba domin zai yi tsada. Ke ba ki yi tunanin haka ba kika rubuta wannan wagegen littafi?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Kasuwar littafi tana da ala\u0199a da kowace \u0199a\u2019idar kasuwanci. \u0198a\u2019idar kasuwanci tana bu\u0199atar ka kyautata abu, sannan ka tallata wa jama\u2019a cewa lallai wannan abin mai kyau ne, sannan kuma ka sa ido kan ganin yaya za a yi su saya. To amma kasuwar littattafan mu na Hausa da ake ganin shin za ta tafi ko ba za ta tafi ba? Shin ina ta tsaya tukunna? Littafi zai fito a sati, amma babu wanda ya san zai fito sai marubucin. Wata\u0199ila ma shi mai shagon da za a kai wa littafin domin ya sayar bai san da littafin ba sai a ranar, a wannan lokacin ake tunanin cewa za a iya tantance shin ko wannan littafin yana da kasuwa ko kuma ba shi da shi? Bisa ga tsarin kasuwanci, littafin da ya zamo cewa na \u0257aya ko ka kyautata aikin sa, misali tafiyar ka ta baya ta nuna wa mutane cewa e, lallai wannan aikin da gaske kake. Ina \u0199o\u0199arin ganin na tallata littafi na tare da sanar da isowar wannan littafi da inganta aikin sa. Kuma wannan shi ne zai nuna wa mutum cewa e, na gama duk abin da zan iya. Abin da ya yi saura kuma shi ne \u0199addara da za ta biyo baya a kan me littafin ya \u0199unsa?<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u0199alubalantar sa, kamar yadda &#8220;adabin kasuwar Kano&#8221; yake da masu \u0199alubalantar sa. Haka ma ya ke da wa\u0257anda suke son sa. To wannan ya nuna cewa ba \u0199o\u0199arin fita daga &#8220;adabin kasuwar Kano&#8221; ba ne, illa cewa ra\u2019ayi na da tunani na shi ne ya yi mani wahayin wannan littafin.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Wacce irin ala\u0199a ce tsakanin ki da masu karatu?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Ala\u0199ar da ke tsakani na da masu karatu ta fi komai da\u0257i a wuri na. Na \u0257auki masu karatun littafi kamar wani \u0199ashin baya ne, kuma su ne za su iya gaya maka cewa abin da ka rubuta ya yi da\u0257i ko kuma an samu kuskure domin ka gyara a rubutun gaba. Hakan ya sa akwai ala\u0199a mai kyau tsakani na da su.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ala\u0199ar ki da sauran marubuta fa, domin masu kula da harkokin marubuta na ganin babu ala\u0199a mai kyau a tsakanin ku marubuta.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ala\u0199a tsakani na da mafi yawan marubuta ala\u0199a ce mai kyau. Ko da yake ni ba a \u0199asar nan nake zaune ba, to amma na samu an kafa \u0199ungiyoyi wanda kuma manufar kafa su shi ne wata ta yi gaba da wata, wanda hakan ko ka\u0257an bai kamata ba. Amma ni ba na cikin kowace \u0199ungiya; kusan in ce ni marubuciya ce mai zaman kan ta.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ga shi ke monita ce a wani zauren tattaunawa a intanet a kan rubuce-rubucen Hausa (Majalisar Marubuta). Ko za ki yi mana bayani a ta\u0199aice kan yadda wannan zaure yake, da manufofin sa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Wannan yana da labari ne na shiga ta ita \u0199ungiyar. Kafin in shiga ban san cewa Hausa adabi ba ne wanda yana da masu \u0199alubalantar wata kasuwa wadda saboda nisa na da ita, iyakaci na in yi littafi in ajiye, amma da shiga ta wannan \u0199ungiyar kafin ma in zama monita a ciki na ga wa\u0257annan amfanonin da dama. A cikin wannan majalisar na samu sanin wasu littattafan Hausa da aka yi masu \u0199ima, da kuma abubuwan da ake \u0199alubalantar marubuta da su, sai in je in \u0257auka wanda zan gyara ya zamanto cewa na gyara. Sannan kusan zan iya cewa a da ina da \u0257an shakku wajen cewa yaya za a yi in yi littafin Hausa mai yawa ya tafi? To amma shiga ta wannan majalisa ya nuna min cewa lallai ashe ana iya yin, kuma zai iya tafiya. Misali, na tarar ana tattaunawa a kan \u2018Ruwan Raina,\u2019 wanda a lokacin ban san shi ba, da kuma \u2018\u2019Yartsana,\u2019 wanda shi ma ban san shi ba sai a cikin wannan majalisar na samu cewa littattafai ne masu yawan shafuka, kuma aka yi masu kyakkyawan bugu. Sai ga shi ba su samu wata matsala ta kasuwa ba, sannan marubutan da suka yi su sun cancanci yabo.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda haka ina shawartar marubuta da su shiga cikin wannan \u0199ungiya ko majalisa domin akwai abubuwan \u0199aruwa masu tarin yawa; haka ma masu karatu, domin su samu damar \u0199alubalantar abin da marubuta suke ciki. Wannan ita ce hanya ta ha\u0257uwa da \u2019yan\u2019uwan su masu rubutu a tattauna da manazarta wa\u0257anda suka yi fice da fuskantar ina adabin ya dosa. Hakan a gani na zai taimaka wajen kawo cigaba ga ita wannan harka tamu.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Yaya kike ganin adabin Hausa zai iya kasancewa nan da wasu shekaru?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: E, ai Juma\u2019ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa. Daga cikin kashi biyu, wato marubuta da masu karatu yanzu ya zamanto su ne suke canza adabin Hausa, wanda wannan kuma alamomi ne na nasara. Da farko idan na soma da masu karanta littafi a zamanin baya, kamar \u0199arshen \u0199arnin da ya wuce, littattafan Hausa suna samun suka domin babbar matsalar da na sha fa\u0257i ita ce masu bayar da sa\u0199on suna da wani sa\u0199o da suka ga cewa lallai ya damu Hausawa, ya kamata kuma a tashi a yi fama da matsalolin, kamar na auren dole da makamantan su, domin haka na da illolin sa na \u0253acin \u2019ya\u2019ya, to amma sai suka manta da wani abu guda \u0257aya, wato ba iyayen ba ne suke karanta littafin za su iya kwafar \u0253acin da aka nuna a cikin littafin, maimakon iyayen wanda da aka yi wasu wannan salon. Hakan ya janyo \u2019yan matsaloli wa\u0257anda littattafan baya suka samu kan su a ciki. To amma masu karatun da ake samu a yanzu su ne \u2019ya\u2019ya na wancan zamanin wa\u0257anda suka karanta kuma su ka \u0199aru da wani abu, su ne suka zama iyaye, suke karatu a yanzu. Adabin Hausa ya samu iyaye da \u2019ya\u2019yan su suna iya karantawa, sa\u0253anin zamanin baya.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na biyu, masu karatu na da hanyoyin sabuwa ko hul\u0257a da marubuta kamar ta wayar tafi-da-gdan-ka ko kuma ta intanet, domin yi masu gyare-gyare ko sharhi da makamantan su. Ta \u0253angaren marubuta kuma, ban da masu yin canjin she\u0199a ma da akwai wa\u0257anda suka ce adabi ko na menene yana da amfani, don haka sun bayar da lokacin su wajen yi wa adabin Hausa hidima wacce ta cancanta za su rubuta da kan su, za kuma su yi kira ga marubuta su ce kuma ku rubuta abu kaza. Saboda haka adabin yanzu idan za mu lura da littattafan da ake rubutawa masu yawan shafuka da kyawu, zai nuna mana cewa duk wani littafi da yake kamar wata annoba ce a cikin adabin Hausa a baya kamar shekara goma, zai zamanto cewa ya kwanta dama.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Akwai wani kira da za ki yi ga su marubutan Hausa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Kiran dai a kowane lokaci shi ne wa\u0257ansu abubuwa ne wa\u0257anda da zarar an same su komai zai daidaita. Marubuci ya kamata ya san cewa ga inda sa\u0199on sa za shi. Na biyu, ana bu\u0199atar marubuci ya san menene adabi. Na uku shi ne menene na sa\u0199o, wato adabin da nake yi wa hidima? Sannan kuma bai kamata marubuci ya yi tsoro ba, ba wai ina nufin sai ranar da marubuci ya fito ya zagi wani babba ba, a\u2019a, tsoron kasuwa ma bai kamata a ce marubuci ya ji shi ba, domin ba a ta\u0253a yin masu yi wa adabi hidima iyakacin sa ya damu da kasuwar sa ba ko inda adabin za shi ba. Don haka ya kamata ya zamanto cewa wannan yana kan gaba.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: To menene zai biyo bayan \u2018Mace Mutum\u2019 daga al\u0199alamin ki?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Abin da zai biyo bayan \u2018Mace Mutum\u2019 shi ne ina so in ci gaba da yin rubutu a manyan shafuka mai ingantaccen bugu, kuma wanda zai zamanto yana da sa\u0199on da zamanin yake so. Wannan ya sanya ba zan iya sanin menene zai biyo bayan \u2018Mace Mutum\u2019 ba, domin ina so ne in kasance kowace shekara a ce da littafin da zai fito, ya zamanto cewa ainahin sa\u0199on da ake bu\u0199ata shi littafin ya taho da shi.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Yaushe ne za ki kammala karatun ki ki dawo Nijeriya da zama?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: Shekara mai zuwa ne zan kammala karatu na, to amma da yake ina da bu\u0199atar \u0199are digiri na na biyu shi ne ya sa ba ni da masaniyar lokacin da zan dawo.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: A can Al\u0199ahiran ko kuwa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: E, ko a Al\u0199ahira ko kuma a gaba da ita.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: A\u2019a, to shi kenan kin dinga karatu? Aure fa?<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA (ta yi dariya): Ai aure ba ya hana karatu.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME:To yaushe za a yi auren? Wasu za su so sanin haka daga gare ki.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: To ai kada wanda ake so a yi da shi ya ji, kuma ya matsu ya ce an sa mara\u0257a magana! (<em>ta \u0199yal\u0199yace da dariya<\/em>)<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Hajiya Rahama, mun gode.<\/strong><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHAMA: To, ni ma na gode.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8212;&#8211;<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>\u0198ARIN BAYANI: An sake buga wannan hirar a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma&#8217;a da ta gabata, 15 ga Fabrairu 2008<\/em><\/p>\r\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_4080\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4080\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hajiya Rahama A. Majid tana daga cikin fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ta rubuta littattafan hikaya masu damar gaske, kuma ta ci moriyar su, ciki kuwa har da littafin ta da ta fi so, wato \u2018Za Ta Iya.\u2019 A yanzu haka \u0257aliba ce a Jami\u2019ar Al-Azhar ta \u0199asar Masar. To, kwanan nan ta yi [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4080\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4080\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4081,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4080","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":52,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Hajiya Rahama A. Majid tana daga cikin fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ta rubuta littattafan hikaya masu damar gaske, kuma ta ci moriyar su, ciki kuwa har da littafin ta da ta fi so, wato \u2018Za Ta Iya.\u2019 A yanzu haka \u0257aliba ce a Jami\u2019ar Al-Azhar ta \u0199asar Masar. To, kwanan nan ta yi [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2008-02-17T18:44:00+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2026-08-21T08:41:26+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"320\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"400\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"12 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid\",\"datePublished\":\"2008-02-17T18:44:00+00:00\",\"dateModified\":\"2026-08-21T08:41:26+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080\"},\"wordCount\":2541,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/Picture-040-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080\",\"name\":\"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/Picture-040-1.jpg\",\"datePublished\":\"2008-02-17T18:44:00+00:00\",\"dateModified\":\"2026-08-21T08:41:26+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/Picture-040-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/Picture-040-1.jpg\",\"width\":320,\"height\":400},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4080#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid - Ibrahim Sheme","og_description":"Hajiya Rahama A. Majid tana daga cikin fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ta rubuta littattafan hikaya masu damar gaske, kuma ta ci moriyar su, ciki kuwa har da littafin ta da ta fi so, wato \u2018Za Ta Iya.\u2019 A yanzu haka \u0257aliba ce a Jami\u2019ar Al-Azhar ta \u0199asar Masar. To, kwanan nan ta yi [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2008-02-17T18:44:00+00:00","article_modified_time":"2026-08-21T08:41:26+00:00","og_image":[{"width":320,"height":400,"url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"12 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid","datePublished":"2008-02-17T18:44:00+00:00","dateModified":"2026-08-21T08:41:26+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080"},"wordCount":2541,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080","name":"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg","datePublished":"2008-02-17T18:44:00+00:00","dateModified":"2026-08-21T08:41:26+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg","width":320,"height":400},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4080#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Ashe Mace Ma Mutum Ce? Hira da Rahma Abdulmajid"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/Picture-040-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4080","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4080"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4080\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5746,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4080\/revisions\/5746"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4081"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4080"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4080"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4080"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}