{"id":4059,"date":"2008-04-04T04:49:00","date_gmt":"2008-04-04T04:49:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4059"},"modified":"2008-04-04T04:49:00","modified_gmt":"2008-04-04T04:49:00","slug":"daga-mace-mutum-sai-me","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059","title":{"rendered":"Daga &#8216;Mace Mutum,&#8217; Sai Me?"},"content":{"rendered":"\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>Fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ta yi mani bayani kan sakamakon da ta gani bayan fitar jibgegen littafin ta a kasuwa. Ina ta sa gaba yanzu?<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>KWANAN nan ne fitacciyar marubuciyar nan Rahma Abdul Majid ta fitar da sabon littafin ta mai suna \u2018Mace Mutum.\u2019 \u0198aton littafi ne, domin rabon ka da ganin littafin hikaya mai yawan shafukan sa tun &#8216;\u0198arshen Alewa \u0198asa&#8217; na marigayi Bature Gagare; shafi 520 ne, don haka ya ma fi &#8216;\u0198arshen Alewa \u0198asa\u2019 yawa kenan.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Jigon littafin shi ne yadda ba a yi wa mata adalci a zamantakewar yau da kulluma a \u0199asar Hausa, saboda irin danniyar da maza ke yi masu.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Mun tattauna da marubuciyar kan littafin, da kuma inda ta sa gaba bayan fitar sa. Bismillan ku:<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>IBRAHIM SHEME: Kwanan nan littafin ki, \u2018Mace Mutum,\u2019 ya shiga duniya. Yaya ki ka ga kar\u0253uwar sa a wurin jama\u2019a?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA A. MAJID: Alhamdu lillah wa shukrallah! Gaskiya batun kar\u0253uwar wannan littafi sai godiya ga Maiduka, domin kamar yadda mu ka zata littafi mai yawan shafuka da yawan farashi kasuwar sa na tafiya ne a hankali, don haka ne ma a lokacin da na ke ganawa da wasu cikin dilolin mu na yi ta yi masu matashiya kan yadda za su jure wa wannan kasuwa mai tafiyar hawainiya. Amma cikin ikon Allah sai ga shi littafi a satin farko an soma neman sa a wasu guraren, ya \u0199are. Sannan ina mai tabbatar maka da har yau bai gama kara\u0257e inda ake neman sa ba saboda saurin tafiyar da ya yi a wasu wuraren da aka fara \u0199addamar da shi. Gaskiya makaranta sun yi rawar gani, sai godiya gare su da Ubangijin mu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Ba a ta\u0253a yin littafin hikaya na Hausa wanda farashin sa ya kai yawan na \u2018Mace Mutum\u2019 ba. To akwai tsoro a zukatun marubutan Hausa cewa wai idan marubuci ya \u201ctsuga\u201d ku\u0257i, ba za a saya ba. Ke ya abin ya shafe ki?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: Kamar yadda na gaya maka a tambayar farko, ni da kai na ina cikin masu irin wannan tsoro, musamman ma da na lura da cewa mafiya yawan makaranta matan cikin gida ne, sannan ga littafin ya yi ku\u0257in wata atamfar biki, don haka na zaci kowa ya zo saye zai ce ya yi tsada, amma sai ga shi mafi yawa na cewa ai ma ya yi arha. Wata\u0199ila wannan ne ya sanya wasu dilolin su ka dinga zabga ku\u0257i bayan da su ka fahimci cewa za a saye shi a ko nawa ne. Don zan iya tunawa cewa an kawo min kukan an sayi littafin a Gombe kan farashi N1,500, sa\u0253anin ku\u0257in bai-\u0257aya da ake sayar da shi, N820.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Jigon littafin ya ta\u2019alla\u0199a ne kan wahalhalun da mata ke sha a \u0199auyuka da birane, ta yadda har a kan ga cewa kamar mace ba bil\u2019adama ba ce. Ki na ganin matan Hausawa sun shirya kar\u0253ar wannan sa\u0199on?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: E, daga yadda na ke hange ko fata, matan mu na Hausawa za su so kar\u0253ar sa\u0199on littafin, sai dai ba zan yi wa kai na al\u0199awarin cin karo da zafafan \u0199alubale ba, ba ma daga maza ba har matan da ake yi wa ya\u0199in. Domin bayan na kammala rubutun \u2018Mace Mutum,\u2019 na lura da cewa akwai dubban mata da su ka fi gwammace wa rayuwar da mu ke ya\u0199a fiye da wadda mu ke son ganin su a ciki. Wannan ba zai rasa nasaba da imanin su kan maganar nan mai cewa bayan wuya sai da\u0257i ba. Don haka \u2018Mace Mutum\u2019 na iya samun kar\u0253uwa ko tirjiya daga wa\u0257anda ake abin domin su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Shin ki na ganin cewa kin fice daga \u0199angin \u201cadabin kasuwar Kano\u201d, ko har yanzu ki na ciki?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: Da cewa ka yi na fita ko ina cikin adabin kasuwar Kano? da na ce ina ciki, domin ba na \u0199yamar adabin wanda shi ya haife ni ni da al\u0199alami na. Amma tun da \u0199angi ka ce, ina jin zan iya cewa na kama hanyar fita daga \u0199angin ci-baya da adabin namu ke fama da shi. Kamar yadda hasashe ya nuna, marubuta da dama sun yun\u0199uro don ficewa daga wannan \u0199angi. Kada ka manta, daga cikin littattafan da su ka ci gasar Abuja akwai adabin kasuwar Kano, wanda hakan ba \u0199aramin ci-gaba ba ne ga wannan adabi ba. Don haka ina jin wannan adabi da kan sa ya na jajibirin ficewa daga \u0199angin da ya samu kan sa ba ma mu \u2019ya\u2019yan sa kawai ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Shin wannan littafi \u0199ir\u0199ira ne gaba \u0257aya ko kuwa akwai wasu sassa da ki ka \u0257auko kai-tsaye daga rayuwar zahiri taki ko ta wasu mutane da ki ka yi bincike a kan su?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: Labarin \u2018Mace Mutum\u2019 \u0199agagge ne, sai dai halin da mata ke ciki a wannan littafi gaskiya ne, don haka labarin na iya yin saurin kama da rayuwar wata ko wasu gungun mata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Littafin ya fito da kurakurai na \u0257ab\u2019i inda za ki ga wasu shafukan babu rubutu ko kuma wasu kwafen littafin ba a yanke gefe-gefen ba. Me ya faru?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: Lallai an samu matsaloli wajen aikin wannan littafi. Ina ga wannan bai zai rasa nasaba da gaggawar da mu ka yi a kusan \u0199arshen aikin ba, domin a yayin da mu ka za\u0199u da mu biya ha\u0199\u0199in masu jiran wannan littafi da su ke ta sauraro su na \u0199orafi kan da\u0257ewar sa bai je kasuwa ba. Amma cikin ikon Allah mun shawo kan kashi 90 cikin \u0257ari na wannan matsala domin mun bi kasuwa mun kar\u0253i mafi akasarin wa\u0257annan littattafai da su ka samu matsala don a mai da su kamfani a sake masu aiki. A halin yanzu akwai a\u0199alla kwafe 288 da aka dawo mana da su don mu sake mai da su cikin mahaifiya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Bayan \u2018Mace Mutum,\u2019 sai me kuma zai biyo baya? A wata hira da ki ka ta\u0253a yi da mujallar Fim a cikin 2005 kin nuna cewa za ki ri\u0199a fitar da littafi makamancin wannan a\u0199alla guda \u0257aya a shekara. To, za mu sa ran ganin wani littafin nan da 2009 kenan?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: Lallai zan iya tuna wannan al\u0199awari nawa a can baya, kuma ina da niyyar tabbatar da shi, sai dai kowa na nasa Allah na nasa. Dubi \u2018Mace Mutum,\u2019 tun 2005 ake fama da matsalar da ba ta fi \u0199arfin mu ba, amma har sai da ya kai 2008. Don haka in har na kasa cika wannan al\u0199awari sai na yi fatan samun uzuri daga makaranta don sanin ba da niyya ba ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>SHEME: Wane kira za ki yi ga marubuta kan batun yin littafi mai inganci, mai yawan shafuka, mai jigon da ba na soyayya ba, da sauran su?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">RAHMA: A kullum kira na ga takwarori na kuma \u2019yan\u2019uwa na marubuta shi ne mu daina tunanin abin da za mu kashe da wanda za mu samu a wannan aiki, domin muddin za mu ri\u0199e wannan tunani ba za mu iya yin aiki mai inganci ba. A \u0199asa irin tamu babu abu mai riba kamar abu mara inganci, don haka in fa mu ka za\u0253i inganci dole mu ajiye tunanin riba, ita ce kan sanya mu jin babu wani jigo ga labari sai wanda kwastamomin mu su ka za\u0253a. Sannan mu tuna iya zubi da salo wajen bayar da labari na iya jan hankalin makaranci, ba sai jigo ba. Don haka kada mu ji tsoron za\u0253en jigo kowane iri muddin mun iya zubi da salo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sannan batun yawan shafuka, kada wani ya ga \u2018Mace Mutum\u2019 ya je ya takura kan sa da cewa sai ya ha\u0257a labari mai yawa ko da ba ma\u2019ana sai surutu da maimaici. Kada mu manta, ingancin labari da ma\u2019ana ya fi yawan shafuka amfani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Don haka kira na a nan shi ne in za a yi littafi mai yawan shafukan a tabbatar yawan mai amfani ne ba haihuwar yuyuyu ba. Sannan mu sani, akwai bambanci tsakanin yawan labari mai amfani da \u0199arami mara amfani. Akwai wasu littattafai da mu ke yi da ba su fi shafi arba&#8217;in ba, ba wai don labarin ba zai iya kaiwa shafi \u0257ari biyu ko \u0257ari uku in an bu\u0257a shi ba sai don tsoron yawan ku\u0257in aiki da \u0199arancin riba. Mu tuna, bai wa labarin ha\u0199\u0199in sa na cika shi shi ma wata riba ce. Allah ya sa mu dace.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2014\u2014\u2014\u2014\u2014\u2014\u2013<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>An buga wannan hirar a mujallar Fim ta watan Afrilu 2008, shafi na 60-61. Haka kuma an ta\u0253a buga wata cikakkiyar hirar da na yi da Rahma A. Majid kan littafin \u2018Mace Mutum\u2019 a mujallar Fim ta Nuwamba 2005 da Disamba 2005.<\/em><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_4059\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4059\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ta yi mani bayani kan sakamakon da ta gani bayan fitar jibgegen littafin ta a kasuwa. Ina ta sa gaba yanzu? KWANAN nan ne fitacciyar marubuciyar nan Rahma Abdul Majid ta fitar da sabon littafin ta mai suna \u2018Mace Mutum.\u2019 \u0198aton littafi ne, domin rabon ka da ganin littafin hikaya [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4059\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4059\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4068,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4059","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":67,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Daga &#039;Mace Mutum,&#039; Sai Me? - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Daga &#039;Mace Mutum,&#039; Sai Me? - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ta yi mani bayani kan sakamakon da ta gani bayan fitar jibgegen littafin ta a kasuwa. Ina ta sa gaba yanzu? KWANAN nan ne fitacciyar marubuciyar nan Rahma Abdul Majid ta fitar da sabon littafin ta mai suna \u2018Mace Mutum.\u2019 \u0198aton littafi ne, domin rabon ka da ganin littafin hikaya [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2008-04-04T04:49:00+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg?fit=1280%2C1065&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1280\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"1065\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Daga &#8216;Mace Mutum,&#8217; Sai Me?\",\"datePublished\":\"2008-04-04T04:49:00+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059\"},\"wordCount\":1466,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059\",\"name\":\"Daga 'Mace Mutum,' Sai Me? - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg\",\"datePublished\":\"2008-04-04T04:49:00+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/02\\\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg\",\"width\":1280,\"height\":1065,\"caption\":\"Littafin 'Mace Mutum' da marubuciya Rahma A. Majid\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=4059#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Daga &#8216;Mace Mutum,&#8217; Sai Me?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Daga 'Mace Mutum,' Sai Me? - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Daga 'Mace Mutum,' Sai Me? - Ibrahim Sheme","og_description":"Fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ta yi mani bayani kan sakamakon da ta gani bayan fitar jibgegen littafin ta a kasuwa. Ina ta sa gaba yanzu? KWANAN nan ne fitacciyar marubuciyar nan Rahma Abdul Majid ta fitar da sabon littafin ta mai suna \u2018Mace Mutum.\u2019 \u0198aton littafi ne, domin rabon ka da ganin littafin hikaya [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2008-04-04T04:49:00+00:00","og_image":[{"width":1280,"height":1065,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg?fit=1280%2C1065&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Daga &#8216;Mace Mutum,&#8217; Sai Me?","datePublished":"2008-04-04T04:49:00+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059"},"wordCount":1466,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059","name":"Daga 'Mace Mutum,' Sai Me? - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg","datePublished":"2008-04-04T04:49:00+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg","width":1280,"height":1065,"caption":"Littafin 'Mace Mutum' da marubuciya Rahma A. Majid"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=4059#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Daga &#8216;Mace Mutum,&#8217; Sai Me?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/IMG-20230207-WA0002-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4059","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4059"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4059\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4068"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4059"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4059"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4059"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}