{"id":3931,"date":"2009-02-09T17:41:00","date_gmt":"2009-02-09T17:41:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3931"},"modified":"2009-02-09T17:41:00","modified_gmt":"2009-02-09T17:41:00","slug":"tsare-iyan-tama-sabon-zubin-zalunci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931","title":{"rendered":"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">BU\u018aA\u018a\u018aIYAR WASI\u0198A ZUWA GA MALAM IBRAHIM SHEKARAU<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mai Girma Gwamna,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">NA rubuto maka wannan bu\u0257a\u0257\u0257iyar wasi\u0199a ne saboda na yi amanna da cewa za ta fi saurin isa gare ka maimakon in bi hanyar da ku ka tsara, saboda ina da magana mai bu\u0199atar sauri. Idan na mi\u0199a wasi\u0199ar a ofishin ka, za ta iya \u0257aukar kwanaki da yawa ko ma watanni kafin ta isa gare ka, kuma kafin lokacin ba za ka iya samun bayani na ha\u0199i\u0199a ta kafa mai zaman kan ta ba kan tantagaryar zaluncin da wasu jami\u2019an ka su ke aikatawa da sunan ka. Na biyu, tun tuni ma ake ta zancen a majalisun hira a tsawon watanni da su ka gabata. Yanzu akwai alamun an jingine maganar ta hanyar wata shari\u2019a wadda ko ka\u0257an ba ta da kan-gado, inda wasu masu fushi da fushin wani su ka yi amfani da a\u0199idar ka ta aiki bisa doka da oda, da tausayin talakawa, da rashin yaudara da kuma tanadodin Musulunci. Bugu da \u0199ari, buga wannan wasi\u0199ar a bainar jama\u2019a zai ba wa duk wani mai sha\u2019awar sanin abin da ake ciki damar samun \u0199arin haske kan \u0257aya daga cikin muhimman al\u2019amuran da ke gudana a gwamnatin ka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ran ka ya da\u0257e, ina da cikakkar masaniya kan wannan lamari, ba kawai don ina biye da maganar a kotun majistare ta Kano inda aka kai ta ba, a\u2019a har ma saboda ni \u0257an cikin gida ne a al\u2019amuran sana\u2019ar finafinan Hausa. Ba sai na nanata maka ba cewa Kano ce cibiyar finafinan Hausa a sama da shekara goma da aka yi ana yin sana\u2019ar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na tabbatar da cewa ba za ka rasa masaniya ba kan shari\u2019ar da ake tafkawa tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano (KSCB) da wani furodusan fim mai suna Alhaji Hamisu Lami\u0257o Iyan-Tama. Ran ka ya da\u0257e, Iyan-Tama \u0257an asalin Kano ne wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da harkar finafinan Hausa gaba, sannan kuma \u0257an wasa ne \u0257an sahun gaba. Hasali ma dai shi ne shugaban farko da aka za\u0253a na \u0198ungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFPAN). Kowa ya san cewa bai ta\u0253a shirya fim ko kuma ya fito a fim \u0257in da za a yi Allah-wadai da shi ba, wato wanda ya sa\u0253a wa kyawawan al\u2019adun jama\u2019ar Kano ko addinin Musulunci. Duk rol \u0257in da zai yi a fim, za ka taras na manyantaka ne; ya kan nace kan lallai a yi fim da ya dace da al\u2019adun mu, sannan shi mutum ne mai bin doka. Finafinan sa sun ci manyan kyaututtukan girmamawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ran ka ya da\u0257e, idan har ka samu damar karanta wannan wasi\u0199ar a yau, to Iyan-Tama ya kwana biyu a gidan yarin Kano, domin a ran Talata wata kotun majistare ta yanke masa hukunci kan abin da ta kira laifuffuka guda biyu, bayan an shafe watanni ana yawo da hankali a kes \u0257in. A hukuncin da kotun ta zartas, Iyan-Tama zai shafe wata uku a tsare ba tare da za\u0253in biyan tara ba. Haka kuma zai biya ma\u0199udan ku\u0257i na tara ko kuma ya yi zaman kaso na tsawon shekara \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yawancin mu da ke sa ido kan lamarin ba za mu damu ba ko ka\u0257an da hukuncin in da a ce da gaske Hamisu ya aikata laifuffukan. Ni \u0257in nan na yarda da bin doka da oda, domin hakan shi ne ginshi\u0199in \u0257orewar mulkin dimokira\u0257iyya. Ba wanda ya fi \u0199arfin doka. In an yi amfani da wannan tsarin ne dimokira\u0257iyya za ta iya \u0257orewa kuma \u0199asa za ta samu zaman lafiya. To amma gaskiyar magana ita ce, Hukumar Tace Finafinai ce ta \u0199ir\u0199iri laifukan da aka ce Iyan-Tama ya aikata, sannan wani al\u0199ali mai goyon bayan hukumar, wanda kuma ya yi \u0199aurin suna wajen \u0257aure duk wani wanda aka gurfanar a gaban sa, ko da bai da laifi, shi ne ya yanke masa wannan \u0257anyen hukuncin. Wani abin ban-damuwa shi ne ana tafka wannan aika-aikar ne da sunan tanadojin nan masu tsarki na Shari\u2019ar Musulunci. Daga fahimta ta da abubuwan da ke fitowa daga bakin ka da ganin wasu abubuwan da ka aikata, har yanzu ban amince ba da cewa kai \u0257in nan za ka goyi bayan zalunci ta kowace fuska ko kuma ka bar wani ya na saka siyasa cikin shari\u2019ar Musulunci don ya ci mutuncin jama\u2019a cikin son rai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2019Yalla\u0253ai bari in \u0257an fa\u0257a maka abin da ya faru. Jami\u2019an Hukumar Tace Finafinai sun kama Iyan-Tama a ofishin sa a Kano, su ka kai shi kotun tafi-da-gidan-ka wadda aka kafa don yi wa \u2019yan fim da marubuta shari\u2019a (aka fa\u0257a\u0257a zuwa duk wani nau\u2019i na rubutu). Abin mamaki, babu wata kotu irin ta; babu kotun \u2019yan aca\u0253a ko ta karuwai ko ta \u2019yan caca ko ta \u2019yan luwa\u0257i, da sauran su. An tuhumi Iyan-Tama da \u201claifuffuka\u201d guda biyu:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">1. Sakin fim \u0257in sa na \u2018Tsintsiya\u2019 a Kano ba tare da Hukumar Tace Finafinai ta amince da shi ba kamar yadda doka ta tanada;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">2. Gudanar da kamfanin shirya fim mai suna Iyan-Tama Multimedia ba tare da yin rajista da gwamnati ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To amma duk wa\u0257annan tuhumar, \u0199arya ne, kuma lauyan sa ya yi \u0199o\u0199arin nuna wa al\u0199ali Alhaji Mukhtar Ahmed hakan. An \u0257auki watanni kafin a yanke hukuncin, wanda ya yi matu\u0199ar girgiza yawancin mazaunan Kano da wajen ta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bari mu fara da tuhuma ta biyu. An yi wa kamfanin Iyan-Tama Multimedia rajista da gwamnati, wato a Corporate Affairs Commission (CAC), wadda ke da alhakin yi wa dukkan kamfanoni rajista a Nijeriya. Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta ce wai Iyan-Tama bai sabunta rajistar sa ta shekara-shekara da ita ba. Wannan ma \u0199arya ce domin watanni kafin a kama shi, ya sayi fom \u0257in har an ba shi rasi\u0257ai. To wanda ya yi wannan yun\u0199urin ai ya na kan hanyar yin rajistar ne kuma bai yi kama da wanda ke \u0199o\u0199arin karya dokar yin fim a Kano ba. Kuma ya na da amincewar Gwamnatin Tarayya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tuhuma ta farko ma ta fi ban-haushi. Ran ka ya da\u0257e, Iyan-Tama bai saki fim \u0257in \u2018Tsintsiya\u2019 a Kano ba. Hasali ma dai ya yi tallace-tallace da hirarraki a rediyo da jaridu kafin a \u0199addamar da fim \u0257in a Abuja, inda ya fito \u0199arara ya ce ba za a saki fim \u0257in a Jihar Kano ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A lokacin da Hukumar Tace Finafinai ta yanke shawarar \u201ckoya wa Iyan-Tama darasi,\u201d jami\u2019an ta sun karya shagon saida finafinai na HRB da ke unguwar Tarauni a Kano, su ka samo faifan sidi na fim \u0257in, wanda wani \u0257an wasan fim ya \u0253oye cikin durowar teburi wanda ya ce a Kaduna ya sayo shi da nufin zai ba wa wata mai sha\u2019awar finafinan sa. Ba wai an kasa sidi \u0257in don sayarwa ba. \u0181ullar sa a Kano bai da wata ala\u0199a da Iyan-Tama. Idan ka karanta takardun kotu inda lauyoyi ke yi wa jami\u2019an Hukumar Tace Finafinai su biyu tambayoyi a gaban al\u0199ali, za ka yarda \u0257ari bisa \u0257ari cewa ba a tabbatar da cewa Iyan-Tama ne ya kawo faifan sidi \u0257in wannan shagon ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A bayyane yake cewa shari\u2019ar Iyan-Tama ramuwar gayya ce kurum. Wani \u0253angare ne na yun\u0199urin ya\u0199i da wasu \u2019yan fim ko ta halin \u0199a\u0199a wanda Hukumar Tace Finafinai ta \u0257aura. A gajeren tunanin hukumar, ta hanyar yin haka ne za a iya share duk wani abu na sana\u2019ar fim da harshen Hausa. Hukumar ta na amfani da ba\u0199ar farfaganda, ta na ba da bayanan \u0199arya, tare da yin ragguwar fassarar Dokar Tace Finafinai ta 2001, sannan ta na amfani da sunan Musulunci ta hanyar da ba ta Musulunci ba wajen sauya al\u0199iblar hanyoyin nisha\u0257i a Kano.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mai girma Gwamna, duk wannan ya sa\u0253a wa furucin ka na tabbatar da adalci. Kuma hakan ya haifar da abubuwa marasa da\u0257i ga gwamnatin ka da kai kan ka, wa\u0257anda zan fa\u0257a maka su yanzu tare da duk girmamawa a gare ka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya mai girma Gwamna, ya\u0199in da ake yi da sana\u2019ar fim a Kano, ana yin sa ne da sunan Shari\u2019ar Musulunci, to amma ko ka\u0257an ba Musulunci ba ne. Wa\u0257anda ke yin ya\u0199in sun yi gangami ne su na furta kalaman Al\u0199\u2019ur\u2019ani mai tsarki da Sunnar Manzo, to amma abubuwan da su ke aikatawa kai ka ce Hitla ne ya ce su aikata shi. Babu wani abu da su ka aikata kan \u2019yan fim da ya nuna cewa sun bi nasihohin Annabi Muhammadu (SAW). Kamar yadda na fa\u0257a a sama, tsarin da su ke bi na halaka sana\u2019ar fim ta na da illa matu\u0199a, ba wai kawai ga \u2019yan fim ba har ma ga gwamnatin Jihar Kano. Zan \u0257an bayyana wasu daga cikin illolin yanzu:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">1. An jefa dubban matasa cikin rashin aikin yi bayan kuwa a da su ne su ke sama wa kan su hanyoyin abinci, wanda hakan ya shafe su tare da iyalan su. Ba a sama masu wasu hanyoyin na daban ba domin samun abinci. Maya\u0199an ka su kan ce, \u201cIna ruwan mu da su? Ai yawancin su ba \u2019yan Kano ba ne!\u201d To amma hakan ya sa\u0253a wa \u0199o\u0199arin gwamnatin ka na sama wa \u0257imbin matasan Kano aikin yi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">2. Ya\u0199in ya kawo koma-baya ga tattalin arzikin Kano wanda da ma ya na cikin garari. Da yake manyan kamfanonin Kano duk sun dur\u0199ushe, kamata ya yi a gina harkar fim ta yadda za ta kasance mai dogaro da kan ta, kuma wadda ta dace da al\u2019adun Kano da dokokin hukuma. Maimakon a yi hakan, sai aka koma ana kashe ta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">3. An haifar da fargaba da rashin sanin al\u0199iblar rayuwa a zukatan matasan, kuma da yawan su sun koma \u2019yan maula.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">4. An haifar da \u0199in Shekarau a zukatan matasan. Hujja ita ce irin wa\u0199o\u0199in \u0253atanci da ke ta bayyana daga situdiyoyin wa\u0199o\u0199in finafinai a Kano, Zariya da Kaduna. Da fari, irin wa\u0257annan wa\u0199o\u0199in su na sukar Hukumar Tace Finafinai ne, to amma yanzu akalar su ta sauya har su na ha\u0257owa da gwamna da iyalin sa. Kai, wa\u0199ar da ta fi yin fice a wannan fagen ma, an shirya ta ne a situdiyon da wani na hannun daman ka ya mallaka, to amma Hukumar Tace Finafinai ta kasa yin komai a kai saboda shi mai situdiyon ba ya ta\u0253o a gare ta. Wannan tsanar da ake yi wa Shekarau ta na ta \u0199aruwa kuma za ta iya kasancewa ba\u0199ar guguwa ga jam\u2019iyyar ANPP a za\u0253en da za a yi a shekarar 2011 a Jihar Kano.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">5. An fara yin shakku kan manufa da kuma al\u0199iblar yekuwar Shariar Musulunci, wadda miliyoyin jama\u2019a su ka runguma. Duk shugaban da ke yin nasihar adalci da gyaran tarbiyya, bai kamata ya hana dubban matasa hanyoyin samun abincin su ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ran ka ya da\u0257e, ina daga cikin masu goyon bayan shirin ka na gyaran zamantakewar jama\u2019a ta yadda za su yi daidai da al\u2019adu da tanadodin addinin da jama\u2019ar mu ke bi. Shi ya sa na ke goyon bayan shirin gwamnatin ka na A Daidaita Sahu, wanda abokin mu Malam Bala Muhammad ke aiwatarwa cikin ban-sha\u2019awa da kuma samun cikakkar nasara. To amma Hukumar Tace Finafinai ta na warware duk wata tufka da A Daidaita Sahu ta cimma nasarar yi. Gaba \u0257aya tsarin a bau\u0257e ya ke, kuma ana aiwatar da shi a kan tafarkin mugunta da ramuwa da rashin jin \u0199ai. Ya kauce wa duk wani tsari na ya-kamata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun yarda da cewa sana\u2019ar finafinai ta shiga ru\u0257u wanda ya kamata a gyara ta a cikin shekarun baya. Hakan ya \u0199ara bayyana ne bayan \u0253ullar majigin batsa na Hiyana. To amma akwai bu\u0199atar a jawo shugabanni na sosai na industiri \u0257in don a samu nasara. Maimakon haka, sai Hukumar Tace Finafinai ta ture su gefe \u0257aya, ta jawo wasu \u2019yan koren ta, sannan ta na shirya tarurruka na yaudara da rainin wayo, har ma da shirya dina don magoya bayan ta su zo su ci abinci. Ba shakka, wannan tsarin na raba kan jama\u2019a da farfaganda irin ta \u2019yan Nazi da hukumar ke yi ba abin da ya haifar sai bala\u2019o\u2019i, sannan an samu gazawa a wajen gyaran tarbiyyar industirin finafinan Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Har yanzu ana sayar da finafinai da fosta-fosta na batsa a Kano. Haka kuma, \u2019yan \u0199alilan \u0257in finafinan Hausa da magoya bayan Hukumar Tace Finafinan su ka shirya (tare da amincewar hukumar don a \u0253oye \u0199aryar cewa ba kashe sana\u2019ar fim ake yi ba) ba su da wani bambanci da irin finafinan da hukumar ta ke i\u0199irarin cewa marasa inganci ne. Don Allah, finafinai masu inganci kuma \u201cwa\u0257anda sun dace da tarbiyya\u201d, guda nawa ne aka shirya a \u0199ar\u0199ashin jagorancin Hukumar Tace Finafinan tun daga lokacin da majigin Hiyana ya fito?<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ran ka ya da\u0257e, za ka yarda da ni idan na ce maka ainihin dabarar shirin fim ba aba ce mai illa ba, don haka bai kamata a kashe ta ba. Za a iya shirya finafinai kan jigogin rayuwa iri-iri wa\u0257anda su ka dace da al\u2019adun mu. Kamata ya yi a yi wa \u2019yan fim jagora, ba wai a ri\u0199a yi masu \u0253atanci ba ko kuma a yi masu korar kare daga gari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ran ka ya da\u0257e, Hamisu Iyan-Tama dai fursunan siyasa ne: ya yi adawa da kai lokacin za\u0253en 2007 ta hanyar fitowa takarar gwamna shi ma. Ai bai ma yi maka wata barazana ba. Kai aka \u0199ara za\u0253a. To amma saboda tsaurin idon da su ke ganin ya yi na yin takara da kai, jami\u2019an ka su na hukunta shi. Sun ce wai shi mutum ne mai cika baki, mai surutu kuma wai ya na sukar gwamnatin ka. To mun ji, shin su \u0257in ba masu cika baki ba ne, su na yin abu sai ka ce sun fi kowa iko a duniya? Shin ba sa kallon duk wani wanda bai yarda da ra\u2019ayin su ba a matsayin abokin gaba ko su kafirta shi, ko maras bin biyayya gare su, ko su ce ai ba \u0257an Kano ba ne ko kuma bai san ainihin abin da ake ciki ba? Shin wannan ba babbar \u0257agawa ba ce?<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kuma ma ko da a ce Iyan-Tama na da cika baki ko kuma abokin adawar ka ne na siyasa, shin hakan hujja ce ta hukunta shi da zaman gidan yari duk da yake bai karya doka ba? Shin ya yi maka illa a siyasance irin illar da masu surutan nan ke yi maka a gidan Rediyon Freedom? Shin a ina dimokiradiyyar da ake ta magana ta ke? Shin ko Manzon Allah (SAW) ko wani daga cikin halifofin sa ko \u0257imbin tabi\u2019an da su ka biyo bayan su za su bi irin wannan hanyar don hukunta abokin adawa?<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mai girma Gwamna, ya kamata ka binciki wannan al\u2019amari na Iyan-Tama, don Allah, musamman rawar da al\u0199alin da ya \u0257aure shi ya taka a shari\u2019ar da sauran shari\u2019un zalunci da ya yi wa masu sana\u2019ar fim. Kuma don me za a ce kotu ta na yi wa wata hukumar gwamnati aiki? Don me al\u0199ali \u0257aya ne ka\u0257ai zai ri\u0199a yin duk wata shari\u2019a da ta ha\u0257o da Hukumar Tace Finafinai bayan an ga sau da yawa ya nuna inda bakin sa ya karkata? Shin wannan mutum ne mai tsoron Allah ko kuwa \u0257an siyasa mai \u0199ullatar jama\u2019a?<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ka yi amfani da \u0199arfin mulkin ka ka fitar da Iyan-Tama daga \u0199angin da aka saka shi a ciki ta hanyar janye \u0199arar da ku ke yi da shi a kotu. Na san ka na da zuciyar yin hakan domin ai ka ta\u0253a yin irin haka a wasu al\u2019amura da su ka ha\u0257o da kai, ciki kuwa har da wanda ya ha\u0257o da \u0253atanci da aka yi wa mai\u0257akin ka. Kada ka bari wasu mutane \u2019yan \u0257oki wa\u0257anda ka ba mu\u0199amai su ri\u0199a ya\u0199ar abokan adawar ka ta hanyar zalunci domin kuwa Gobe \u0198iyama za ka amsa tambayoyin ka ne yayin da za su amsa nasu daban da naka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2019Yalla\u0253ai, zan tsaya a nan, sai a nan gaba za mu \u0199ara yin wannan magana da sauran maganganu. Ni ne mai biyayya a gare ka, kuma mai ba ka shawara tagari. Wassalam.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>(Wannan fassara ce na sharhin Turanci da na yi kwana baya. An wallafa wannan na Hausan a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma\u2019a da ta wuce)<\/em><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_3931\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3931\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>BU\u018aA\u018a\u018aIYAR WASI\u0198A ZUWA GA MALAM IBRAHIM SHEKARAU Mai Girma Gwamna, NA rubuto maka wannan bu\u0257a\u0257\u0257iyar wasi\u0199a ne saboda na yi amanna da cewa za ta fi saurin isa gare ka maimakon in bi hanyar da ku ka tsara, saboda ina da magana mai bu\u0199atar sauri. Idan na mi\u0199a wasi\u0199ar a ofishin ka, za ta iya [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_3931\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3931\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-3931","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":25,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"BU\u018aA\u018a\u018aIYAR WASI\u0198A ZUWA GA MALAM IBRAHIM SHEKARAU Mai Girma Gwamna, NA rubuto maka wannan bu\u0257a\u0257\u0257iyar wasi\u0199a ne saboda na yi amanna da cewa za ta fi saurin isa gare ka maimakon in bi hanyar da ku ka tsara, saboda ina da magana mai bu\u0199atar sauri. Idan na mi\u0199a wasi\u0199ar a ofishin ka, za ta iya [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2009-02-09T17:41:00+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"14 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci\",\"datePublished\":\"2009-02-09T17:41:00+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931\"},\"wordCount\":2830,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931\",\"name\":\"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2009-02-09T17:41:00+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3931#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci - Ibrahim Sheme","og_description":"BU\u018aA\u018a\u018aIYAR WASI\u0198A ZUWA GA MALAM IBRAHIM SHEKARAU Mai Girma Gwamna, NA rubuto maka wannan bu\u0257a\u0257\u0257iyar wasi\u0199a ne saboda na yi amanna da cewa za ta fi saurin isa gare ka maimakon in bi hanyar da ku ka tsara, saboda ina da magana mai bu\u0199atar sauri. Idan na mi\u0199a wasi\u0199ar a ofishin ka, za ta iya [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2009-02-09T17:41:00+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"14 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci","datePublished":"2009-02-09T17:41:00+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931"},"wordCount":2830,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931","name":"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2009-02-09T17:41:00+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3931#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3931","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3931"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3931\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3931"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3931"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3931"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}