{"id":3775,"date":"2010-09-23T02:12:00","date_gmt":"2010-09-23T02:12:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3775"},"modified":"2010-09-23T02:12:00","modified_gmt":"2010-09-23T02:12:00","slug":"wai-da-sunan-yancin-addini","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775","title":{"rendered":"Wai da sunan \u2019yancin addini!"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A makon ba a ji irin ta ba. Wai so ya yi a yi gangamin }ona Al}ur&#8217;ani mai tsarki a ranar Asabar da ta gabata. Tun lokacin da faston ya bayyana wannan }udiri nasa a dandalin duniya na intanet (a shafin Facebook), da sunan \u201cRanar Babbaka Al}ur\u2019ani ta Duniya\u201d, aka shiga musayar miyau kan al\u2019amarin a ko&#8217;ina a fa]in duniya. Shi dai wannan bidiri, wata }aramar majami&#8217;a ce mai suna Dove World Outreach Centre da ke garin Gainesville da ke jihar Florida ta }asar Amerika ce ta shirya shi, a }ar}ashin fasto mai suna Rabaran Terry Jones, a matsayin tunawa da kewayowar ranar harin }unar Ba}in Wake ]in nan da aka kai wa Amurka da jiragen sama a watan Satumba 2001. Kowa ya zuba ido ya ga abin da zai wakana, amma kwatsam, a ranar Alhamis ta makon jiya sai fasto Jones ya bayyana ]age taron.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan ]agewa da ya yi ta sa Musulmi a fa]in duniya sun yi ajiyar zuci, sun yi murna, to amma kuma sun ji haushin kasawar da faston ya yi. Sun yi murna domin hakan ya sa an kauce wa faruwar wata fitina da ba a san inda za ta tsaya ba in ta tashi, sun kuma ji haushi saboda gangamin na Jones ashe soki-burutsu ne, kuma wata hanya ce ta neman suna. Duk da haka, Musulmi sun fahimci cewa soke gangamin ya }ara nusasshe mu da al}awarin da Allah (SWT) Ya yi a cikin littafin Sa mai tsarki cewa Shi mai karewa ne ga wannan Littafi a koyaushe.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ba Musulmi ka]ai ba ne su ka yi murna da ]age gangamin }ona Al}ur&#8217;anin. Hatta Kiristoci da Yahudawa sun yi murna, domin kusan kowannen su ya yi tir da yun}urin da faston ]an shekara 58 ya yi. A gaskiya, babu wani Kiristan kirki da zai goyi bayan irin wannan aika-aikar. Dalili shi ne, duk da yake Musulmi da Kirista sun bambanta matu}a kan manyan ginshi}an addinan su, amma su na girmama junan su, musamman ma a wannan zamani da duniyar ta }an}ance, ta zama tamkar wani ]an }aramin }auye inda kowa ya san kowa, sannan jama\u2019a mabambantan addinai su na rayuwa tare a cikin gari ]aya ko }asa ]aya. Jones dai ya yi }aurin sunan da ya so ya yi, to amma kama tun daga fadar Fafaroma zuwa fadar shugaban Amurka har zuwa kan jarumar finafinai Angelina Jolie babu wanda bai yi Allah-wadai da shi ba. Daga birnin Montreal na }asar Kanada har zuwa Nijeriya babu wanda bai yi kira a gare shi da kada ya kuskura ya tafka wannan shirmen nasa ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An yi zanga-zangar nuna rashin amincewa a }asashe da su ka ha]a da Afghanistan da Pakistan da Indonesiya. Fadar Fafaroma ta ce Kiristoci \u201cba su amince da wannan gagarumar ~arnar da ake shirin yi kan littafin da mabiya wani addini su ka amince da cewa mai tsarki ba ne.\u201d Wani shugaban Kirista a Lahore, babban birnin Pakistan, wato Achibishop Lawrence John, ya bayyana }udirin Jones da cewa ya \u201csa~a wa girmamawar da mu ke yi wa dukkan addinai kuma bai yi daidai da a}ida da kuma karantarwar addinin mu ba.\u201d Shugaban Kiristocin }asar Lebanon, Michel Suleiman, ya ce barazanar gangamin }ona littafi mai tsarkin \u201cbayyanannen sa~ani ne ga karantarwar addinan nan uku da su ka samo tsatso daga jinin Annabi Ibrahim da kuma bu}atar daraja juna a tsakanin su.\u201d Addinan dai su ne addinin Yahudanci (Judaism), da Kiristanci da kuma Musulunci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A birnin Washington na Amurka, shugabannin addinai daban-daban sun yi babban taro a cibiyar \u2019yan jarida ta }asa inda su ka yi kira ga mabiyan addinai da su ha]u su yi bataliyar yin artabu da \u201cfargaba da rashin ha}uri\u201d da ake nuna wa Musulunci. Shi kuma tsohon babban limamin cocin Katolika na Washington, wato Kadinal Theodore McCarrick, kiran }iyayyar da ake yi wa Musulunci ya yi da sunan \u201cbabban lokaci da ke bu}atar babban martani.\u201d Sannan a}alla shugabanni guda 24 na addinai daban-daban da ke kusa da cocin Jones a garin Gainesville sun shirya gudanar da ayyuka don nuna }in gangamin }ona Al}ur\u2019anin. Wani fasto da ke majami\u2019ar United Church ta garin Gainesville ]in, wato Larry Reimer, ya ce Jones \u201cba ya wakiltar kowa&#8230; Abin da ya ke yi babu girmamawa a ciki, sannan babu ruwan Allah a ciki, wanda Shi ne ya ce mu }aunaci junan mu.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A nata ~angaren, gwamnatin Amurka ta ji tsoron cewa \u2019ya\u2019yan }asar za su iya shiga wani mugun yanayi a }asashen waje. Shugaba Barack Obama ya bayyana }udirin Jones da cewa zai ba }ungiyar Al}a&#8217;ida damar samun }arin membobi. Jami&#8217;an gwamnatin sa ma sun yi nuni da hakan. Misali, Janar David Patreaus, wanda shi ne kwamandan sojojin Amurka da ke Afghanistan, ya bayyana wannan ba}ar aniya ta Jones da cewa ita ce \u201cainihin irin abin da }ungiyar Taliban ta ke amfani da ita kuma za ta jawo mana manyan matsaloli &#8211; ba ma a nan }asar ka]ai ba, har ma a sauran sassan duniya inda mu ke mu\u2019amala da al\u2019ummar Musulmi.\u201d Takwaran sa da ke Ira}i ma, Janar Ray Odierno, ya yi garga]in cewa idan har aka ci gaba aka yi wannan gangamin na }ona Al}ur\u2019ani, to babu shakka akwai raddin da zai biyo baya daga Musulmi. Ya ce: \u201cIna da damuwar cewa hakan zai jawo a kai wa sojojin mu hare-hare.\u201d Ita kuma ministar harkokin waje ta Amurka, Hillary Clinton, ta yi tir da yun}urin ne, ta ce \u201cbabban abin kunya\u201d ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idan mun lura, daga kalaman da ke sama, za mu iya fahimtar cewa }udirin fasto Jones bai samu tagomashin sauran Kiristoci ba, don haka ba wai dukkan su ba ne su ka ha]e wa Musulunci kai su ka ce a yi hakan. Kawai wasu tsirarun masu tsattsauran ra\u2019ayi ne su ka shirya abin; hasali ma dai, kwata-kwata mabiyan Jones mutum 50 ne a duk }asar. Na biyu, Jones ya yi amfani da irin damar da kafafen ya]a labarai na Amurka su ke ba \u2019yan taratsi irin sa ne wajen ya]a manufar sa. Su wa]annan kafafe, da ma haka su ke kambama }an}anin abu, su maida shi }ato; kowane irin shirme aka wurga masu da sunan abin labari ne, sai kawai su ]auka su bi duniya su na yayatawa. In da ba su yayata wannan shirmen na Jones ba, to da shikenan hankalin kowa ba zai tashi ba.<br>Na uku, shugabannin siyasa na }asashen Turawa sun }i goyon bayan Jones, ba wai kurum don ya sa~a wa karantarwar addinin su ba, har ma saboda yun}urin wannan ja\u2019irin zai iya jefa \u2019yan }asar su da ke waje cikin ha]ari. Na hu]u, wannan lamarin ya }ara tabbatar mana da cewa tunanin nan da wasu masana ke yi na cewa wata rana za a kwafsa tsakanin }asashen Turawa da Musulunci, har yanzu bai kau ba. Ba shakka, }udirin Jones babbar alama ce da ke nuna cewa mabiya addini masu }iyayya da duk wani addini su na }ara zurfafa }iyayyar su a cikin yun}urin su na ganin bayan ]aya addinin. Idan kuwa haka ne, ashe akwai babban aiki a gaban masu }o}arin ganin an samu fahimtar juna da zaman lumana a tsakanin addinai mabambanta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A gaskiya, a }asashen Turawa ne ka]ai, musamman ma a Amurka &#8211; inda duk abin da aka ce maka zai yiwu, to zai yiwu &#8211; ake samun wani wanda ake ganin babban mutum ne a }asar ya shirya irin wannan aika-aikar har a saurare shi. Amma abin tambaya shi ne, me ya sa hukumomin Amurka ba su yi }o}arin hana shirmen Jones ba maimakon su tsaya su na ba shi magana? Na san amsar da za a ba ni ita ce ai wannan coci na garin Gainesville ya na da dama, a }ar}ashin tsarin mulkin }asar, ya yi abin da ya ga dama bisa \u2019yancin yin addini. Lokacin da Jones ya ce ya soke gangamin }ona Al}ur\u2019anin, ya yi }o}arin danganta yun}urin sa da wani yun}urin da wasu Musulmi su ke yi na gina masallaci a harabar wurin da aka kai hare-haren jiragen saman nan a cikin 2001. Wannan ba wani abu ba ne illa }o}arin yi wa Musulmi tarna}i na ba gaira ba dalili, domin kuwa ai gina masallaci a wurin ba wula}anta addinin Kirista ba ne. Ni a ra\u2019ayi na, bai zama ma dole a gina masallaci a wurin ba; dalili: yin hakan zai }ara gur~ata dangantaka da \u2019yan }asar wa]anda ke kallon wurin a matsayin wata fuska ta tsantsar Amerikanci, kuma zai zafafa dangantaka a tsakanin addinai. Kamar yadda Obama ya fa]a, gina masallacin bai sa~a wa doka ba to amma ba lallai ba ne a ce ya dace &#8211; wato kamar yadda wani jami\u2019in fadar White House mai suna David Axelrod ya ce lokacin da ya ke tarfa yawun bakin sa kan aniyar Jones, inda ya ce ta yiwu Jones \u201cya na da \u2019yancin yin hakan. Amma abin tambaya shi ne ko hakan ya dace.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A yanzu dai akwai alamun cewa wannan hayaniya ta Jones ta wuce, to amma fa kada mu yi sake. Har yanzu akwai sauran rina a kaba domin kuwa akwai mutane masu ra&#8217;ayi irin nasa da yawa a Amurka, kai har ma a Nijeriya. Ya kamata }asashen Turawa su sake yin nazarin dokar su ta ba da cikakken \u2019yancin addini. Tsaron lafiyar jama\u2019a ha}}i ne da ya rataya a wuyan gwamnati. Idan har abin da Jones ya yi }o}arin aikatawa barazana ce ga tsaron Amurka kamar yadda masu magana su ka fa]a, shin wannan bai zama kamar ya na karya dokar Amurka ba kenan? Shin ba akwai Musulmi masu yawa ba da ke tsare a }iri}irin tsibirin Gwantanamo kawai bisa zargin sun yi abin barazana ga bu}atun Amurka?<br>Kyakkyawar aniyar nan ta Obama ta rage rashin jituwar da ke tsakanin }asashen yammaci da addinin Musulunci ta na samun barazana daga mutane masu tsattsauran ra\u2019ayi irin su Jones. Barin irin wa]annan mutanen su na ya]a }iyayyar su ya sa~a wa }udirorin da Obama ya ta~a zayyanawa a gagarumin jawabin da ya yi a jami\u2019ar Al-Azhar ta Misira lokacin da ya hau mulki. Shi \u2019yancin yin addini, kamar kowane \u2019yanci, ya na fa da iyakoki; \u2019yanci ne da ya ba ka damar ka yi addinin ka, amma bai ba ka damar ka hana wani yin nasa addinin ba. {ona Al}ur\u2019ani &#8211; wanda hakan ya nuna tsananin }iyayya ne &#8211; ya na nufi a hana Musulmi su gudanar da addinin su, ta hanyar wula}anta addinin su, da tsoratar da su da kuma muzanta su. Wasu \u2019yan tsirarun masu tsattsauran ra\u2019ayi ba su da \u2019yancin yin duk wani abu da zai iya jawo ramuwar gayyar da za ta yi sanadiyyar salwantar rayukan wasu wa]anda ba su ji ba ba su gani ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kamata kuma mu fahimci cewa in da wannan ta\u2019asar ta yi nasara, to za ta iya bazuwa a wasu }asashen wa]anda ba ruwan su da haukan da aka kitsa a Gainsville. Ko yanzu ]in ma, maganganun sa~o da Jones ya ri}a furzaswa kan Musulunci ya ba}anta ran Musulmi da yawa, musamman ma da yake cikin Ramadan ya ri}a yin su, wato wata mafi tsarki a Musulunci. Shi fa Jones, wanda ba ya wakiltar Amurka ko addinin Kirista, bai damu ba idan wani ya mutu a sanadiyyar shirmen da ya tafka. Shi da kan sa ya nuna hakan lokacin da ya fa]a wa gidan talabijin na ABC cewa wai \u201cabin ba}in ciki ne\u201d idan ko da ran mutum ]aya ya salwanta a dalilin wannan abu, \u201cto amma duk da haka, mu ba mu damu da cewa laifin mu ba ne.\u201d Don Allah, Amurka kada ki bari mutane irin wa]annan su na aikata abin da su ka ga dama wai da sunan \u2019yancin yin addini.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_3775\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3775\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A makon ba a ji irin ta ba. Wai so ya yi a yi gangamin }ona Al}ur&#8217;ani mai tsarki a ranar Asabar da ta gabata. Tun lokacin da faston ya bayyana wannan }udiri nasa a dandalin duniya na intanet (a shafin Facebook), da sunan \u201cRanar Babbaka Al}ur\u2019ani ta Duniya\u201d, aka shiga musayar miyau kan al\u2019amarin [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_3775\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3775\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-3775","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":29,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Wai da sunan \u2019yancin addini! - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Wai da sunan \u2019yancin addini! - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A makon ba a ji irin ta ba. Wai so ya yi a yi gangamin }ona Al}ur&#8217;ani mai tsarki a ranar Asabar da ta gabata. Tun lokacin da faston ya bayyana wannan }udiri nasa a dandalin duniya na intanet (a shafin Facebook), da sunan \u201cRanar Babbaka Al}ur\u2019ani ta Duniya\u201d, aka shiga musayar miyau kan al\u2019amarin [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2010-09-23T02:12:00+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"10 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Wai da sunan \u2019yancin addini!\",\"datePublished\":\"2010-09-23T02:12:00+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775\"},\"wordCount\":2029,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775\",\"name\":\"Wai da sunan \u2019yancin addini! - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2010-09-23T02:12:00+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3775#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Wai da sunan \u2019yancin addini!\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Wai da sunan \u2019yancin addini! - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Wai da sunan \u2019yancin addini! - Ibrahim Sheme","og_description":"A makon ba a ji irin ta ba. Wai so ya yi a yi gangamin }ona Al}ur&#8217;ani mai tsarki a ranar Asabar da ta gabata. Tun lokacin da faston ya bayyana wannan }udiri nasa a dandalin duniya na intanet (a shafin Facebook), da sunan \u201cRanar Babbaka Al}ur\u2019ani ta Duniya\u201d, aka shiga musayar miyau kan al\u2019amarin [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2010-09-23T02:12:00+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"10 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Wai da sunan \u2019yancin addini!","datePublished":"2010-09-23T02:12:00+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775"},"wordCount":2029,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775","name":"Wai da sunan \u2019yancin addini! - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2010-09-23T02:12:00+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3775#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Wai da sunan \u2019yancin addini!"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3775","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3775"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3775\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3775"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3775"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3775"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}