{"id":3773,"date":"2010-09-23T02:09:00","date_gmt":"2010-09-23T02:09:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3773"},"modified":"2010-09-23T02:09:00","modified_gmt":"2010-09-23T02:09:00","slug":"irin-yayan-wannan-zamanin","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773","title":{"rendered":"Irin &#8216;ya\u2019yan wannan zamanin"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wai wa\u0257anne irin \u2018ya\u2019ya ne mu iyaye mu ke haifa a wannan zamanin? Shin mun yarda ha\u0199\u0199in mu ne ko me su ka zama da kuma ko me su ke aikatawa a cikin al\u2019umma? Idan su ka zama na kirki ko kuma su ka lalace, shin za mu ce a dalilin tarbiyyar da mu ka yi masu ne? Wa\u0257annan tambayoyin sun yi ta walankeluwa a rai na a tsawon lokaci. Sun fara yawo a zuciya ta, tare da yin \u0199alubale ga tunani na, tun lokacin da aka ce an kama wani matashi \u0257an babban gida, wato Umar Faruk Abdulmutallab, da laifin wai ya yi \u0199o\u0199arin tada bam a cikin jirgin sama lokacin da su ka \u0199araci birnin Detroit na \u0199asar Amurka, a ranar 25 ga Disamban da ya wuce. Tambayar da jama\u2019a su ka yi ta yi a lokacin ita ce: don me zai yi hakan? Me ya ke bu\u0199ata a rayuwa? Masu zargin sa da aikata laifi dai sun ce wai \u0199ungiyar Al\u0199a\u2019ida ce ta sa shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Babbar tambayar da ta dugunzuma ni, ta faru ne a makon jiya lokacin da labari ya \u0253ulla cewa wani matashin ya yi wa uwar sa da uban sa da \u0199annen sa uku kisan gilla a Kano. Kisan gillar, wadda aka yi a daren Lahadi, ta sa na \u0257au al\u0199alami da nufin yin sharhi kan yadda aikata muggan laifuka a \u0199asar nan ya ke \u0199ara yawaita. Shi magidancin da aka kashe a Kano \u0257in, kamar yadda ku ka ji a labarai, jami\u2019in hukumar tsaron \u0199asa ta SSS ne, wato Alhaji Garba Bello. An kashe shi ta hanyar yanka da wu\u0199ar \u0257akin girki shi da kusan dukkan iyalin sa in ban da mutum biyu. Jini ya kwarara a gidan, abin ba kyan gani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da farko, tun kafin a ce \u0257an mutumin ne ya yi kisan, na yi matu\u0199ar girgiza kan rashin tausayin da aka nuna wajen kisan. Wane irin laifi ne wannan bawan Allah ya yi da har za a ce an shafe shi daga doron \u0199asa tare da duk iyalin sa a irin wannan mugun yanayi? Wane mara imani ne zai ma yi tunanin aikata hakan a matsayin ramuwa? A rai na, na ce tilas ne duk wani mai \u0257aukar albashi da sunan aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a \u0199asar nan ya tabbatar da cewa an gano makisan wa\u0257annan mutanen. Kada \u2018yan sanda su yi \u0199asa a gwiwa wajen gano wa\u0257annan makisan marasa imani!<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To amma ka\u0257uwar da na yi ta farko kan kisan ba ta kai ko cikin cokalin wadda na yi ba washegari da sabon labari ya \u0253ulla: wai Bello ne, wato babban \u0257an marigayin da marigayiyar, ya kashe su! Inna lillahi wa inna ilaihir raji\u2019un! A cewar kwamishinan \u2018yan sanda na Jihar Kano, Alhaji Mohammed J. Gana, wai Bello (wanda aka fi sani da suna Baba) shi ne ya tafka wannan ta\u2019asa saboda ya yi imani da cewa mutan gidan su za su shiga halin ha\u2019ula\u2019i idan mahaifin sa, wanda ba shi da lafiya, ya rasu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan abu ya fi ba ni mamaki fiye da ainihin kisan domin kuwa ya jefa ni a kogin tunani kan makomar mu ta kiran kan mu da sunan bil\u2019adama da mu ke yi, wato masu hankali da sanin ya-kamata da kuma kar\u0253ar \u0199addara ko wace iri ce. Tambayoyin da ake ta yi a \u0199asar nan su ne: wane irin abu ne zai sa \u0257a ya halaka uwar sa da uban sa da \u0199anne uku \u2013 biyu mata, namiji \u0257aya? Shin ya haukace ne baki \u0257aya a lokacin? A gaskiya, ba a ta\u0253a aikata mugun abu irin wannan a Kano ba tun cikin 2006 lokacin da wani matashin ya kashe Hajiya Sa\u2019adatu Rimi, wadda matar uban sa ce, wato tsohon gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Rimi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan kisan gilla da aka yi ya fita daga cikin da\u2019irar hankali, kai ka ce ba a nan \u0199asar ya faru ba. Mu dai mu kan karanta a jarida ko mu gani a talbijin cewa an yi irin wannan kisan kiyashin a wata \u0199asar Turawa, inda da ma son abin duniya, da zaman \u2018yan marina da kuma yin watsi da \u0199a\u2019idojin addini sun sa an yi fatali da kyakkyawar tarbiyya. Mu a nan Nijeriya, sai a da\u0257e ba ka ji wani ya kashe mahaifin sa ko uwar sa ko kuma shi kan sa ba, kuma idan har irin hakan ya faru mutane su kan yi matu\u0199ar al\u2019ajabi tare da tsananin fargaba. A kan dubi wanda ya aikata irin wannan ta\u2019asar a matsayin dabba mai sunan mutum.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dalilin da aka ce Bello ya bayar na yin kisan duk shirme ne, kuma kame-kame ne na mutumin da \u0199wa\u0199walwar sa ta ta\u0253u. Don an kore shi daga jami\u2019a inda ya ke karatu ba hujja ba ce da ke nuna cewa rayuwar sa ta zo \u0199arshe daga nan; akwai matasa da yawa irin sa, ko ma wa\u0257anda ba su kai shi galihu ba, kuma su kan ci gaba da yin rayuwar su har su more ta a wasu sassan na rayuwar \u0257an\u2019adam. Haka kuma, ci gaba da rayuwar iyayen sa da \u2018yan\u2019uwan sa ba ha\u0199\u0199in sa ba ne. Abincin su da sauran bu\u0199atun su na rayuwa duk su na hannun Maiduka. Tunanin da aka ce ya yi na aikawa da su barzahu don kautar da su daga fa\u0257awa cikin fatara da yunwa, sam, ba ya cikin tunani nagari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da farko, Bello ya amince da aikata laifin, domin an gabatar da shi a gaban manema labarai inda ya amince \u0257in. To amma daga bisani dai labarin ya fara sauyawa. Ran Alhamis ta makon jiya, wani kawun Bello ya yi i\u0199irarin cewa ba Bellon ba ne ya aikata ta\u2019asar, wai jami\u2019an tsaro ne su ka tilasta masa har ya yi wancan furucin. Sannan shi ma Bello, da aka kai shi kotu ran Litinin da ta wuce, ya musanta zargin cewa shi ne ya yi kisan. To yanzu dai ya rage ruwan kotu ta yanke hukunci kan wannan sabon zancen. To amma mu a namu \u0253angaren, maganar farko da aka yi ta sa tilas mu tsaya tsayin daka, mu sake duban irin ri\u0199on da mu ke yi wa matasan mu. Irin wannan ta\u2019asar fa ta na faruwa a \u0199asar nan, ko da ba ta kai zurfin wannan ta Kanon da ake magana ba: sai ka ji an ce wani yaro ya kashe uban sa ko uwar sa a kan wani \u0257an sa\u0253ani da bai taka kara ya karya ba. Ko kwanan nan, irin haka ta faru a Jihar Katsina, inda wani ya da\u0253a wa uban sa wu\u0199a, ya aika da shi lahira. A makon jiya ma, a Legas, an kwata irin wannan, inda wani ya kashe uban sa. A yau Juma\u2019ar nan ma da mu ke magana, jaridar Aminiya ta ruwaito yadda wani ma\u2019aikacin kurkuku ya kashe \u2018ya\u2019yan sa tagwaye.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sau da yawa, ba mu damu ba idan mun ji an yi irin wannan ta\u2019asar, a tunanin mu ai ba mu abin ya shafa kai-tsaye ba. Mun manta da cewa a gidan wasu ko gidan ma\u0199wabtan su, abu ne mai ciwo ya faru. A ko yaushe fa ana yin kisan gilla a \u0199asar nan, wanda ya kan haifar da ciwo a zukata da dama. Rayuwa su na ta salwanta a yayin da rigingimu ke \u0199aruwa. Ga dai fashi da makami da kuma rikicin addini, wanda duk su na cin rayuka masu yawa. Ana kisan kai ma a harkar siyasa, inda wasu \u2018yan siyasar da ke gaba da junan su su kan yi hayar \u2018yan iskan gari, wa\u0257anda yawanci matasa ne, don su halaka abokan gabar su. Wata sa\u2019a, jami\u2019in gwamnati za ka ji an kashe, wato kamar jami\u2019in EFCC \u0257in nan da aka bindige a gidan sa a Kaduna a ran Litinin ta makon jiya. Wata sa\u2019a kuma, \u2018yan jarida ake kashewa, kamar dai Bayo Ohu na jaridar The Guardian.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dole ne mu tashi tsaye cikin hanzari mu samo maganin matsalar. Iyaye ne ya kamata su fara \u0257aukar mataki na farko wajen cusa tarbiyya a rayuwar \u2018ya\u2019yan su tun su na \u0199anana. Tarbiyya daga gida ta kan fara. Hausawa dai na cewa icce tun ya na \u0199arami ake tan\u0199wara shi. A wannan zamanin, sai ka ga iyaye da dama \u2013 musamman ma mazan \u2013 ba su da lokacin kula da abin da ke faruwa a gidajen su, su na can su na neman abinci ko \u0199arin dukiya. Na biyu, tilas ne gwamnati ta ri\u0199a sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta na samar da ilimi mai nagarta da kuma aikin yi ga matasa. Tun tuni harkar ilimi ta zaganye, makarantu sun zama abin da su ka zama, ba su iya amfanar da al\u2019umma kamar yadda ya kamata, domin ko da yaro ya gama karatun sai ka ga zu\u0199u ne kawai ya yi ko mu ce karatun aku. Don haka sai ya kasa samun aiki. Idan kuwa har babu nagartaccen ilimi, sai matasan mu su kasance ba su \u0257aukuwa a wuraren aiki, wanda hakan kan sa su zama abin nema ga muggan mutane masu ba\u0199ar niyya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A yau, matasan mu sun raja\u2019a ga bin munanan halaye, ciki kuwa har da shaye-shaye ko kallon hotuna da finafinan batsa. Kuma a \u0199o\u0199arin su na samun abin sakawa a bakin salati, sai su koma su na aikata laifuffuka da kuma nau\u2019o\u2019in karuwanci. Ba mu damu da abin da su ke karantawa a wasu littattafai da mujallu ko intanet ba, ko abin da su ke gani a cikin wasu finafinan, ko kuma abin da su ke saurare a wasu wa\u0199o\u0199in.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A yayin da hakan ke faruwa, shugabannin mu su na can su kuma su na wawure dukiyar \u0199asar. Sai ka ga fatara da yunwa na \u0199aruwa a yayin da ake tafka cin hanci da rashawa. Hakan na \u0199ara haifar da yawaitar muggan laifuffuka. Sakamakon duk wannan su ne irin munanan abubuwan da ba mu so mu gani da idon mu ko mu ji da kunnen mu. Abin takaicin ma shi ne, ba mu so a \u0257ora mana laifin kasawar da mu ka yi. To amma ita gaskiya, gaskiya ce, kuma dole mu fuskance ta. Sannan idan mun dubi fuskar ta, sai mu kau da kai domin babu kyakkyawar sura gare ta saboda yadda mu ka bari ta munana. Da ma Hausawa sun ce wanda bai \u0199i ji ba, ba zai \u0199i gani ba.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_3773\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3773\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wai wa\u0257anne irin \u2018ya\u2019ya ne mu iyaye mu ke haifa a wannan zamanin? Shin mun yarda ha\u0199\u0199in mu ne ko me su ka zama da kuma ko me su ke aikatawa a cikin al\u2019umma? Idan su ka zama na kirki ko kuma su ka lalace, shin za mu ce a dalilin tarbiyyar da mu ka [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_3773\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3773\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-3773","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":17,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Irin &#039;ya\u2019yan wannan zamanin - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Irin &#039;ya\u2019yan wannan zamanin - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Wai wa\u0257anne irin \u2018ya\u2019ya ne mu iyaye mu ke haifa a wannan zamanin? Shin mun yarda ha\u0199\u0199in mu ne ko me su ka zama da kuma ko me su ke aikatawa a cikin al\u2019umma? Idan su ka zama na kirki ko kuma su ka lalace, shin za mu ce a dalilin tarbiyyar da mu ka [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2010-09-23T02:09:00+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Irin &#8216;ya\u2019yan wannan zamanin\",\"datePublished\":\"2010-09-23T02:09:00+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773\"},\"wordCount\":1774,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773\",\"name\":\"Irin 'ya\u2019yan wannan zamanin - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"datePublished\":\"2010-09-23T02:09:00+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3773#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Irin &#8216;ya\u2019yan wannan zamanin\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Irin 'ya\u2019yan wannan zamanin - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Irin 'ya\u2019yan wannan zamanin - Ibrahim Sheme","og_description":"Wai wa\u0257anne irin \u2018ya\u2019ya ne mu iyaye mu ke haifa a wannan zamanin? Shin mun yarda ha\u0199\u0199in mu ne ko me su ka zama da kuma ko me su ke aikatawa a cikin al\u2019umma? Idan su ka zama na kirki ko kuma su ka lalace, shin za mu ce a dalilin tarbiyyar da mu ka [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2010-09-23T02:09:00+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Irin &#8216;ya\u2019yan wannan zamanin","datePublished":"2010-09-23T02:09:00+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773"},"wordCount":1774,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773","name":"Irin 'ya\u2019yan wannan zamanin - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"datePublished":"2010-09-23T02:09:00+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3773#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Irin &#8216;ya\u2019yan wannan zamanin"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3773","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3773"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3773\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3773"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3773"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3773"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}