{"id":3425,"date":"2011-02-10T16:21:00","date_gmt":"2011-02-10T16:21:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3425"},"modified":"2011-02-10T16:21:00","modified_gmt":"2011-02-10T16:21:00","slug":"sai-bango-ya-tsage","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425","title":{"rendered":"Sai Bango Ya Tsage\u2026"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idan har wannan makon ya \u0199are jam\u2019iyyun adawa na siyasa a Nijeriya ba su ha\u0257u su ka fito da \u0257an takara guda \u0257aya da za su shigar a za\u0253en watan Afrilu ba, to kawai mu \u0257auka cewa duk a cikin su babu wanda zai iya doke Dakta Goodluck Jonathan \u2013 ko an yi za\u0253e ba magu\u0257i ko kuma an yi za\u0253e da almundahana. Abin da ya sa na yi wannan kintacen shi ne amannar da na yi cewa a yanzu kam, kawunan wa\u0257annan jam\u2019iyyu da ke kiran kan su jam\u2019iyyun siyasa duk a rarrabe su ke a kan batun yin wani gagarumin shiri don za\u0253en, kuma babu wata \u0199wa\u0199\u0199warar alama da ke nuna cewa za su iya zama su baje komai a faifai a cikin mako \u0257aya.<\/p>\n<p>Yanzu hankalin jam\u2019iyyun a tashe ya ke a daidai lokacin da wa\u2019adin da Hukumar Za\u0253e ta \u0198asa (INEC) na su kawo sunayen \u2019yan takarar su ya kusa cika. Dalili shi ne fargabar da ta cika zukatan jam\u2019iyyun ganin cewa yanzu Jonathan ya samu tikitin tsayawa takarar a \u0199ar\u0199ashin inuwar jam\u2019iyyar PDP, wanda ya \u0199ara masa \u0199arfi fiye da yadda ya ke kafin a yi za\u0253en fidda gwani na jam\u2019iyyar mako uku da su ka gabata, kuma akwai alamun lallai zai iya lashe za\u0253en da za a yi a Afrilu. Yanzu akwai bayyanannun alamu masu nuna cewa idan har jam\u2019iyyun adawa ba su ha\u0257u su ka mara wa \u0257an takara \u0257aya baya ba, to ham\u0253arar da Jonathan da kaifin \u0199uri\u2019a zai kasance tamkar \u0257aukar Dala ba gwammo.<\/p>\n<p>Akwai tarurrukan da ake ta yi don tabbatar da an cimma hakan, to amma har yanzu babu wanda ya haifar da \u0257a mai ido. A ranar Juma\u2019a ta makon jiya, jaridu sun ruwaito labarin wani taro da aka yi \u201ca asirce\u201d tsakanin Malam Nuhu Ribadu na jam\u2019iyyar ACN da Janar Muhammadu Buhari na CPC a gidan shi Buharin da ke Kaduna. An ce an yi taron ne da nufin fito da hanyoyin da za a bi a \u0199wace mulki daga hannun Shugaba Jonathan. Wannan tunanin ya yi daidai da \u0199o\u0199arin da ake ta yi na ganin cewa mulki ya dawo arewa a za\u0253e mai zuwa.<\/p>\n<p>To amma ko wannan yun\u0199urin zai yi nasara kuwa? Kai mai karatu, ka ma fi ni sanin amsar. A ha\u0199i\u0199anin gaskiya, jam\u2019iyyun adawa na \u0199asar nan dai duk jam\u2019iyyun son rai ne. Kowane \u0257an adawa so ya ke a ce shi ne a saman sauran, shi ya sa bai yarda da duk wata yarjejeniyar a ha\u0257u a fidda jaki daga duma ba in ban da wadda za ta ba shi karsashi. Duk wani taro nasu ya na \u0199arewa ne a fayau domin duk wanda ya je taron ya na zuwa ne da \u0199o\u0199on barar don-Allah-wane-ka-bar-mani.<\/p>\n<p>Ba sai mun wahala ba wajen gano abin da ke janyo hakan. Ita siyasar adawa da ake yi a Nijeriya a yau, ba irin ta da ba ce. Yanzu babu \u0253ur\u0253ushin a\u0199ida a jam\u2019iyyun, wanda hakan ya sa su ka kasance tamkar \u2019yan biyu masu kama \u0257aya in ban da ta wajen sunayen su. Amma su kuwa jam\u2019iyyun zamanin da, lokacin da duniya na kwance lafiya, wato jam\u2019iyyun Jamhuriya ta Farko irin su NCNC, NEPU, UMBC, da AG, da na Jamhuriya ta Biyu irin su UPN, NPP, GNPP, da PRP, an kafa su ne bisa wata a\u0199ida. Duk mutanen da je jagorantar su ko su ke cikin su mutane ne da su ka kafe kan abin da su ka yi amanna da shi, ba wai don su na tunanin cewa amannar su \u0257in za ta kawo masu dukiya ko suna ba, a\u2019a sai domin sun yarda babu kokwanto da cewa hakan ita ce hanya mafi sahihanci da za a bi a gyara al\u2019umma kuma a gina \u0199asa.<\/p>\n<p>Gidan yanar Wikipedia da ke intanet ya bayyana cewa a\u0199idun siyasa sun kasu ne gida biyu: 1. Buri: Wato yadda ya kamata al\u2019umma ta rayu ko a tsara ta, sai na 2. Gwadabe: Wato hanya mafi dacewa da za a bi a cimma shi wannan burin. Shi ya sa a \u0199asar Amurka za ka taras da cewa mutum ko dai ya na jam\u2019iyyar Democrat ne ko kuma ya na jam\u2019iyyar Republican; a Birtaniya kuma ko dai ka na jam\u2019iyyar Labour ne ko ka na ta Conservative. Ban da wa\u0257annan, babu wasu manyan jam\u2019iyyu, illa wasu \u0199ananan jam\u2019iyyu da ke gefe guda don kula da mutanen da su ke ganin ra\u2019ayin su ya bambanta da na wa\u0257annan \u0257in.<\/p>\n<p>Ka lura, ita a\u0199idar siyasa kamar addini ce: mutum ba ya ficewa don kurum kwa\u0257ayin wata ganima da ya hango. Mutane su kan ha\u0257e ne saboda sun yi amanna da wasu muradai da aka tsara, wanda shi ne ke sa su su yi wani abu a siyasance tare da yin aiki da kundin a\u0199idar su. Ba su ha\u0257uwa don kawai a taru a ci abin \u0199walamar da ke kan tebur ko don a yi ginsamin abin jefawa cikin aljihu.<\/p>\n<p>A yau, labari ya bambanta. Sai ka ga gungun mutane su na ta nin\u0199aya a tekun siyasa, su na sanye da bajen wai su \u2019yan siyasa ne. Duk \u0199ibar su, mayunwata ne kawai, kuma yunwar da su ke ji (ta giyar mulki ko ta naira) ita ce ke tunzura su, ba wai a\u0199ida ba. Shi ya sa ba mamaki ka ga yadda \u2019yan siyasar da su ka yi suna a matsayin \u2019ya\u2019yan wata jam\u2019iyya, an wayi gari sun yi tsalle sun auka wata jam\u2019iyyar, ko da kuwa sun yi shekaru su na \u0253ata ta. Ana kiran wannan halayyar wai sauyin she\u0199a, kuma \u2019yan siyasa da dama a wannan \u0199asa tamu su kan yi hakan cike da alfahari, kuma iya \u0199arfin su, a yayin da kuma su ke borin kunyar cewa wai an \u0199i jinin su ne a \u0257aya jam\u2019iyyar. Misalin irin wa\u0257annan \u2019yan siyasa bai da adadi. An za\u0253i Alhaji Atiku Abubakar a matsayin gwamna a \u0199ar\u0199ashin PDP a shekarar 1999, to amma lokacin da wasa ya yi tsami tsakanin sa da Obasanjo sai ya kafa jam\u2019iyyar AC, wadda ta lashe za\u0253e a Jihar Ikko. A yau, ya dawo PDP, jam\u2019iyyar da ya so ganin bayan ta, har ga shi ya nemi zama \u0257an takarar ta na shugabancin \u0199asa. Alhaji Aminu Bello Masari babban \u0257an PDP ne, wanda shi ne kakakin Majalisar Wakilai na tsawon shekaru. A yau, ya na takarar gwamna a jam\u2019iyyar CPC a Jihar Katsina. Dora Akunyili ma \u2019yar PDP ce wadda ta ri\u0199e mu\u0199amin ministar ya\u0257a labarai da sadarwa a \u0199ar\u0199ashin shugabannin \u0199asa har biyu; a yau, \u2019yar takarar zama sanata ce a \u0199ar\u0199ashin jam\u2019iyyar APGA a Jihar Anambara. Dakta Abba Sayyadi Ruma, wanda a da babban \u0257an PDP ne, inda har ya ta\u0253a zama sakataren gwamnati a Jihar Katsina kuma daga bisani ya zama ministan aikin gona, yanzu ya na takarar gwamna a \u0199ar\u0199ashin CPC. Shi ma Sanata Adamu Aliero jagora ne a PDP a da, amma yanzu ya na takarar zama sanata a \u0199ar\u0199ashin CPC a Jihar Kebbi. Malam Nuhu Ribadu wani jigo ne a gwamnatin PDP a zamanin Cif Olusegun Obasanjo, amma yanzu \u0257an takarar zama shugaban \u0199asa ne a \u0199ar\u0199ashin ACN. Alhaji Attahiru \u018aalhatu Bafarawa ya zama gwamnan Sakkwato ne a \u0199ar\u0199ashin ANPP, amma ya tafi ya kafa jam\u2019iyyar DPP har ya yi mata takarar zama shugaban \u0199asa a za\u0253en 2007, amma a yau \u0199usa ne a ACN, inda kwanan nan ya nemi tsayawa takarar shugaban \u0199asa. Kai, lissafin bai kammaluwa!<\/p>\n<p>A yanzu wa\u0257annan mutanen da ire-iren su su na nuna mana cewa su wasu mahajirai ne da aka cuta a baya. To amma kowa ya san cewa sun canza she\u0199a ne don kawai an tokare su a jam\u2019iyyun su na baya, kuma za su iya komawa inda su ka fito da zarar sun samu mulki ko kuma sun ga babu sa\u2019ida a inda su ka zo. Dalili kuwa, su a wurin su ai siyasa ba addini ba ce. Sai ka ce ba su ma san ma\u2019anar kalmar \u2018a\u0199ida\u2019 ba. Shi ya sa su ke watangaririya daga wannan jam\u2019iyya zuwa waccan ba tare da jin kunya ko tsoro ba, sai ka ce \u0199udan zuma mai neman furen kallo don ya yi \u0199oto. Ha\u0199i\u0199a, wannan shi ne babban dalilin da ya sa ha\u0257uwar jam\u2019iyyun adawa don su kada shugaban \u0199asa da ke kan gado ya ke da matu\u0199ar wuya a \u0199asar nan, wai gurguwa da auren nesa. Bari mu gani a cikin \u2019yan kwanakin nan idan a siyasar wannan zamanin za su sauya hali duk da yake Hausawa sun ce hali zanen dutse, ba ya kankaruwa.<\/p>\n<p>&#8212;-<\/p>\n<p>An buga a LEADERSHIP HAUSA<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_3425\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3425\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Idan har wannan makon ya \u0199are jam\u2019iyyun adawa na siyasa a Nijeriya ba su ha\u0257u su ka fito da \u0257an takara guda \u0257aya da za su shigar a za\u0253en watan Afrilu ba, to kawai mu \u0257auka cewa duk a cikin su babu wanda zai iya doke Dakta Goodluck Jonathan \u2013 ko an yi za\u0253e ba [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_3425\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3425\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4387,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-3425","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"a3_pvc":{"activated":true,"total_views":23,"today_views":0},"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Sai Bango Ya Tsage\u2026 - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Sai Bango Ya Tsage\u2026 - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Idan har wannan makon ya \u0199are jam\u2019iyyun adawa na siyasa a Nijeriya ba su ha\u0257u su ka fito da \u0257an takara guda \u0257aya da za su shigar a za\u0253en watan Afrilu ba, to kawai mu \u0257auka cewa duk a cikin su babu wanda zai iya doke Dakta Goodluck Jonathan \u2013 ko an yi za\u0253e ba [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2011-02-10T16:21:00+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg?fit=1080%2C458&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1080\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"458\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Sai Bango Ya Tsage\u2026\",\"datePublished\":\"2011-02-10T16:21:00+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425\"},\"wordCount\":1511,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/04\\\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425\",\"name\":\"Sai Bango Ya Tsage\u2026 - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/04\\\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg\",\"datePublished\":\"2011-02-10T16:21:00+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/04\\\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2023\\\/04\\\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg\",\"width\":1080,\"height\":458,\"caption\":\"Hatiman jam'iyyun PDP, ACN, da CPC\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?p=3425#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Sai Bango Ya Tsage\u2026\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/i0.wp.com\\\/ibrahimsheme.com\\\/wp-content\\\/uploads\\\/2026\\\/02\\\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/logo\\\/image\\\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.net\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Sai Bango Ya Tsage\u2026 - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Sai Bango Ya Tsage\u2026 - Ibrahim Sheme","og_description":"Idan har wannan makon ya \u0199are jam\u2019iyyun adawa na siyasa a Nijeriya ba su ha\u0257u su ka fito da \u0257an takara guda \u0257aya da za su shigar a za\u0253en watan Afrilu ba, to kawai mu \u0257auka cewa duk a cikin su babu wanda zai iya doke Dakta Goodluck Jonathan \u2013 ko an yi za\u0253e ba [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2011-02-10T16:21:00+00:00","og_image":[{"width":1080,"height":458,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg?fit=1080%2C458&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Sai Bango Ya Tsage\u2026","datePublished":"2011-02-10T16:21:00+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425"},"wordCount":1511,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425","name":"Sai Bango Ya Tsage\u2026 - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg","datePublished":"2011-02-10T16:21:00+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#primaryimage","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg","contentUrl":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg","width":1080,"height":458,"caption":"Hatiman jam'iyyun PDP, ACN, da CPC"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?p=3425#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Sai Bango Ya Tsage\u2026"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/wp-content\/uploads\/2023\/04\/IMG-20230401-WA0003-1.jpg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3425","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3425"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3425\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4387"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3425"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3425"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.net\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3425"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}